← Book details Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 126 OF 300

Sashe 126

Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari da safe Imaan na kumbure kumbure ta gama shirin islamiyya bayan Ammi tace baxata xauna mata a gida ba, Maryam ta sami Ammi a kitchen a hankali tace "Ammi don Allah ki barta kar ta je yau, I don't have anybody to gist with idan ta tafi fa" Ammi tace "Ga kakarki can ki je ku yi hiran mana" da sauri Maryam tace "A'a ni bana son hirarta kawai tayi ta xagin mutane, nima ta fara xagina" Ammi tayi murmushi tace "She is ur grandma dai" Maryam tace "Sure, pls Ammi kin yarda kar taje?" Ammi tace "Karfe sha biyu xa su tashi ai, kuma sauka xa su yi soon Maryam, imaan ko shakkar fashi bata yi shi sa nayi forcing dinta ta wuce" Maryam tace "Ohk then, Allah ya kai mu 12 din" daga haka ta fita kitchen din, Imaan ta fito daki bayan ta dauko jakarta ta nufi kitchen ta tsaya bakin kofa kamar xata yi kuka tace "Ammi na tafi" Ammi tace "Breakfast din fa?" Ta girgixa kai tace "Ni sai na dawo" Ammi tace "Oho cikin ki" Juyawa imaan tayi ta fita, Maryam ta rakata xuwa parking space, dai dai fitowar Mujaheed da makullin mota a hannunsa, Maryam tayi masa murmushi tace "Good morning ya M.A" ba tare da ya kalleta ba yace "Morning Maryam kin tashi lafiya?" Tace "Sure.. Alhmdllh" Imaan dai tuni ta dauke kai, Maryam tace "Aiki xaka fita ya M.A" yace "Noo, sai da yamma nake fita aiki during weekends" Tace "That's nyc... Do you need my company?" Ya kalleta kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Sure... if that will suit you" ta kalli Imaan tace "Alryt sweetheart xan raka Ya M.A, ayi karatu da kyau a islamiyya" imaan ta kalleta tace "Ohk bye" tana fadin haka ta saci kallon Mujaheed taga kallonta yake, da sauri ta dauke kai, Ya bude motarsa ya shiga ya tada, Maryam ta xaga ta shiga gaba. Ko da Imaan ta dawo daga Islamiyya karfe sha biyu Maryam bata dawo ba, Imaan na kallon Ammi tace "Ammi wai tun da safe har yanxu Maryam bata dawo ba?" Ammi tace "Ehh wai sun fita tare da Mujaheed koh?" Imaan ta tabe baki ta mike ta wuce dakinta. Bayan azahar tana gama cin lunch ta tafi bangaren Inna, Inna na xaune parlor tare da Mama Hadiza, Imaan ta gaida small mum din nata sannan ta gaida Inna da ta tsuke fuska, Inna ta amsa tace "Ke kiji Hadiza da wani mummunan xance Imaan, wai duk abinda xa ayi na bikin Mujaheed mai kyau ko mara kyau in saka ido kar in yi magana, Saboda ita bata da tsoron Allah, bata son gaskiya xuciyarta ta kekashe, to me mutum xai min wanda Allah bai min ba" Mama Hadiza tace "Ni dai ki fahimce ni Inna, idan ba mu fada maki gaskiya ba kina da mai gaya maki ne, ba girman ki bane komai kika gani ki tanka a tafi da ke a baki, Haba inna" Inna tayi mitsi mitsi da ido tace "An dade ba a tafi da ni bakin ba, ni da bikin jikana ki dinga gaya min maganan banxa, ke kinsan wahalan da nayi da Mujaheed kuwa, wllh wllh ko Rukayya bata da iko da shi a yanxu, mutumin da yasa na dinga fada da jama'ah a anguwa yau ya kwale d'an wancan gobe ya danne d'an wancan, da ma Allah ya rufa min asiri bai sa an min duka a anguwar ba har Allah ya raba ni da anguwar? ke kinsan sau nawa na shirya na tafi makarantar su Mujaheed fada da malamai kuwa... Kishiyoyina kuwa duk min dambatu da su a kan Mujaheed, Sannan ace wai in xama kurma a bikinsa kamar uwata tace min je ki kya gani? To wllh karya ake...." Mama Hadiza tace "Ba ace ki xama kurma ba amma ba komai xa ki tanka ba, ba komai xaki shishshige ma ba, Allah na tuba Rukayyar da ma in don ta nata ne bata son a shiga lamarin bikin, ji fa tasan don bikin takanas na xo kasar nan amma tun sannu da xuwan da ta min jiya a bangarensu ban sake ganinta ba, ace kuma tayi farin ciki da xuwana...." Inna ta kunduma ma Umma xagi tace "Ai ba ita ke aurar da d'a ba nice nan mai aurar da Mujaheed kar ki ji komai, mu xuba kuma a gani, Allah dai ya kai mu ranan da rai da lafiya, sai dai mu kwashi yan kallo da ita a bikin nan idan kuma bata yi hankali ba dama baxata kwana gidan nan ba ranan bikin" Mama Hadiza ta tabe baki bata dai ce komai ba, Inna tace "Haka kawai, inyi wahala da shi a dinga gaya min maganan banxa" Imaan dai murmushi kawai take tana danna wayar hannunta, sallama aka yi bakin kofar parlon, Imaan ta juya da sauri jin muryan Sadeeq, Inna ta mike daga xaunen da take da sauri tana washe baki tace "A'ahhh sannu da xuwa Bukar, kai ne da ranan nan... Bisimillah shigo abun ka... Ba kowa daga ni sai Hadiza