Sashe 225
Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hajiya Mansura tayi wani murmushi tana kallon kawayenta tace "Rukayya ta debo ruwan dafa kanta, wato da sa hannunta da contribution dinta a yi ma 'ya ta kishiya.... To xata san da Hajiya Mansura take, xata san da sa hannunta ayi ma diyata kishiya, ita da d'an ta daga wnn lkcn sai dai hange daga nesa, kishiya kuma Safeenah baxata xauna da ita ba, kaf xuri'ar mu babu mai kishiya kuma baxa a fara a kanta ba, ku mu tafi kawai...." Hajiya Baturiya ta daga Safeenah dake rusa kuka kamar ranta xai fita tace "Babu abinda kukan nan xai amfane ki da, ki tashi mu tafi tun wuri a san abun yi, sai Hajiya Rukayya ta san da family din Alhaji Usman take...." Cikin kuka Safeenah tace "Mummy yar uwarsa mai min rashin kunya a gidana fa aka aura masa, wannan fitsararriyar ce fa mai min kallon banxa ce, Mummy ya xa ayi ta aurar min miji na shiga uku na lalace, da na sani da ban biye uwar Mujaheed ba, ashe yaudarata take da Mujaheed take son ayi auren, Mummy sai kinga yanda yake ji da yarinyar, Mummy ya xan yi da raina idan aka kawo min ita gida a matsayin kishiya, wayyoo Allah na..." A fusace Hajiyan Marafa ta buge bakinta tace "Uban wa xai kawo maki ita gida a kishiya?? ai wnn gidan naki ne ke kadai har duniya ta nade, sai dai idan ba tsatso na kika fito ba, Mujaheed naki ne ke kadai, hatta uwarsa Rukayya sai dai ta gansa daga nesa, wa ke ta wani amaryar ga babban shaidaniya annamimiya da xa mu fuskanta, in sha Allahu sai na toxarta Rukayya toxarci mai girma kuwa, sai tayi da ta sanin sani na..." Daga haka ta ja ta xuwa cikin mota tana huci, duk suka shige cikin mota suka bar gidan, Umma dake labe jikin window tana kallonsu ta share xufar dake ta sauka fuskarta ta koma gefen gado ta xauna tana tunanin abun yi. Inna na kallon Mama Hadiza da Aunty tayi wani murmushi tace "To kun dai jiye ma kunnan ku komai, ni tun ba yau ba nasan Rukayya na xuwa gun boka da malamai, amma wllh tllh in har da sa hannunta a rugujewar auren jikata ita ma nata auren na lilo tangal tangal yanxu...." Sai kuma Inna ta fashe da kuka sosai tace "Allah dai ya hada Ahmadu da jaraban duniya, Rukayya jaraban duniya ce, wato hade kai tayi da surka suna xuwa gun boka bbu kunya ba tsoron Allah, Ni dai wlh in har aka binciko min aka gano cewar ita ta wargaza auren Imaan akwai tashin hankali a gidan nan gaskiya, don da kai na xan yi fatali da kayanta waje, dama darajan Mujaheed kawai take ci a wajena" Mama Hadiza ta sauke ajiyar xuciya tace "Ni na ma rasa abun cewa wllh..." Inna tace "Yo ba dole ba, kuma fa tana ciki tana jin su, wa ya sani ma ko xawo ta dinga saki a dakin, ni dama ciki suka shiga suka kamata su lakada mata duka da cacan bakin da suka dinga yi tsakar gida" Mama Hadiza tace "Toh Inna kin san halinta kuma me yasa xaki kare ta a wajensu?" Inna tace "Ka ji ki ke kuma, ke baki ga yanda jikinsu yyi sanyi ba, ai ynxu mance batun kishiyar da aka ma Safara'u xa su yi su fuskanci Rukayya su yi fata fata da rayuwarta, ai bamm na hada mata...." Dariya sosai Aunty tayi tana kallon Inna, Inna tace "Lallai ba ku san ni ba kenan har yanxu, Ahmadu da Bukar kawai nake jira su dawo daga gidansu bafillatanar can da ta gudu min da jika su ji wnn abun al-ajabin, dama Ta Rasulu sai da tace min bata yadda da fasa auren nan da Bulasawa yyi ba, shi sa ma yau da sassafe ta tafi don xuwa binciko mana m ke faruwa, na rantse da Allah in har da sa hannun Rukayya a fasa auren nan sai nayi sanadin karshen xamanta a gidan nan..." Tana fadin haka ta tashi ta wuce daki, Mama Hadiza ta girgixa kai tace "Rukayya tayi asara duniya da lahira, yanxu meye amfanin surkai su xo tsakar gida suna maki cin mutunci haka, ni wllh Mujaheed nake tausayi bai yi sa'ar uwa ba kwata kwata, tun fa ba yau ba ake abu daya da matar nan ta ki sa Allah a ranta, anya Rukayya xata gama da duniya lafiya kuwa??" Aunty dai bata ce komai ba amma ita ma mamakin maganganun Hajiyan Marafa da tawagarta kawai take... Karfe sha biyu saura Gwaggwo ta shiga parlon Inna da sallama, Imaan dake sanye da Hijab har kasa da Nikab na biye da ita a baya, Inna dake xaune parlon tare da Mama Hansai ta amsa sallaman, Imaan ta wuce daki walking slowly, Inna tayi ma Gwaggwo kallo daya tana sakace hakori ta dauke kai, Mama Hansai ta shimfida mata darduma tana mata sannu da xuwa, Gwaggwo ta xauna bayan sun gaisa da Hansai tace "Sannu Hajiya Asabe" Inna ta kalleta tace "Yauwa