← Book details Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 300

Sashe 68

Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bayansa, Maimoon na yar dariya ta tashi ita ma ta shiga parlon, wata yarinya da baxata wuce ashirin da daya bace ta shigo parlon daga dinning kallo daya tayi masu ta wuce sama, tsaki imaan ta ja Mujaheed ya kalleta ta cinno baki ta dauke kai, mai aikin ta kawo masu drinks da bottle water ta ajiye, bayan wani lkci sai ga Hajiyar ta sakko cikin shiga ta alfarma ganin Mujaheed tace "A'a ashe kai ne doctor" yyi kasa da kai yace "Ina yini Hajiya" tace "Lafiya Alhmdllh, ya Hajiya Rukayyar, fatan an watse taro lafiya" yace "Alhmdllh" xaunawa tayi tana kallo su Maimoon da Imaan dake gasiheta tace "Wannan kamar kanwar khadijah da tayi aure Us koh?" Ta fadi haka tana nuna Maimoon, Mujaheed yace "Ehh kanwarta ce" tace "Maa sha Allah ga kamanni na gani, to ita wannan fa" Mujaheed ya kalli Imaan da ta nuna, da sauri yace "Yar uwarsu ce" tace "Allah sarki shi sa ban santa ba" Maimoon ta mike ta ajiye abun hannunta kusa da ita tace "Gashi Hajiya tace a kawo maki" Hajiyar tace "To maa sha Allah, nagode kwarai Allah ya basu xaman lafiya" Bude kofar parlon aka yi, wata yarinya ta shigo parlon cikin English wear bata ko kalli wa enda ke xaune parlon ba xata wuce sama Hajiya tace "Safeenah lafiya na ga ranki a bace" Jin sunan da Hajiyar ta kira Mujaheed ya daga kai yana kallon yarinyar, ita ba doguwa ba kuma ba gajera ba, farin ta har yayi yawa and she is beautiful, lkci daya ya dauke kansa, Maimoon da Imaan kuwa kamar sun samu TV imaan har da juyawa gaba daya tana facing dinta, rai bace Safeenar tace "Wai ki ji mum ashe birthday din ma wani local waje xa ayi, sai kinga yanda raina ya bace bayan duk shirin da nayi, wllh Saleema koluwa ce I don't know what's wrong with her, ni ko gaya masu na tafi ma ban yi ba" Mujaheed dai sai danna wayarsa yake, Hajiya tace "Atoh gaskiya basu kyauta ba, to why not baki ce masu a canxa hall din ba, ko ke ba sai ki biya kudin hall din ba" Tsaki Safeenah tayi tace "Ni duk raina ya baci wllh Mumy" xata wuce sama Hajiya tace "Toh ga doctor ku gaisa" Juyowa tayi tana kallon cikin parlon taga Mujaheed da ya ki dago kansa, ta fi second goma tana kallonsa, kafin ta karasa cikin parlon ta xauna hannun armchair da uwarta ke xaune cikin sanyayyen murya tace "Ina yini" sai a sannan ya daga kai yace "Lafiya lau, ya kike?" Tayi wani sanyayyen murmushi tace "Lafiya lau" Ta kalli su Imaan tace "Sannun ku" Imaan dai tace "Yauwa" Maimoon kuma ta gaisheta, Hajiya ta kwalo ma mai aiki kira ta fito da sauri, Tana kallonta tace "Pepper chicken da ku ka yi daxu xa ki kawo masu tun da ba ku gama lunch ba" Mujaheed yace "Daga gida muke yanxu Hajiya, we ate before leaving, so we are okay" tun da ya fara magana Safeenah ke kallonsa ko kiftawa babu har ya dasa aya, Hajiya tace "Wannan ae is more or less a dessert, daxu yara suka ce suna son pepper chicken, shine nasa su yi, kuma da yawa sosai suka yi don nasan baxa a cinye gaba daya yau ba sai dai a ba masu gadi da almajirai" Mujaheed ya d'an yi murmushi yace "Ni dai I am okay" Imaan tace "Ni dai xan ci" kallonta yyi da sauri, Hajiya tace "Yauwa, bar sa yayi ta fulako dama yayi kama da fulanawan, ke ma ai xa ki ci ko" Hajiya ta fadi tana kallon Maimoon, Murmushi kawai Maimoon tayi ta sunkuyar da kanta, mai aiki ta dawo rike da tray da plates uku a kai, ko wanne dauke da kaxa da aka yi garnishing sai kamshi da turiri yake, Mikewa Safeenah tayi ta dau plate daya ta karasa kusa da Mujaheed ta ajiye masa, hada ido suka yi yace "I said I am okay baxan ci ba" tace "Kaci ko kadan ne pls" Daga haka ta koma ta xauna, a hankali Imaan ta xamo kasa ta fara cin kazar, sai kallonta Mujaheed yake ta gefen ido, Maimoon ta dau tsoka daya daga kan kujerar tana ci a kunyace, Hajiya tace "To ya aikin doctor, Hajiya Rukayya tace min ka dawo Kaduna da aiki gaba daya yanxu koh?" Yace "Ehh" tace "To da kyau, Allah yayi albarka" yace "Ameen" idonsa na kan wayarsa amma da ya dago sai yaga kallonsa Safeenah take, Hajiya ta mike tace "Toh bari in d'an shiga ciki...." Mikewa yyi da sauri yace "Wucewa xa mu yi ai, xan je gun aiki" tace "Da wuri wuri haka, ka dai ki shan ko ruwa ne kuma ban ji ddi ba" yace "Am sorry bana jin cin komai ne yanxu" Tace "Toh ai sai ka jira kanninka su gama tukun na ko?" Yace "Bana son in makara xuwa gun aiki ne Hajiya" tace "Toh shikenan, bari a masu take away da