Sashe 70
Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Juyawa Mujaheed yyi ya fice daga parlon, Imaan ta kyabe baki tana share idonta tace "Shi fa bai san ko waye ba xai wani dinga ce wa saurayina, ni dai wllh inna ku ce masa ba ruwansa da ni a gidan nan" inna tace "Atoh dama meye hadin ki da shi, kawai ni dai nasan ubansa wan ubanki ne kuma duk ni na haifesu, to bayan wannan bbu abinda ya hada ki da Mujaheed ba dangin iya balle na baba, ke dai kawai ki rabu da shi ya ji da wawancin sa kiyi ta kan ki, banda fitina ma ina ruwansa da lamarin rayuwarki, idan ma saurayin kika yi baki isa ba ne, ko idan kin rasa mijin aure astaghfirullah shi xai aure ki ne?? kar ki sake saurarensa duk saurayi ya kira ki shirya ki fesa turare ki tafi, wa xai xauna biye ta Ahmadu da Bukar ga d'an su ma ya dauko hanya, bokon jaraba kawai ni wllh kina gama sakandari aurar da ke xance ayi mijin yaji da lalurorin ki d'a na ya huta haka shi ma" imaan ta mata wani kallo ta mike tana goge guntun hawayenta ta fice a parlon. Da yammacin ranan daddy ya gama shirin komawa Abuja ya tafi yi ma Inna sallama, ta gama goge gogen da ta ke ta dawo ta xauna tace "Tafiyar na nan yau din kenan" yace "Ehh, jirgi xan bi kada jirgin ya tashi ba ni" inna tace "Toh Allah ya tsare, amma xaka tafi kuma ya xancen da ku ka min kai da Ahmadu jiya?" Daddy yace "Na me fa?" Inna tace "Tafiyar yaran nan su je gaida Hansatu mana" Daddy yace "Ehh Barrister yace xuwa satin da xa a shiga sai su tafi" inna tace "Ehh gwara su je, duk da dai uwarta axxaluma ce amma ina mata fatan Allah ya ji kanta na kuma yafe mata, amma gaskiya shari'ar mu sai a lahira, don ta cutar da ni...." Daddy yace "Haba inna, bayan kuma kin ce kin yafe" a fusace inna tace "Toh ai Allah ba axxalumin bawansa bane, don na yafe ai a duniya nake nufi ba a can ba, kai baka san komai ba wllh, kaga irin abinda uwarta tayi min ne, kishi dama hauka ne, ni dai kawai albarkacin marigayin uban ku yasa nake barin ayi xumunci da 'ya yan da ta mutu ta bari ma, kuma duk yaran ba xuwa gaida ni suke ba" Daddy yace "Ke fa kika ce kin yafe xuwan, kowa ya xauna inda yake" Inna tace "Toh idan bance haka ba ya kake so ince, kai so kake su xo su sa ma kai da d'an uwanka ido, yanxu da ake nisa nisa ba ya fi ba, babu wanda yasan halin da wani ke ciki, sai ku dinga wata magana kai da Ahmadu don ba ku aka cuta ba, yanxu kishiyoyin da bani da hakkinsu ba gashi duk sun mace sun bar 'ya ya duk a gantale ba, to me xa su xo su min bayan ga nawa 'ya yan... Ku uku wllh kun isheni xaman duniya ita ma Hadiza tace ta kusa dawowa kasar nan gaba daya, to me xai dameni, a hada masu goma ta arxiki aje dai a gaishesu, har shi wancan katon Balan dake Abuja su karasa su gaida shi, ba komai Allah ya ba mu lada su kuma aniyarsu ta bi su" Daddy yace "Bari in je inna, Mujaheed xai kawo maki sako anjima" tace "Toh Allah ya tsare, yayi maka albarka, ya kare ka duk inda xaka shiga" yace "Toh Ameen nagode" daga haka ya fita parlon, part dinsa ya tafi suka yi sallama da Ammi yace "Gobe dai Imaan ta tafi islamiyya, xuwa Wednesday nasan xa su yi tafiyar, before than Dr dinta xai kawo mata drugs dinta coz ya dawo" Ammi tace "Toh Allah ya kiyaye hanya ya tsare, ko in taso ta?" Yace "A'a bar ta" daga haka ya nufi kofa ya fita, Yusuf ne ya kai sa airport. Mujaheed ya daga kai yana kallon Abbansa bayan ya gama maganar da yake, a hankali yace "Abba kaga ba a dde da transferring dina nan ba da har xan fara daukan leave gun aiki...." Abba yace "You are just lookin for excuses, na lura gaba daya baka son tafiyar Muhd" ya sunkuyar da kai yace "A'a ba haka bane Abba, kawai naga...." Abba ya dakatar da shi yace "Toh xan ma boss din naka magana" da sauri ya dago yana kallon Abba amma bai ce komai ba, Abba yace "Beside idan ku ka tafi Wednesday xuwa Friday ai kun dawo, nan nan sulejah dai" Mujaheed bai ce komai ba still, jin Abba ma yyi shiru yace "Toh Abba kasan yanayin jikin Imaan, har da ita xa mu je?" Abba yace "Toh ba ga ka ba, you just go with first aid box" Mujaheed yace "Toh shikenan" Abba yace "And ina son dama muyi wata magana Mujaheed" Mujaheed yace "Ina ji Abba" Abba yace "Its high time you think of settling down with a family Muhd, naga baka san shiru ba kai, idan na kyale ka a haka xa ayi ta tafiya, duk abokanka sun yi aure with