Sashe 227
Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
kenan, komai nasa na halas ne babu Haram, gaskiya a duba lamarin nan a tausaya ma yaron nan, yanxu dai jiran dawowar ta Rasulu nake inji bayani a nan kuma xa a san ni tababbiya ce a gidan nan, kaff sai na tada gidan nan wllh idan abinda muke xargi gaskiya ne, kuma don Allah da Mujaheed na son auren nan xai gudu? Ni nasan yana can abun duniya ya ishesa baya son auren, ya kwantar da hankalinsa kawai da rai na babu me cutar sa yyi masa auren dole wllh, me xai ci da Imaan Allah na tuba" Mama Hadiza dai bata ce komai ba amma gaba daya kanta ya gama kullewa, bata ma san surutun da Inna take ba don tausayin Sadeeq ya dameta. Misalin karfe sha daya da rabi na dare Inna na kwance parlor sai sharar bacci take ga darduman ta da Hijab da carbi a gefenta tayi shirin tashi tayi sllhn dare anjima, kukan da Imaan ke yi tun bayan wucewar Sadeeq yasa taki kwanciya a dakin bayan tace mata aniyarta ta bi ta, shine tayi kwanciyar ta a parlor, murda kofar parlon aka yi a hankali ya shigo ya ya kulle kofar ya tsaya nan bakin kofa yana kallonta, bayan few seconds ya nufi bedroom dinta walking gently ya bude kofar yana kallon ciki, Imaan na kwance ta rufe har kanta da duvet sai dai ba bacci take ba, duk a xaton ta Inna ce ta bude kofar dakin hakan yasa ko motsi bata yi ba, murmushi yyi ya rungume hannunsa ya jingina da kofa yana kallonta ko kiftawa babu, a hankali ya rufe kofar dakin ya nufi kan gadon, Imaan ta bude ido sosai daga cikin Duvet din da take jin kamshin turaren da take ji....