← Book details Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 300

Sashe 82

Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mikewa inna tayi ta dauko kudin da Sadeeq ya bata a daki tana murmushi tace "Dubu goma ce ciff, babu yanda banyi da yaron ya bari ba ya ki, toh ni ko xan tsaya muna jayayya da shi ne, haka dai na hakura na amsa" Mujaheed ya kasa daina kallonta ko kiftawa babu, Abba ya sauke ajiyar xuciya yace "Toh Allah ya saka da alkhairi" inna tace "Toh ya xancen turo magabatan nasa fa?" Ya d'an yi shiru sai kuma yace "Inna da dai a jira Sadeeq ya dawo koh?" A fusace inna tace "Oh oh Allah waye kuma Sadeeq?? dole sai Bukar din yana nan? kai ba mahaifi kake wajenta ba, Bukar da idan ya tafi Habuja kamar baxai sake dawowa ba, ni ba ruwana ka kirasa a waya ka gaya masa komai in ma ya kama ya taso ne ya taso kawai, to nasan bayan shekara nawa xai dawo idan muka tsaya jiransa??" Abba ya dinga gyada mata kai nan ko neman abinda xai ce mata yake, can dai yace "Toh ko xa ki kirasa da kanki Inna??" ta tsuke fuska tace "Baxan kira ba idan baxa ka kira ba a bar kiran, iyaka in shirya in tafi kano gun kawun ku ya amshi gaisuwa da kudin auren kawai, ai ba ku kadai ke da iko da ita ba" cikin low voice Mujaheed yace "Meyasa baki maganan wa enda suka girmeta a gidan sai ita??" Inna ta masa wani kallo tace "kana nufin su ku kenan masu tambadewa a titi, wato kai da Isuhu, to ni meye ruwana da rayuwarku fisabilillahi? Da ku yi aure da kar ku yi duk daya wllh tunda baku da mafada, ko ni na ajiye ku da xan maku magana idan ba rainin wayo ba, ko me na hada da ku? Ga dai iyayenku suna kallonku basu ce komai ba sai ni bare? Imaan dai Allah ya fiddo mata zankadeden miji in sha Allah, to ni na ajiye ku da xan maku magana idan ba rainin wayo ba, ko me na hada da ku??" Abba ya mike yyi kasa da kai yace "Toh ina fita ynxu xan kira Sadeeq din" Inna tace "Gwara haka dai, kana kiransa ka zayyane masa duk abinda nace tass, kace masa yaron ma takwaransa ne shi ma Sadeeq ake ce masa, baka gansa ba Ahmadu kyakkyawa ga hanci kamar an xana biro, ga idanuwa maa sha Allah" sai da safe Abba yayi mata ya nufi kofa Mujaheed ya bi bayansa, inna ta bi Mujaheed da harara tace "Oho dai bakin cikin ka xai kare maka Mujaheed, daga jin kanwarka tayi miji sai bakin ciki ya bayyana karara a fuskar ka? To aniyar moda ta bi randa, imaan dai nan gani nan bari" Shi dai bai tanka ta ba har ya fita ya kulle kofar. Abba na fita ya shiga kiran d'an uwan nasa, daddy na dagawa ko gaisawa basu yi ba yace "Toh tsohuwa dai ta 6aro mana wani babban aikin Sadeeq" Daddy yace "Tohhh, Me kuma ya faru" Abba yace "Wai aure take son ayi ma Imaan" Daddy ya wani bude ido da mugun mamaki yace "Aure kuma Barrister?" Abba yace "Wllh, and she is damn serious, kawai kirana tayi daxu tana nemana shine na taho and this is what she said" cike da confusion Daddy yace "Aure fa kace Barrister, toh ita tayi mata mijin?" Abba yace "Na dai ji tana ta xancen d'an gidan Bulasawa, ban san ko ita Imaan din ta ma san sa ba, I tried telling her she is too young ko secondary bata gama ba but inda inna take shiga ba nan take fita ba, she didn't even give me a listening ear, she so mean it, so ko xaka kirata yanxu??" Daddy yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un me yasa inna take haka" Abba yace "Kaga gobe Friday if you can squeeze up things ka taho sai mu san yanda xa mu yi koh? Ni bana son in ja xancen ne ranta ya baci kasan yanda take abubuwanta, shi sa mata sallama kawai na fita" Daddy yace "But ka fa san idan tayi deciding abu it's hard ta canxa barrister" Abba yace "Don't worry, ka dai taho goben sai mu san abun yi in sha Allah" Daddy yace "Toh Allah ya kai mu" sallama suka yi Abba ya kalli Mujaheed da kansa ke kasa yana tafiya absentmindedly, Abba ya dafa shoulder dinsa yace "Are you okay son?" Kallon Abba yyi da sauri, sai kuma ya d'an yi murmushi yace "Sure Abba, kawai dai har yanxu I am surprise at what grandma is planning" Abba ya sauke ajiyar xuciya yace "Imaan din har nawa take ma banda abun inna, ga shi ba wani lafiyan kirki gareta ba, inna dai kam abun ta gaba yake ba baya ba, ita kawai ayi auren saboda d'an mai kudi ne, Allah ma kadai yasan abubuwan da ta fada ma yaron, tun tasowar mu muke fama da ita a haka muna ta lallabawa dai, gashi bbu abinda ya canxa har yanxu, abu kuma ya xo ya hade da tsufa, sai dai mu yi ta mata addu'a, Allah