Sashe 213
Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
biyu tsaye har sannan wayar na hannunta, Maimoon dake diban ma Imaan dake xaune saman darduma ta idar da sllh abinci a plate ta kalleta ganin ko motsin kirki bata yi tace "Lafiya Mariya" Mariya bata yarda ta kalli Maimoon ba sbda hawayen da ya kawo idonta, Maryam ta ajiye dankunnen da take kokarin sakawa ita ma tana kallon Mariya tace "Hope all is well dear?" Fita Mariya tayi daga dakin da sauri sai a sannan ta fashe da wani kuka, gaba daya suka bi ta da kallon mamaki, Imaan ta ji gabanta yyi mugun faduwa ta mike daga saman darduman, Maimoon ta mike ta bi bayan Mariya hankali tashe, Maryam ma ta bi bayansu, Imaan ta kalli agogo dake nuna biyu da 'yan mintuna sannan ta sauke idonta a hankali tana karanto addu'a a ranta ko xata samu natsuwa daga bugawan da xuciyarta ke yi, wayarta ta dauko tana dubawa ko xata ga even if it's text from Sadeeq na sanar mata cewar an daura masu aure amma bata go komai ba, ta xauna gefen gado tana goge hawayen dake xubo mata. A hanya Daddy na kallon Abba dake driving xa su koma gida yace "Barrister I don't think what u did was a way a out, ya kake son yyi da mata biyu? A lkci daya kawai" Abba dai bai ce komai ba sai driving yake a nutse, kawu Bala dake cikin motar yace "Gaskiya ne, kada a 6ata daya goma bata gyaru ba, sannan kai baka yi shawara da kowa ba Ahmad" Abba yace "I did what I think is best brothers, da d'an uwana ya ji kunya gwara nayi koma mene, we will sort everything out right daga baya in sha Allah," A haka har suka iso gida babu wanda ya sake cewa komai. Rabon abinci Umma suke yi amma gaba daya ta kasa kunnuwa ta xuba idanu tana jiran dawowarsu Abba da xancen bbu daurin auren Imaan, Safeenah dake hada uban salad sai taunar cingam take ita ma dai tana jiran news, irin cakarewar da tayi kai kace ita ce amaryar, tun sassafe dama ta iso gidan ana ta aiki da ita duk da ta bar Mujaheed yana headache tun cikin dare bata ma san ko xai je daurin auren ba, Umma na ganin shigowarsu Abba duk da ba ita ce mai girki ranan ba haka ta bi bayansa tana masa sannu da xuwa da fara'a tana cewa Allah yasa an daura a sa'a Allah kuma ya bada xaman lafiya, a takaice ya amsa da Ameen, tace "bari in kai maku abinci parlor" ganin mood dinsu gaba daya daga shi har Daddy har ma da kawu Bala taji kamar tayi tsalle don murna, da dukkan alamu dae tayi nasara, Abba na kallon Daddy da ya nufi part dinsa walking like the gentleman he is yace "Sadeeq" juyowa Daddy yyi, Abba yace "Mu tafi can parlona for lunch..." Daddy bai masa musu ba ya dawo suka wuce parlon Abba, Ammi na compound ita ma amma tun shigowarsu ta sha jinin jikinta ganin yanayin Abban Imaan da kawu Bala kai kana ganinsu kasan da matsala don haka bai boyu a fuskarsu ba, Abba ma ne kadai ke d'an yake, abinci iri iri da aka yi Umma ta dinga dire masu a parlor tana cewa "Allah ubangiji ya nuna mana na yan baya, Allah ya basu xaman lafiya gaba daya yasa anyi a sa'a" Babu wanda ya tanka ta a parlon har ta fita tana murmushi sai dai bata ji dadin kin cewa komai da suka yi ba, gashi gaba daya ta hana yan uwanta maxa xuwa daurin aure balle ta kirasu taji yanda aka yi gun daurin auren, fitowa tsakar gida tayi tana hangen inda xata ga Yusuf ko xata d'an samu labari ganin frnds dinsa na ta shigowa compound din... Abba yayi breaking din silence din parlonsa yana kallon daddy da ya jinginar da kansa da kujera yyi nisa tunanin da yake, yace "Naga kamar hankalin ka bai kwanta gaba daya da auren nan da aka daura ba ko Sadeeq?" Kallonsa daddy yyi yace "Not at all, ina dai mamakin al'amarin ne, sannan am hoping this shouldn't be a big blow to my daughter, you know her condition.... Bana son wani abu ya sameta coz baxan iya dauka ba" Abba ya dafe kansa shi ma yana tunanin ta inda xa su fara fasa news din nan wa mutanen gida.... Mama Hadiza ce xaune parlon Abba tare da yayyinta bayan kiran da kawu Bala yyi mata a waya, kai kana ganinta xaka hango tashin hankalin da ke fuskarta karara, lkci daya ta shiga furta Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Daddy dai kansa na jingine da kujera, Abba ya girgixa kai yace "Abinda ya faru kenan Hadiza, mu ma haka lamarin ya xo mana" Hawaye ya kawo idon Mama Hadiza tausayin Daddy ya cikata, hakan bai kamaci only child dinsa ba, to ko ya ita kuma Ammi xata dau xancen balle ita Imaan din gaba daya, Hawaye ta dinga yi sosai tace "Allah ya isa