Sashe 199
Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
kiji, wllh da Mujaheed ya aure min jika gwara tayi ta xama ba aure ina kallonta, me xata ci da sauran Safara'u Allah na tuba?? Me xata yi da surka irin Rukayya ta6a66iya, ke ma dai wllh muguwa ce ta Rasulu, waye kuma Mujaheed da xa ki ce ya aurar min Imaan in shiga uku in lalace, Ina Imaan xata kai sa, ke dai wllh fitinanniya ce tirrrr" Mikewa Imaan tayi ta wani hade rai ta nufi kofa, Inna ta hade rai tace "Atoh maxa yi tafiyar ki Imaan kada a sa min ke a bakin duniya, Toh ni dai tunda kin gama ganin kaya tashi kiyi tafiyar ki ta Rasulu ba ruwana kar ki kawo mana rudani a lamarin mu, tunda ke rudaddiya ce, tashi ki tafi haka a gaida su Muhammadu" Ta Rasulu tace "Toh banda Mujaheed din dama wa xai iya da ciwace ciwacen Imaan Allah na tuba, ni fa tunda Uwar Bulasawa ta kore ni da d'ana ta hanamu abinci na tsaneta har yau" Inna tace "Toh ae ba ni da Ahmadu ta kora ba ta Rasulu, kuma ko da ni ta kora ma xuciyata me kyau ce fesss na yafe mata duniya da lahira, ke dai kawai kiyi ta kanki ta Rasulu, bikin ma ni bance lallai sae kin xo ba kar ki kunya ta ni don Allah ki rufa min asiri kiyi xaman ki a gida kin ji???" juyawa Mujaheed yyi ya fita parlon, Inna ta bi sa da harara tace "Waye kuma Mujaheed da xan hada jikata da?? Kai Allah dai ya isa da wannan tunanin naki gaskiya" Washegarin ranan Imaan suka fara jarabawan waec, karfe biyu saura suka tafi yin first paper dinsu, xuwa hudu da wani abu suka gama suka fito, tunda suka fito Maimoon ke kallon Imaan da ta nemi dakali ta xauna, Maimoon ta karasa kusa da ita tace "What happened Imaan?" Imaan ta kalleta a hankali tace "Kamar bana jin dadi" Maimoon tace "Toh sannu yanxu driver xai xo sai mu wuce gida" Mariya ta nufo su tace "Amaryar mu how was today's paper?" Imaan tace "Alhmdllh" Mariya tace "ki taso ku gaisa da Ya sadeeq yana waje, yace in kira ki" Imaan ta d'an turo baki tace "A'a ni dai kice masa baki gan ni ba plss" Mariya tace "C'mon ki taso mu je plss how will I say ban gan ki ba" Maimoon ta dago Imaan tace "Mu je kila ma Driver ya xo" Maimoon na rike da hannunta suka fita wajen gate din makarantar, a hankali Imaan ke tafiya har suka isa gun motar Sadeeq ta tsaya, ya dinga kallonta daga glasses din idonsa yace "What's wrong?" Mariya tace "Nima na tambayeta daxu tace ba komai" bude motar yyi ya fito yana kallonta daga sama har kasa yace "Me ke damun ki?" Kamar xata yi kuka tace "Ina yini?" Yace "I said what's wrong?" Ta sunkuyar da kai tace "I am not feeling fine" Back seat ya bude mata yace "Shiga in ajiye ki gida" ta buda ido sosai tace "Driver dinmu na xuwa" kallonta kawai ya tsaya yi, hakan yasa ta kalli Mariya, Mariya tace "Ki tafi xa mu taho yanxu" Sadeeq yace "Kema shiga mu je may be baxata yi tunanin guduwa xan yi da ita ba" dariya Mariya tayi tace "Toh kuma driver yana hanya, ku tafi kawai xa mu jira shi da su Ummi" ta fadi haka tana nuna masa Ummi dake can tsaye sai kallonsu take suna kallon direction dinta kuma ta dauke kai da sauri, a hankali Imaan ta shiga bayan motar, Mariya kuma ta shiga front seat, ya rufe motar ya xaga ya shiga maxaunin Driver ya tada motar suka bar kofar makarantar, tun da suka dau hanya yake kallonta ta madubi, ita ko ta jinginar da kanta ta rufe ido, har suka isa gida, parking yyi bakin gate yana kallonta ta madubi still, can ya bude motar ya fito ya dawo baya ya xauna, sai a sannan yasan bacci take da gaske, ya kai hannu forehead dinta ta bude ido da sauri ta koma baya, yyi kasa da murya yace "Ina ke maki ciwo?" Ta sunkuyar da kai tace "Ina jin xaxxabi" yace "Tun yaushe??" Tace "Da safe" shiru yyi bai ce komai ba, can ya sauka motar yana kallonta yace "Come down" a hankali ta fara sakkowa motar ya kama hannunta don taimaka mata, xata kwace hannun ya ki saketa, Bata yarda ta kallesa ba ta fito motar, yana kallonta yace "Anjima xan xo maki da drugs" tace "Toh nagode" saketa yyi ta juya xata shiga gate suka yi ido hudu da Mujaheed dake kallonsu yana xaune gun mai kiosk dake layin, ta dauke kai da sauri ta shiga gate din, duk da hada idon da Sadeeq yayi da Mujaheed shigewa motarsa yyi ya tada ya bar layin.