kuma ya rabamu da ita lafiya, amma abinda ya ban mamaki shine ta yanda ta san yaron, kuma anya Imaan ta ma san sa kuwa?" Mujaheed dai bai ce komai ba sai pressing din counter dinsa yake a hankali, Abba yace "Kai kasan yaron Bulasawan da take fadi?" Mujaheed ya girgixa kai, bayan few seconds yace "But ina ga Yusuf baxai rasa sanin sa ba don yana mingling da irin su" Abba yyi murmushi yace "I will call and ask him" suna isa sashinsu, Abba yace "Don't forget ka fita ka siyo mata naman da tace" a hankali yace "Toh" motarsa ya bude don makullin na hannunsa ya shiga, Abba kuma ya shiga cikin gida, Mujaheed ya ja motar ya fita compound din. Mujaheed na dawowa daga siyo Tsiren da Abba yace ya nufi part din su Imaan, a hankali ya kwankwasa kofar sannan ya murda yaji a bude, shiga parlon yyi, ya sauke idonsa bayan sun hada ido da Ammi yace "Gashi Abba yace a kawo mata" Ammi ta kwalo ma Imaan kira don tana bedroom dinta, ko me ta tuna sai kuma ta mike xata amshi ledan sai ga Imaan ta fito sanye da kayan barcinta, xata shigo parlon Ammi ta dinga mata wani kallo, da sauri ta juya ta koma dakin ta rufe kofar, Ammi ta karbi ledan ta nufi dakinta ba tare da ta amsa sai da safensa da ya mata ba, juyawa yyi ya fita parlon ya kulle kofar. Washegari daga Imaan har Ammi suka yi mamakin xuwan Daddy ba notice, Bayan Daddy ya shiga bedroom Ammi ta bi bayansa, xaune ta samesa gefen gado tace "Yallabai xuwa babu notice, hope lafiya dai" Yace "Ehh I came for something urgent, xuwa lahadi xan koma in sha Allah" tace "Allah ya kai mu" shiru yyi hakan yasa tace "A kawo maka breakfast ne?" Yace "Noo, Ina son maki wani tambaya, Imaan tana da wani ne dake nemanta?" Ammi tayi shiru tana kallonsa a bit shocked, can tace "Lafiya Yallabai?" yace "I am asking you..." girgixa kai Ammi tayi, she have got no option then to protect her daughter, a hankali tace "Not at all, ita da bata xuwa ko ina daga boko sai islamiyya, is there any problem" yace "Ohk" mikewa yayi ya shiga bathroom ita kuma ta fita a sanyaye tana mamakin tambayar, to me kuma ya faru, tana fita parlor tayi still don sai a sannan ta tuna abinda Imaan tace inna tayi jiya, wato har inna ta kirasa kenan ta gaya masa, daki ta tafi gun Imaan, tana kallonta tace "kin ga abinda nake guje maki ko, to ina jin inna ta kira Daddyn ki har ta fada masa xancen yaron jiya, without any doubt abinda ya dawo da shi kenan" Imaan ta xaro ido a tsorace tace "Daddy ya maki maganan ne?" Ammi tace "Dama tun ba yanxu ba nace maki ba ruwana kar ki ja min matsala, gaskiya sai ki san abinda xa ki ce ma Daddyn ki, don't involve me in this" daga haka ta fita dakin, imaan ta kasa xaune waje daya gabanta ya dinga faduwa hawaye cike idonta, daga karshe ta fice a dakin, direct part din inna ta nufa hawaye cike idonta.... shigar Mujaheed parlon kenan ya je gaisheta daga inda yake tsaye, ko amsa gaisuwarsa bata yi ba tana kada shayi a kofi tace "Ni fa Mujaheed tsabar yanda nasa maganar jiya a rai har mafarkinsa sai da nayi wlh, wai ga Imaan a daula iya daula babu abinda babu a runtumemen gidan na more rayuwa, har naje masu sati biyu, in gaya maka yau... a kawo min kaji, gobe.... a kawo xabee, gata... a kawo kwayakwayay, citta... a kawo tika tikan Kifaye, ga gwangwanin madarana da bournvita da suga an min dak'en da shi a daki, nayi wani jazur da ni sai sheki nake malam, Shi ko bulasawan kullum xai fita sai ya ajiye min dubu biyu in sa kati, wllh tllh ba karya nake maka ba Mujaheed" Mujaheed dai na tsaye daga bakin kofa yana kallonta, ta tabe baki ta yagi bread ta kai baki tace "Ni dai ba ruwana, Ahmadu ya shigo in san yanda suka yi da Bukar din" Jin an bude kofa Mujaheed ya juya, imaan ta shigo ko takalmi bata cire ba, tana kallon inna kamar xata fashe da kuka tace "Inna me kika ce ma daddy na?" Inna tace "Waye kuma Daddyn ki?" Imaan tace "Wai ni nace maki wanda kika gan ni da shi jiya saurayina ne??" Inna ta kyabe baki tace "Kya ji da shi, ni dai baxan kula ki ba ki xageni, na riga na gama maganata, wllh Mujaheed baka ga yanda ta ji kunya ba jiya da ta gan ni kamar fa ta nutse, ni dai ban bi ta kanta ba ban kuma kulata ba bakina a leko na ja Bulasawan muka shigo ciki, to kuma meye xata shigo min ta tale baki kamar wata agwagwa? Ni dai ba ruwana" Mujaheed ya juya ya fice daga parlon... imaan ta durkushe wajen tana kuka sosai tace "Wllh idan kika sa Daddy ya min fada ko
Chapter 82 · 0% Book details