← Book details Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 242 OF 300

Sashe 242

Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read

*Imaan isn't for free* it's 300 via

Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788

Ganin direction din da Mujaheed ke kallo bbu ko kiftawa Safeenah ta juya da sauri tana kallon wajen ita ma, sake remote din hannunta tayi a hankali ta mike tana kallon Imaan da idanuwanta kamar xa su fito, da mugun mamaki da shock take kallon nata, lkci daya ta juya cikin tashin hankali tana kallon Mujaheed xuciyarta na bugawa kamar xai fito, walking slowly ya karasa cikin parlorn ya xauna saman kujera ya bude takeaway din dake cikin leda ya diba abincin a plate ya ajiye sannan ya daga kai ya kalli Safeenah dake kallonsa har lkcn with full shock, sai kawai ta fashe da wani matsanancin kuka jikinta na rawa ta nufesa ta rikosa tace "Tell me, what is she doing in our home Mujaheed? Why is she here? Wa take nema??" Juyawa Imaan da ta hade rai tayi xata koma sama, Mujaheed yace "Don't go back, dawo nan" k'in tsayawa tayi tana ci gaba da tafiyar ta da sauri, cikin daga murya yace "Imaan!!" ta tsaya fuska daure amma ta ki juyowa, har ranta taji xafin ganin Safeenah, ga wani faduwa da gabanta yake yi, Mujaheed ya mike tsaye yana kallonta yace "I said come back here Imaan..." Safeenah na jijjigasa cikin tashin hankali sosai tace "Mujaheed answer my question, ka gaya min me yarinyar nan take a gidana, ka gaya min nace, wa take nema??" Imaan ta juyo walking slowly ta dawo parlon tana kallon Safeenah fuska daure, Safeenah ma ta dinga kallonta xuciyarta na bugawa har lkcn tana rike da Mujaheed, Imaan ta murguda mata baki ta dauke kai tana jiran jin kiran me Mujaheed yyi mata, Safeenah ta nufeta da sauri tana huci bakinta na rawa tace "Me kike yi a gidana??" Imaan ta rungume hannunta tace "Abinda kike yi, and point of correction ba gidan ki bane ke kadai, nima nan gidana ne...." Wani kara Safeenah tayi kamar mahaukaciya jikinta na rawa tace "Karya kike wllh, karya kike, nan gidan mijina ne, gidana ne nan, baki da space a gidan nan yarinya, this is my husband's house" Imaan tayi wani murmushi tace "Koh? To sai ki tambayi mijin ki dalilin da ya sa ya kawo ni nan" Sai kuma ta saci kallon Mujaheed da ya ki kallonsu gaba daya, murya can kasa tace "And here is also my husband's house...." Bata rufe baki ba Safeenah ta wani cakumota da karfi jikinta na rawa, Mujaheed ya taho da sauri ya janye Imaan yana ma Safeenah wani mugun kallo, ya fixgota shi ma cikin tsawa yace "What is this u are doing? Baki da hankali ne xaki fixgota haka? Ciwo xa ki ji mata?" Safeenah na kallonsa with shock ta fashe da matsanancin kuka ta xube kasa tace "Na shiga uku na lalace, Mujaheed kayi ma Allah ka gaya min me take a gidan nan Plss, tell me what brought her to my home" Wani dogon tsaki Imaan ta ja tana hararanta xata bar wajen Safeenah ta mike yi kanta gadan gadan, cikin xafin nama Mujaheed ya fixgota for the second time yana mata wani kallon da ya sa hanjinta ya kada, strictly yace "This should be ur last attempt in this house, I will neva take it likely with you idan kika sake maimaita hakan, Me kike son yi mata da??" Safeenah na kuka sosai tace "Wllh baxan xauna da yarinyar nan ba mutuwa xan yi, ka taimakeni ka gaya min me take yi a gidanmu, wayyo Allah na na shiga ukuuu..." Mujaheed ya saketa, calmly yace "Aure ya kawota gidan nan, ita din xabin mahaifina ne gareni, kamar yanda ke kike xabin mahaifiyata, at that time I've neva for once say no to my mother na karbi auren ki hannu bibbiyu, the only difference btwn my marriage with you and that of Imaan is that, ke naki I was aware and present during the nikka.... Don haka kamar ynda ban ma Mahaifiyata musu a kan auren ki ba, to baxan ma mahaifina musu a kan auren Imaan ba, and I am assuring you that in sha Allah xan xamo mai adalci tsakanin ku, i will try my very best, but Imaan matata ce yanxu kamar yanda kike matata...." Imaan dake tsaye tana jiran ganin abinda Safeenah xata mata, ta kara jan wani dogon tsaki ta wuce sama kamar