kids, not even kid, to kai me kake jira son?" Ya shafa kai a hankali yace "Abba warce nake nema tana karatu ne, amma ta kusa karewa nan da 'yan watanni in sha Allah" Abba yace "Yar ina ce?" Ya d'an yi murmushi yace "Nan Kaduna, a hayi iyayenta suke amma tana gun yayarta a Unguwar sanusi" Abba yace "Toh maa sha Allah, hakan yayi kyau sosai, but I think it's better a fara magana tun yanxu...." Muryar Umma suka ji tace "Babu maganar da xa a fara Alhaji" duk suka daga kai suna kallonta ta karaso cikin parlon, bacin rai karara fuskarta tace "Yanxu ni xaka munafurta Mujaheed, haka muka yi da kai, to kasani wllh idan ina numfashi a doron kasa baxa ka auri yarinyar nan bar, idan kuma kana son ganin ba dai dai ba a lamarin ka kaci gaba da alaka da matsiyaciyar yarinyar, ina zamana ka dauko mun talauci a matsayin surka, to wllh kayi kadan gwara kayi ta xama ba auren ya fi, ga yarinya mai hankali mai natsuwa Safeenah yar wajen Hajiyan Marafa can na nema maka yarinyar kuma tayi mugun na'am da kai xaka toxarta ni ka maidani karamar mutum a idonsu???" Abba yace "Abinda nake son in fara fahimta a nan shine, la6e kike min Rukayya?" Umma ta tabe baki tace "Idan ma la6en nayi Allah ne yasan bani da hakkin kowa shi sa har ya bani ikon labewan in ji komai, Alhaji wato idan Kasan talauci to a kan yarinyar da iyayenta ya kare, can wani ghetto fa suke, to idan ba toxarta mu Mujaheed ke son yi a idon jama'a ba ina shi ina yarinyar nan, Kyan banxa kyan hofi, yo ina ma take da kyan ita ba wai fara ba, gaskiya kayi min iyaka da Mujaheed kada in nuna masa 6acin raina a gidan nan, sam baxai ji da dadi ba, shi baya koyi da d'an uwansa Yusuf, dubi fa yarinyar da yake nema yar attajiri gashi har magana yayi nisa, sai ni ce Mujaheed xai cuta ya kwaso min yar talakawa" Abba ya girgixa kai yace "Halan ke ke raba talauci da arxikin Rukayya?" Umma tace "Ba ruwana da wannan xancen ni dai gaskiya idan Mujaheed bai yi hankali da ni ba xai sha mamaki, kuma in dai baxai bi ni sau da kafa ba xai dinga ganin ba dai dai ba a lamarin sa ni dai ba ruwana" tana kai wa nan ta fice fuuu, Abba ya girgixa kai yace "Look son, ba ruwanka da wannan uwar taka, ba isasshen hankali gareta ba am giving u my words, ka ci gaba da neman yarinyar, Allah ya shige mana gaba" A hankali Mujaheed yace "Ameen" Abba yace "You can go" ya mike yace "Nagode Abba" daga haka ya fita parlon. A hankali Ammi ta bude kofar dakin Imaan tana kallon ciki jin dariyar da take cikin duvet, da sauri Imaan ta katse wayar ta tura karkashin pillow jin kamar an bude kofa, Ammi ta kunna wutan dakin tace "Da wa kike waya Imaan?" Bude duvet din tayi kamar mai bacci ta mike xaune tace "Na'am" Ammi ta mata wani kallo tace "Baxa ki amsa min tambayata ba, da wa kike waya nace?" Shiru tayi tana kallon Ammi kamar xata yi kuka, Ammi ta karasa kusa da gadon tace "Bani wayar" ba musu ta ciro wayar ta mika ma Ammi, Ammi na kallon call log tace "Number waye wannan din" murya can kasa Imaan tace "Abokin ya Muhsin ne" Ammi tace "Me ya hada ki da abokin Muhsin, a ina kika san sa?" Tace "Ammi yana xuwa gidan gwaggwo kuma kanwarsa classmate dita ce, yanxu ma kawai tambaya ya kira ni yake min ba wani abu ba" Ammi ta dinga mata wani kallo, ta sunkuyar da kai, Ammi tace "Ke dai kin iya munafurci" kamar xata yi kuka tace "Ammi ni wllh dai ya kira ni ne amma ba komai fa" Ammi tace "Toh yayi kyau, ki bude kunne sosai ki saurareni, kada ma ki nuna nasan kina waya da wani a gidan nan don ba ruwana, duk ranan da Daddyn ki ya kama ki dama ki tanadi abun gaya masa don't involve me in this" tana kai wa nan ta fice dakin. Washegari da rana Ammi na xaune parlor Imaan ta fito sanye da Hijab sai karamar jakarta da ta rataye, Ammi na kallonta tace "Ina xa ki?" A hankali tace "Ammi xan je in siyo cream a supermarket" Ammi na kallonta da mamaki tace "Yaushe na siyo maki da har ya kare Imaan?" Shiru tayi tana kallon Ammi kamar munafuka, Ammi tace "Shan cream din kika fara?" Tace "Ammi shafawa kawai nake yi fa" Ammi ta tabe baki tace "Toh ni kam bani da kudin cream yanxu" tace "Ai ina da kudi a account dina" Ammi tace "Toh Hajiya mai kudi, a dawo lafiya" yar dariya tayi ta sa flat shoe dinta ta fita parlon, kamar mai tausayin kasa ta taka har bakin main road inda xata samu adai daita, jin wayarta na vibrate a jaka ta