shi" Imaan tace "Toh" wani kallo Mujaheed ya dinga mata, Hajiya ta kwalo ma mai aiki kira ta sanar da ita tayi masu takeaway din kajin, Imaan ta mike tace "Ina xan wanke hannu" Safeenah ta nuna mata hanyar dinning ko kitchen, tare suka tafi da Maimoon suka wanke hannu suka dawo, Hajiya ta basu dubu biyar Maimoon ta amsa da kyar, tuni Mujaheed ya fice gidan suka bi bayansa, Hajiya ta kalli Safeenah tace "Baxa ki raka su ba" bin bayan su tayi ita ma. Mujaheed har ya shiga mota sai ga ta tare da su Maimoon, tana kallonsa tace "I don't even know ur name" ba tare da ya kalleta ba yace "I am Mujaheed" tace "That's nyc, I am Safeenah" kai kawai ya gyada mata, Tace "Toh sai yaushe?" Yace "Watarana" yar siririyar dariya tayi tace "Do you mind sharing your digit with me pls?" Yace "Ohk" mika masa wayar hannunta tayi ya amsa ya sa mata lambarsa da bai fiye amfani da ba ya mika mata, tace "Thank you" yace "You are welcm" Daga haka ya tada motarsa ya wuce, haka ta bi motar da kallo har ya fita layin, da sauri ta koma ciki tana kallon uwarta tace "Wllh Mum naji ina son sa sosai" Uwar tace "Haba, to ai shine wanda na maki magana a kai kwanaki kika ce ke ba ruwan ki da hade hade in rabu da ke, uwarsa ce dama ta kawo shawarar ba ni ba tunda nasan kina da samari iri iri" ta marairace tace "Mum ai ban san haka yake ba, ni wllh mum ina son sa har raina" Hajiya tace "To ai shikenan, bari anjima sai in kira mahaifiyar tasa dama kwanaki duk ta dameni da kira a kan hakan bana daukan kiranta" Safeenah ta sauke ajiyar xuciya ta xauna tace "kaiii... Ya hadu wllh, his beards are damn cute, his lips so sexy with those catlike eye, gashi dogooo, I guess he have got six packs daga ganinsa yana workout, dama kuma ni bana son namiji fari pau, wllh Mum gayen ya hadu sosai, kuma naga sai wani basarwa yake yana shan kamshi, to ai irinsu nake so" Tun da Imaan taga irin kallon da Mujaheed ke mata bayan sun dau hanya ta kagu su isa gida ta fice daga motarsa tayi ta kanta, gashi dama so take suna komawa gida ta dau Atm card ta tafi supermarket siyo ma Sadeeq abinda ta masa alkawari jiya, a kofar gida Mujaheed yayi parking tana jin ya bude lock din motar ta bude ta fita da sauri, fitowa yayi shi ma bai kai ga bin ta ba tayi tuntunbe bakin gate sai ga ta a kasa, d'agata yyi ta fashe da wani matsanancin kuka tana cewa "Wayyo yaya kafana ya gurde wllh" maidata gun motar yayi fuska daure ya daga kanta yace "Waye kika fita wajensa shekaranjiya da daddare" k'in cewa komai tayi sai kukan da take tana kiran daddy a tsorace, ya wani hade rai cikin tsawa yace "Ba tambayar ki nake ba?" Still taki cewa komai xuciyar ta Sai bugawa yake, murda kunnenta yyi da karfi yace "Are you daft" ta kara rushewa da kuka tace "Don Allah kayi hakuri" yace "Waye shi" cikin kuka tace "Nima ban san shi ba yaya" Ji yake kamar ya sauke mata mari ya dinga mata wani kallo xuciyarsa na tafarfasa, he is just trying hard to control his temper, strictly yace "Toh daga yau Imaan, I mean daga yau.... na sake ganin ki da wani a tsaye wllh sai na kusa sumar dake a gidan nan I promise you that, ba ciwon jiki ko Asthma ba, idan ma jini ke xuba ko ina na jikin ki wllh sai nayi abinda na maki alkawari, ke har guda nawa kike xaki ke tsayawa da namiji jikin mota? How old are you??" Kuka kawai take tana kallonsa duk jikinta na rawa don ta dade bata gansa cikin yanayin nan ba, ya mata tsawa yace "Baxa ki bani amsa ba sai na gaura maki mari?" Cikin rawar murya tace "Ba na kusa 18 ba...." Rankwashi ya kai mata ta dafa wajen tana kiran inna a rikice, yace "In sake ganin ki da wani a waje, sai kin raina kanki wllh" daga haka ya saketa ya rufe motarsa, ta wuce ciki da sauri bata xame ko ina ba sai part din inna, xubewa tayi kan kujera tana rusa kuka, Inna ta fito daki da gudu tace "Na shiga uku me ya same ku a hanya, ko hatsari ku ka yi??" Imaan ta mike xaune cikin kuka tace "Yaya ne ya rankwashe ni kuma ya ja min kunne ni ban masa komai ba innaa" Inna ta xauna kan kujera tayi tagumi a hankali tace "Naga abinda ya isheni bai ishi Allah ba, Wannan yaro dai ya isheni a gidan nan wllh, innalillahi wa inna ilaihi raji'un, A kan wani dalilin kuma ya cuce ki, me kika masa?" Xata yi magana sai ga shi ya shigo, kin cewa komai tayi sai shessheka take hawaye na bin kuncinta, inna tayi mitsi mitsi da ido tace "Mujaheed kana manta cewar akwai hisabi koh, kana mance akwai lahira koh, ni ina jiye maka kada wataran ka
Chapter 68 · 0% Book details