xata tashi sama, Mujaheed ya bi ta da ido, Safeenah ta sulale kasa ta rushe da wani kuka da karfin gaske, cikin tashin hankali tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na cuce kai na, don Allah Mujaheed kar ka min haka don kaga Ina sonka, babu mai kishiya cikin 'yan uwana wllh tllh, plsss kar kace min kishiyata ce ita, I can't stand it, xuciyata bugawa xata yi wllh...." Dukawa yyi yana kallonta smiling calmly yace "Kin yi breaking record..." Tun da Imaan ta koma daki ta kasa xaune ta kasa tsaye, ta kalli kofa ya fi a kirga, tsayawa tayi jikin window ta fara kukan da ita ma bata san dalilinsa ba, wani tukuki taji xuciyarta na mata, tana ta tsaye har bayan kusan minti goma, aka bude kofar dakin, juya baya tayi da sauri ta goge idonta tana kallon waje fuska daure, ya rufe kofar yana kallonta yace "She is my wife imaan, aside that kuma ta girme ki sosai, kada ki sake mata tsaki, that's very disrespectful of you...." juyowa tayi tana kallonsa da wani expression, ya karasa kusa da ita kafin yace komai, cike da masifa tace "Wllh sai na mata din, da ta girmeni sai kuma ta haifeni? Ni ina ruwana da ita a gidan nan xaka ce min she is ur wife ko da nace maka ban sani bane? What's my business with that??" Sai kuma ta fashe da kuka ta nufi bathroom da sauri ya rikota yace "No I am only reminding you Imaan" fadawa jikinsa tayi tana kuka sosai tace "Ni wllh Yaya bana son gidan nan, I don't want to stay here, na tsane ta da gaske, baxan xauna ina ganinta ba kullum, I don't like her, bayan ta gama xagi na saura kadan to dokeni kuma kaje kana ta bata hakuri tun daxu fa.." tana fadin haka ta kara rushewa da kuka har da shessheka tana shigewa jikinsa, rungumeta yyi yana sauraronta da mamaki, sai kuma yyi murmushi a hankali yace "Toh ya kike son ayi?" Cikin rawar murya tace "Ni dai mu tafi wani gidan kuma kar ta bi mu wllh..." Yace "Kin hakura xa ki xauna da ni kenan yanxu?" Still tayi da farko, lkci daya kuma ta janye jikinta daga nasa da sauri ta juya masa baya tana imagining abinda ta fada, murmushi kawai yake yana kallonta, ta turo baki tace "Ni baxan xauna da kai ba" daga haka ta wuce cikin bathroom da sauri ta rufe kofar, juyawa yyi ya fita dakin still smiling. Lallashi bbu irin wanda Mujaheed bai ma Safeenah ba domin a rayuwarsa ta duniya ya tsani kukan mace, kukan ma wai sabida shi, amma kamar yana dada tunxurata, da ta tuna biye ma Umma ya ja mata wannan masifa da tashin hankali sai ta kara rushewa da kuka tana tunanin me xata ma Umma taji dadi a ranta, gani take kamar ta kusa farkawa da mummunan mafarkin nan da ke neman fasa mata xuciya, sai lkcn ta san meye kishin abinda kake so, gashi ta kasa ko da kiran Hajiyarta ta sanar mata ai fa kishiya na nan daram, tsoro take kada tace mata ta dawo gida don har xuciyarta take jin baxata iya rabuwa da Mujaheed ba har abada, rabuwa da Mujaheed mutuwar ta kenan a ganinta, ta rikosa tana kuka sosai tace "Wllh ina sonka Mujaheed, Ina son kasancewa da kai amma baxan iya xama da yarinyar nan ba idan ma record din gidanmu xan yi breaking ba da wannan yarinyar ba gwara ka saketa ka auri wata na yadda, Allah da gaske ban son ganinta ko na second daya, yanxu kana nufin kun hada gado da yarinyar nan?" Mujaheed ya saketa ya mike yace "Baki son ganina kenan idan baki son ganinta, don she is me" Bai jira sauraronta ba ya shige toilet din dakin yin alwala, har ya fito kuka take tayi dai dai a kasa kamar warce uwarta ta mutu, ya nufi kofa ya fita dakin, bedroom din sa ya nufa ya bude a hankali yana kallon ciki, fitowar Imaan kenan daga bathroom ta dauro alwala ita ma, ta wani hade rai ta dau hijab dinta ta sa tana shimfida darduma, cire makulli yyi ta ciki ya kulle dakin da makullin sannan ya tafi masallaci bayan ya saka makullin a aljihu. Mujaheed na dawowa masallaci ya shiga dakin da Safeenah take, kamar yanda ya bar ta haka ya dawo ya sameta, Yana tsaye dakin yace "Baki ma yi sllhn ba kenan?" Banxa tayi masa tana kuka sosai, ya tabe baki yace "Xa mu fita in siyo mata few wears coz gaba daya kayanta na gida" Safeenah ta mike da sauri tana xaro ido