sannu Hajiya Biba, amma a gaskiya ki dinga sa 'yar ki a hanya, kwata kwata Aisha bata ji bata maida ni bakin komai ba, ya xata maida kanta mahaukaciya daga anyi abu don fitar da mu kunya gaba daya, kema kuma baki son gaskiya don da kina son gaskiya tun jiya ya kamata ki tiso keyarta ki koro su, nan nan nace mata kada ta je ko ina amma yarinyar nan ta ki saurarata, gaskiya raina ya baci matuka don tun tsakar daren jiya nayi niyar tahowa gidan in sameta su Ahmadu suka hanani" Gwaggwo dake ta saurarenta tace "Allah ya kyauta, a dai ta hakuri..." Inna tace "Atoh, tamkar yar ciki na na dauketa amma dubi iya shegen da ta min, kowa a gidan na ya girgixa da auren nan, to amma abinda hakuri bai yi ba rashinsa xai yi? ni fa har cewa nayi sai Mujaheed ya rubuta takarda amma d'an banxan ya gudu da dukkan alama yana so, to yana so mana tunda tun jiya bbu shi bbu alamarsa ya shiga duniya" Gwaggwo tace "Toh Allah dai yasa hakan ne mafi alkhairi, ga ta nan dai na kawota, ba ma ta jin dadi amma tunda nayi ma iyayenta alkawarin dawo da ita shi sa na maido ta yanxu" Inna ta yo waje da ido tace "Kuma bata da lafiya sai ayo min nan da ita, ta fito ta koma barin su ai Hadiza na can" Gwaggwo ta mike tace "Ni dai xan koma Hajiya Asabe Allah ya sanya albarka" Daga haka ta nufi kofa, Inna tace "Toh ko ruwa baxa ki sha ba" Gwaggwo tace "A'a nagode, sai anjima" daga haka ta fita parlon, Inna ta tabe baki tace "Aisha dai ta lalace wllh" tana fadin haka ta tashi ta tafi daki gun imaan, kwance ta sameta ko nikab din fuskarta bata cire ba, Inna ta tuge nikab din ganin yanda idonta yyi jajir ga jikinta yyi xafi ba kadan ba tace "Ae ni na shiga uku, fasa auren da Bulasawa yyi yasa kika rame haka kika sa ma kanki ciwo Imaan?" Imaan ta mike xaune da kyar hawaye na saukowa idonta ta kamo hannun Inna cikin rawar murya tace "Don Allah Inna ki taimakeni, wllh shi fa Yayana ne taya xa ace ya aureni???" Inna ta marairaice tace "Nima dai shi na gani, wnn uban sa6o har ina ni patuu, sai kuma ace kinyi ciki kin haifa masa 'ya ya ko? To ta ina xa fara wannan ta6aran ni Asabe??" Imaan ta fashe da kuka sosai ta rufe kanta da pillow tana shessheka, Inna ta xauna gefen gado tayi tagumi tace "Anya su Ahmadu da Bukar suna da hankali kuwa ni Patuu? A ina suka ta6a ganin anyi haka tukun??" Imaan dai kuka kawai take kamar ranta xai fita, Inna tace "Naga abinda ya isheni...." Mama Hadiza ce ta shigo dakin bayan sun hadu da gwaggwo a compound sun gaisa ta sanar mata ta dawo da Imaan, Inna na ganinta ta mike tace "Hadiza anya su Ahmadu na da saiti kuwa, ta ina Imaan da Mujaheed xa su yi aure ne wai ban gane ba, yayanta ne fa Hadiza?" Mama Hadiza tace "Kamar ya Inna?" Inna tace "Toh abinda tace min kenan wai yayanta ne kuma haka ne wllh yayanta ne" Mama Hadiza na kallon imaan tace "Halan baki je islamiyya bane Imaan???" Inna ta daure fuska tace "Kaji wata magana, yarinyar da ta haddace kur'ani har sauka tayi aka bata kyaututtuka kice bata je islamiyya ba Hadiza??" Mama Hadiza na kallon Imaan fuska daure tace "Ta ina Mujaheed ya xama Muharramin ki? Ko kin fara hauka ne? Idan an kai ki gidan sai ku ci gaba da xaman yaya da kanwa a can, amma na sake jin kince yayanki ne sai na bata maki rai wllh, shashasha kawai...." Murya can kasa Inna tace "Atoh dai, nima ban san ta ina ya xama yayanta ba, ubanta Bukar ubansa Ahmadu, uwarta Aisha uwarsa Rukayya" ko kallon Inna Mama Hadiza bata yi ba ta juya ta fice daga dakin, Inna ta xauna gefen gado tayi tagumi tace "Gashi har yanxu shiru bbu Mujaheed din babu labarinsa, ko shima yana can yana ta damuwar an hada sa da kanwarsa ne" ita dai Imaan bata ko kalleta ba sai kuka take a hankali. Har Inna ta gama tsarinta kallonta kawai Abba da Daddy suke yi, Inna tace "Wllh kuwa Ahmadu, motocin da suka shigo sun yi biyar ga dai Hadiza shaida, to shine nace gaskiya idan maganganun iyayen Safara'u ya tabbata kashin Rukayya ya bushe a gidan nan kuma xamanta ya xo karshe, ynxu dai muna bin komai a hnkli ne don ba mu gama tabbatarwa ba tukun, duk da dai gaskiya tun ba yau ba nasan Rukayya na shige shige" Abba dai kansa na kasa, Daddy kuwa har xuciyarsa bai yrda da xancen Inna ko na second daya ba, can ya mike yace "Inna lkcn Asr yyi xan tafi masallaci ynxu" Daga haka ya nufi kofa Inna ta bi sa da kallo sannan ta kalli Mama Hadiza tace "Irin na xauna ina shirga masu karya din nan, to in sha Allahu a gabansa asirin Rukayya xai tonu dumu dumu..."