da Imaan" da gudu imaan ta shige dakin Inna, Sadeeq ya shigo parlon kansa a kasa, Inna na washe hakora ta kalli Mama Hadiza dake xaune kan kujera tace "Ke tashi ki basa waje ya xauna mana, sirkin ku ne" Sadeeq ya bude ido yace "A'a kaka ga waje ai" Bai jira cewarta ba ya xauna saman carpet dake shimfide, Inna ta nufi fridge ta bude ta kwaso ruwa uku da malt uku ta taho, Mama Hadiza dai sai bin ta take da kallo cike da takaici, Sadeeq na kallonta a hankali yace "Ina yini?" Mama Hadiza tace "Lafiya lau, Sannu da xuwa" Inna tace "Saurayin Imaan ne, jira kawai yake ta kare sakandari ayi magana, d'an gidan Ahmad Bulasawa ne mai gidajen man fetur a arewa, sunan yayanki garesa.... Baki ga kirkinsa ba, ni dai tunda nake ban taba cin karo da mutum mai kirki da mutunta babba irinsa ba" Mama Hadiza dai ta kasa cewa komai, Sadeeq dai ya sunkuyar da kansa sai murmushi yake, Inna ta kwalo ma Imaan kira tace "Ji walakanci, to meye na gudu daga jin sallaman bawan Allah, baxa ki fito ku gaisa ba, ba don ke ba a ina xa mu sansa" Imaan da ta xauna saman gadonta ta turo baki ta ki cewa komai, Sadeeq na shafa kansa yace "Dama baki na xo gaidawa kaka" Inna tace "Ahh toh madallah, Ka ganta nan xaune...." Ta fadi haka tana nuna masa Mama Hadiza tace "Uban Imaan ne ya sha nono ya bar mata, ita ce autata, yaranta hudu a duniya Allah yayi ma daya rasuwa, dayar tayi aure tana can gidan mijinta a kasashen turawa, sai kaninta da ke karatu sannan wannan yarinya Maryam da suka xo tare, sa'ar Imaan ce yarinyar kawai dai Imaan ta fita tsayi, ita kuma Maryam din ta fi Imaan xama mace" Tagumi Mama Hadiza tayi tana kallon uwartata, Sadeeq kam murmushi kawai yake kansa a kasa, Inna tace "Toh duk ba wannan ba, kana da labarin bikin Mujaheed wannan Juma'ah me xuwa ne kuwa Bukar?" Sadeeq ya kalleta yace "Ai kam bata gaya min ba kaka..." Inna ta saki salati ta rike ha6a tace "Kaga fitina koh? Duk da dai ko ta gaya maka ko bata gaya maka xa ayi bikin baxa a fasa komai ba amma ai da ta gaya maka, Toh ni dai na gaya maka yanxu, bikin ranan Juma'ahn nan ne" Sadeeq yace "Toh Allah ya kai mu lafiya kaka" Inna tace "Ameen dai, ai har ya kai ni gidan da xa su xauna da amaryar tasa ni da imaan mun gani, baka ga gidan ba d'an madaidaici dai dai kafinsa dai, toh ba dai laifi... ni dai nace Allah ya sanya albarka ai dai ya fi babu wai d'an agwai da bak'in da" Sadeeq ya kasa daina murmushi nan ko dariya ne kawai ke cin sa, Takaici yasa Mama Hadiza ta mike tana kallonsa tace "Toh Sadeeq nagode da gaisuwa Allah yayi albarka bari in shiga can cikin gida" Yace "Toh Ameen mama, nagode" fita tayi daga parlon, Inna tace "Toh ki ce ma Aisha don Allah tayi miyar shuwaka yau, naji raina na so" Mama Hadiza dai bata ce komai ba, Inna tace "Don Allah Imaan ki rufa min asiri ku fito ku gaisa, wannan ai kauyanci ne daga ganin saurayi ki shige daki, ni ko lokacinmu ba a haka" Sadeeq yace "Ki kyaleta kaka" Inna tace "In kyaleta d'an nan?" bata jira cewarsa ba ta mike xata shiga dakin, Imaan na ganin haka ta maxa ta sa hijab dinta ta fito, Inna tace "Ki daina haka don Allah sai ayi tunanin goyon kauye ce ke, nan ko a Habuja aka haife ki" Dariya Sadeeq ya fara yi imaan ta daure fuska ta xauna saman kujera a hankali tace "Ina yini?" Yace "Lafiya lau, ya gida?" Inna ta xauna tana murmushi tace "Gida Alhmdllh" kallonta Imaan tayi da sauri ta wani daure fuska, can ta kallesa tace "Let me see you off, since you've accomplished ur mission here today" Yana murmushi yace "I see why you don't want the 3 of us together..." Inna dai sai washe baki take tana kallonsu tace "Ae ita ma babban makaranta tayi, babu irin turancin da bata iya ba wllh" Mikewa Imaan tayi tana kallon Sadeeq tace "Let go" Mikewa yayi trying hard not to laugh yace "Toh kaka na gaishe da Mama da ke, ni xan koma" Inna tace "Ai mun gode da gaisuwa Bukar Allah maka albarka...." Dubu goma ya ajiye mata tayi tagumi tace "Ni dai na shiga uku Bukar baka gajiya??" kofa ya nufa yace "Ai ba yawa kaka, ayi hakuri" daga haka ya fita don tuni Imaan ta fice daga parlon, sai da suka bar part din Inna Sadeeq ya tsaya ya dinga dariyar da bai samu damar yi a parlor ba non stop, Imaan ta dinga kallonsa kamar xata yi kuka, ganin yanda yake dariya seriously ta jingina da flower tana ci gaba da kallonsa don bata taba ganin dariyarsa haka ba sai this very moment, he looks more cute laughing, bata san lkcn da tayi murmushi ba her eyes still on him,
Chapter 126 · 0% Book details