← Book details Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 246 OF 300

Sashe 246

Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

dai ni ce, banxa kawai jahila mahaukaciya..." Safeenah da ta yo waje da ido jikinta na rawa tace "Ni kike xagi???" Imaan ta sakko da kafafuwanta daga saman gadon dai dai shigowar Mujaheed dakin, ta mike tana kallonta tace "An xage ki din kiyi abinda xa ki yi, karya nake ke ba jahila bace? Ko kin ta6a leka islamiyya??" Kallonsu Mujaheed ya tsaya yi da mamaki, Safeenah na kallonsa ta fashe da matsanancin kuka tace "Kana ji ko dear, ni wai take ce ma jahila mahaukaciya daga na shigo na gaisheta nace ta sakko mu yi breakfast, meye laifina a nan Mujaheed don na shigo nace ta sakko mu karya..." Kuka take sosai tana kallonsa, Wani dogon tsaki Imaan ta ja tace "Makaryaciyar banxa kawai" daga haka ta nufi bathroom kamar xata tashi sama ta shige tayi banging kofar da karfi, Mujaheed da ya bi ta da kallo baki bude ya mayar da dubansa kan Safeenah dake kuka sosai, karasawa yyi kusa da ita a hankali ya jawota jikinsa murya can kasa yace "I am happy da baki kulata ba, kinga yarinya ce, she still don't know what she is doing, but I will teach her discipline" daga haka ya ja ta suka fita dakin tana shessheka.... Abba ne tsaye parlon Inna tare da Mama Hadiza da ta rungume hannu, a fusace Inna tace "In har baxan tafi da kayan sawa ba to wllh sai dai kowa ya fasa xuwan a hakura kawai, ya xa ayi in tafi waje me nisa har Zaria ban je da kaya ko kala uku ba, Ni fa ba kwana nace xan je in yi kamar gantalalliya mara mafadi ba, amma ai yana da kyau duk matafiyi ya dinga yawo da kaya sbda bacin rana, kaji min dai sai kace kun fi ni sanin abinda nake, wllh ban taba tafiya bbu jakar kaya ba ko da kuwa awa daya xan je inyi a waje, sabida fatara sai in tafi da xanin jikina kadai ina yawo a garin zaria kamar almajira..." Abba yace "Toh inna tafiyar da xa aje a dawo a ranan ina amfanin tafiya da kaya? Me xa kiyi da kayan, Da driver fa xa ku je ku dawo" Inna tace "Yau naga jaraba, Ina ruwanka da rayuwata ne Ahmadu, Kai xaka yi tafiya ko ni? Yanxu idan na bi hanya Ina ta kwarara masu amai a mota kayan Imaan ko na Safara'u xan je in canxa a gidan??" Mama Hadiza tace "Zaria fa xa mu je ba Lagos ba Inna" A mugun fusace inna tace "Ko maraban jos xa mu ba ruwan ki kiyi ta kanki, bbu shegen da ya isa sa ni in fita gidan nan da xanin jikina kadai kamar a kaina talauci ya kare..." Daddy ne ya shigo parlon da sallama shima yyi shirin komawa Abuja ranan, yace "Har yanxu ba ku fito ba Inna..." Inna tace "Ina fa xan fito Bukar, ai tafiyar nan ina jin babu shi don ni dai baxan bi hanya bbu kaya ba gaskiya, Kai ko da ban yi amai ba a hanya to ni nasan kafin mu isa Zaria xan jike shataf da gumi, to uwata ce min tayi je ki kya gani da xan xauna da kaya ina warin xufa Bukar???" Daddy yace "Haba inna sai kace warce xata sokoto ko gombe, nan nan Zaria fa xa ku, ku dawo anjima, idan ba xama kike son xuwa yi a gidan ba ina amfanin tafiya da kaya?? Sai dai in xauna masu kike son yi kawai, amma sau nawa kike xuwa kano kice ke ko jaka baxa ki dauka ba? Gashi har rana yyi ba ku kama hanya ba, hakan is not good" shiru Inna tayi bata ce komai ba sai yan idanuwa, Daddy ya juya ya fita parlon, Mama Hadiza ta dau warmer dake cike da dambun nama da Inna tayi ma Imaan ta fita parlon tace "Muna jiran ki a mota" Abba na kallon Inna da ta sunkuyar da kai a hankali yace "Ae sati uku xa su yi xarian sai su dawo kaduna, idan ya so sai ki..." A fusace inna tace "Rufe min baki malam, Ina ruwana da ko kwana nawa xa su yi a Zaria? Ko nace maku xuwa xan yi in xauna masu kamar shashasha tsofe tsofe da ni, me Mujaheed da Imaan xa su bani wanda Allah bai ban ba? Yaran da aka ma auren dole auren jaraba wa yasan halin da suke ciki ma yanxu, wllh In don ta kai da Bukar ne ni baxan ma je ba don baku da kirki barin wannan mutumi Bukar, da 'yar sa ce kadai a gidan wllh na ma fasa xuwan gaba daya, to amma ni yanxu gun Mujaheed kawai xanje ba gunta ba wllh, bbu ruwana don ubanta ba ma son xuwa in je gidan yake ba, ubanta ba shi da kirki" tana fadin haka ta mike ta fice daga parlon ba tare da ta dau jakar kayanta kusan kala shidda da ta hada ba a Ghana must go.
Chapter 246 · 0% Book details