tsakaninmu da shi, ya cuce kansa ba mu, Allah ya saka ma Imaan..." Abba ya d'an yi murmushi ya ciro wayarsa a aljihu yyi dialing number Mujaheed don sure bai gansa gun daurin aure ba, sai da ya kirasa sau biyu sannan ya daga, Abba ya amsa sallaman da yyi yace "Ban gan ka gun daurin aure ba why?" Mujaheed dake kwance ya mike xaune da sauri yana kallon agogo ganin time cikin sanyin murya yace "I slept off Abba, kiranka ne ya tashe ni ban san lkci ya wuce haka ba, har an daura kenan?" A takaice Abba yace "A'a ana jiran ka, I want to see you home now my frnd..." Mujaheed ya gyada masa kai ya kasa cewa komai har Abba ya katse wayar, hade kai yyi da gado trying hard to control himself... Aunty ce ta fara shigowa parlon Abba sannan Ammi ta dalilin kiran da Abba yyi mata ta wayarta wai su taho tare da Ammi, Kallonsu ta dinga yi bayan ta shigo parlon, Mama Hadiza dai kanta na kasa ta ci kuka har ta gode Allah, Ammi ma ta dinga kallonsu lkci daya taji gabanta ya fadi ta xauna kasa a hankali jin kafafuwanta sun kasa daukarta, Aunty ta xauna ita ma cike da karfin hali tace "In ji dai lafiya Abba?" A takaice Abba yace "Lafiya lau" Kawu Bala yace "Lafiyar kenan Amina..." Bude kofa aka yi Umma ta shigo ita ma ta dalilin kiranta da Abba yyi, ganinsu Ammi da Aunty, da Mama Hadiza a parlor kawai taji kamar ta saki guda mai xakiii, rumors da ake tayi tsakar gida ya tabbata kenan, Ta xauna da mamaki fuskarta tace "Lafiya kuwa Alhaji, me ya faru?" Ko rufe baki bata yi ba Yusuf ya shigo parlon tare da Inna da ta cakare cikin super abunta an daura dankwali sai xuba kamshi take ta daura mayafi a kan dankwalin, tana murmushi baki har kunne tace "Toh Allah ubangiji dai yasa an daura a sa'a Allah ya kauda idon makiya, ya kuma sa gidan xamanta ne, ku kuma Allah maku albarka ya baku lada" Kawu Bala ne ya amsa da Ameen kansa a kasa, shi dai daddy kansa na jingine da kujera, inna ta nemi kujera ta xauna tace "Toh wani shawarar kuma xa ayi yanxu aka tara mu a nan, ga dai bak'i can na baro" Abba yayi murmushin karfin hali yace "Mujaheed muke jira Inna" Inna tace "Ae dole, shi ne ubanta na hudu a nan ai...." Bude kofa aka yi sai ga Mujaheed ya shigo parlon sanye da shadda fari kal sai walkiya yake, duk suka dinga kallonsa ya nemi gefen Yusuf da kansa ke kasa ya xauna ya gaishe da iyayen nasa gaba daya da ladabi duk suka amsa, Abba ya kalli Aunty a hankali yace "Go and get Imaan immediately" Mikewa Aunty tayi ta fita ita gaba daya ta gama shan jinin jikinta don gani take ba alkhairi yasa aka tara su parlor ba, ba alkhairi xa su ji ba. Aunty na rike da hannun Imaan da ke lullube cikin mayafi suka shigo parlon Abba, ta xaunar da ita gefenta, imaan bata iya ta dago ba balle ta ga mutanen dake cikin parlon gabanta dai sae faduwa yake, Umma dai har ta fara lissafin nawa xata kai ma mutumin nan kyauta don nuna masa farin cikinta, gaba daya ta kasa boye how happy she is ah wajen duk da ynda ta dinga dakewa, tunda Imaan suka shigo da Aunty Mujaheed ke kallonta ko kiftawa babu, Abba ya bude wajen da addu'a sannan a hankali yace "Bbu amfanin tsaya jan xance ko wani boye boye, kuma ina son kowa a nan ya dau abinda ya faru yau a matsayin kaddara wanda aka ce ta riga fata, mu ma ba haka muka so ba, kowa ma ba haka xai so ba, sai dai kawai mu kara gode ma Allah don shi ya san dai dai, a takaice dai bbu xancen auren Fatima da yaron nan Sadeeq yanxu..." Ba sai na fadi irin girgixan da mutanen dake xaune parlon suka yi ba a lkcn, ciki kuwa har da Umma da ta dinga salati tana xaro ido tace "Babu aure Kuma, bbu aure fa kace Alhaji, a kan wani dalili xa a fasa aure gashi mun tara jama'ah ta ko ina, me ke faruwa don know" Inna dai gwalo idanuwa tayi ta mike tana kallonsu Abba jikinta na rawa kamar maxari tace "Mutuwa Sadeeq din yyi Ahmadu?" Imaan ta fada jikin Aunty ta fashe da wani kuka mai ban tausayi, Ammi kam bata iya ta daga kanta ba, nan ko ita ma hawayen take, Aunty dake hawayen ita ma tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, me ke faruwa Alhaji" Yusuf bai iya ya kalli mutanen parlon ba duk jikinsa yyi sanyi ba kadan ba, Mujaheed ya dinga kallon Abba ko kiftawa bbu xuciyarsa na bugawa jin abinda yace, kawu Bala yyi kasa da murya yace "Duk ku yi hakuri, we never saw this coming, and we are in it all together, komai ya samu bawa a duniya dama rubutattce ne, kuma bbu wanda ya isa ya kauce ma kaddararsa, wannan yaro Sadeeq dai da kansa ya xo