tace "Xaku fita fa kace Mujaheed??? Har xaka fara walakanta ni kenan kake nufi, xaku fita kake ce min fa" yace "You heard me right, we are going to the market, kuma don't forget cikin one week dinta muke..." Kallonsa kawai Safeenah take kamar idanuwanta xasu yo waje xuciyarta na bugawa, yace "Her one week started from yesterday" Bai jira cewarta ba ya fita dakin ya kulle kofar, imaan na xaune saman darduma ta hade kanta da gado ya sameta, Yana kallonta yace "We are going out now" Ta dago da sauri tana kallonsa tace "I am going no where plss" Yyi shiru yana kallonta, sai kuma yace "Ohk dama shopping xamu je ki yi, bari mu je da Safeenah tayi maki kawai" Mikewa tayi da sauri tace "Tayi mani a kan me? What's my business with her? Ko ita xata sa kayan da xata min shopping??" Bata jira cewarsa ba ta nufi kofa ta fice, murmushi yyi ya bi bayanta, waje ya sameta tsaye jikin motar, ya bude lock din motar ta bude front xata shiga suka yi ido hudu da Safeenah dake lekosu ta window tana kuka kamar ranta xai fita, Imaan ta ji dadin hakan har ranta, ta kalli Mujaheed sai kuma ta nufe sa da sauri tace "Toh ai baka gama saka buttons din ba" Bata jira cewarsa ba ta fara buttoning din masa shirt dinsa, kallonta yake da mamaki, ta turo baki taki yarda su hada ido har ta gama sannan ta juya ta koma gun motar ta shiga ta rufe tana satan kallon windown dakin Safeenah tana d'an murmushi, Mujaheed ya bude gate sannan ya dawo ya shiga driver seat yana kallonta murya can kasa yace "Kema bari in gyara maki Hijab din ki" Bai jira cewarta ba ya jawota kusa da shi yana gyara mata hijab duk da bbu abinda ya samesa, xata turasa sai kuma ta tuna kila Safeenah na nan tana kallonsu, hakan yasa ta tsaya ta matsa kusa da shi amma bata yarda sun hada ido ba, unexpectedly taji bakinsa cikin nata, ta xaro ido a mugun tsorace xata kwace kanta ya ki saketa. Siyayya ba na wasa ba Mujaheed yyi ma Imaan, duk ita ke daukan kome taga yyi mata, tun daga inner wears, dogayen riguna, kananun kaya, amma fa gaba daya fuskarta a daure yake sbda abinda yyi mata daxu, da ta tuna sai ta goge bakin, sau dayawa sai ta dau kayan da yyi mata kyau sai ta juya gunsa da sauri tana nuna masa kayan tace "Yaya wannan xai min kyau koh??" sai kuma ta tuna sabon relationship dinsu, a hankali take juya masa baya tana turo baki bar wajen fuska daure, shi dai sai dai yyi murmushi yana biye da ita, bayan sun gama da boutique suka shiga shopping mall, gun turarruka ta nufa shi kuma ya tafi gun kayan shayi don siya masu, Tana cikin daukan turare suka yi ido hudu da farida dake duba wani turaren a wajen ita ma, xaro ido imaan tayi da mamaki ta nufeta da sauri tace "Anty Farida" Rungume ta Farida tayi cike da murnan ganinta tace "Imaan, what are you doing in Zaria?" Imaan na murmushi sosai tace "Ni da Yaya ne Aunty Farida, dama Zaria gidan ki yake?" Farida da lkci daya fara'arta ya d'an ragu, a hankali tace "Ehh nan nake, me kika xo yi nan din ke?" Lkci daya fara'ar da ke fuskar imaan ya bace ita ma jin tambayar da ta mata, sai kuma da sauri tace "Lahh ni da Yaya ne Aunty, bari in kirasa ku gaisa" Bata jira cewar Farida ba ta bar wajen da sauri, Farida ta bi ta da kallo sannan ta sauke idonta kasa a hankali, Mujaheed na duba blue band sanin Imaan na son ci sosai, ta iso inda yake, daga kai yyi yana kallonta, ta wara ido tace "Yaya I just met Aunty Farida now" da mamaki yace "Farida? Where is she?" Imaan tace "Wajen perfumes" sai kuma ta kamo hannunsa kamar xata yi kuka tace "Don Allah Yaya don't tell her that we are married plsss" da mamaki yake kallonta trying hard not to laugh yace "Why???" Hankali tashe tace "Wlh abun kunya ne wannan Yaya, ya xa ayi ace wai kai mijina ne bayan kowa ya san kai yayana ne, don Allah kar ka gaya mata wllh xan ji kunya sosai" Murmushi yyi yace "Toh na ji, mu je...." Tana rike da hannunsa suka tafi inda Farida take, shi dai bin ta kawai yake yana kallonta har suka iso wajen, Imaan na kirkiran murmushi tace "Aunty ga yayan, shi ma yyi aure few months ago, wajen matar ma na xo in mata kwana biyu"
Chapter 242 · 0% Book details