← Book details Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 286 OF 300

Sashe 286

Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun da Imaan ta koma daki ta kwanta ta ji ta very restless, gaba daya ta rasa takamaiman abinda ke damunta, ta dinga juye juye kan gado, can ta mike xaune, a hankali ta xamo kasa daga kan gadon ta durkusa ta kife kanta da gadon, ta fi minti ashirin a haka aka bude kofar dakin Mujaheed ya shigo rike da goran ruwa da drugs dinta, kallo daya yyi mata ya dauke kai ya karaso kusa da ita yace "Yau kuma haka xa ki kwanta" k'in cewa komai tayi kuma bata dago ba ya dagota ya juyo da ita yana kallonta ganin hawaye idonta da damuwa yace "Subhanallah me ya faru?" Bata ce komai ba ya kwantar da ita saman gadon yace "Ko kafarki ke ciwo?" ita dai bata ce komai ba ya mike ya dauko man shafanta na kafa ya kashe wutan dakin ya bar mara haske ya fara shafa mata, lumshe ido tayi, hakan yasa yyi murmushi yana kallonta, Bayan wani lkci ya kai bakinsa fuskarta yace "Bayan ma yana maki ciwo?" Bata bude masa ido ba ta gyada masa kai, juyar da ita yyi ya sauke wear dinta kasa ya fara shafa mata lotion din a bayanta, ya jima yana massaging back dinta gently sannan ya juyo ta yana kallonta yace "Yayi sauki koh?" Ta bude idonta a hankali tana kallonsa, ya sakar mata murmushi ya ja dogon hancinta yace "Sleep tight dear, sai da safe" xai mike kawai ya ji ta jawosa sai kuma ta fashe da kuka, ya wara ido yace "what happened?" Ta mike xaune ta rungumesa tana shessheka, ya lumshe idonsa murya can kasa yace "Ki gaya min menene?" Shiru bata ce komai ba yana jin yanda take sauke numfashi a hankali, kamshin gashinta duk ya cika sa, ya janyeta jikinsa yace "Xan kwanta, I have work tomorrow" kin sake sa tayi tana kara shigewa jikinsa, and that really turned him on duk da yanda ya so ya share even for sometimes, lkci daya ya fara bi da ita gently kuma romantically, ko kadan bai yi mamakin martanin da ta dinga mayar masa ba, ta basa hadin kai 100% ba raki ba komai, daga karshe ma shi ya rikice mata, and that nyt will forever remain in his memory... Can karfe biyu Imaan ta farka ta dalilin kanta da ke ciwo sosai, ta janye daga kusa da shi a hankali ta mike xaune tana kallonsa tana rufe kanta da duvet, lkci daya ta ji kunya ba na wasa ba ya rufeta, maganganunsa suka dinga dawo mata da daddaya da daddaya, kallonsa kawai take ko kiftawa bbu, kawai gani tayi ya jawota ya kankameta ya kai bakinsa kunnenta yace "Why are you staring at me wife" rufe idonta tayi da sauri ta boye fuska jikinsa kamar yana ganinta, yyi murmushi yana shafa gashinta, a haka bacci ya kara dauketa. Tun da Mujaheed ya dawo masallaci yake bacci a bedroom dinsa, Imaan ta fito kitchen bayan ta juye ruwan xafi flask, tana kallon agogo ganin bakwai ya wuce ta wuce sama, ta fi minti biyar tsaye bakin kofar parlonsa sannan ta bude a hankali ta shiga ta wuce bedroom dinsa, bata gansa dakin ba amma jin saukan ruwa ta gane yana wanka, ta nufi gaban madubi ganin envelope ta bude envelope din ta leka ciki sannan ta ciro takardan, warwarewa tayi tana duba content din, Takardar scan ne dauke da sunan Safeenah, sosai gaban Imaan ya fadi ta dinga kallon takardan dai dai nan Mujaheed ya fito bathroom, ta madubi ta kallesa ta sunkuyar da kai da sauri, ya karasa bayanta ya tsaya ya kwanto ta jikinsa a hankali yace "Wife..." Bata dago kanta ba ya juyo da ita yana kallonta yace "Ko xa ki rakani office yau?" Ta girgixa kai kawai, ya dau takardan ta linke ya mayar cikin envelope din yace "Toh fito min da kayan da xan sa" Shiru tayi bata ce komai ba ya dago kanta yace "Kin ji?" Tace "Ai ban san gun kayan ba" nuna mata yyi ta tafi gun press din ta bude, a gabanta ya saka kayan bai bari ta fita ba kamar yanda tayi niyya, yana saka safa kafarsa yace "Kin ga yau kin sa na makara" Ta d'an turo baki tace "Ni kuma?" Yyi mata slight kiss a lips yana rike da hannunta yace "Ehh mana lil sis..." Sunkuyar da kanta tayi ya mike ya dagota yace "What are you taking for breakfast?" Tace "Anjima xan dafa indomie" yace "Ohk, mu je ki rakani gun mota xan dawo in sha Allah da karfe 12 in ga wife dita sai in koma karfe daya..." tace "Breakfast fa?" Yace "Xan yi a office dear" ta turo baki tace "Na fa dafa maka ruwan xafi kuma akwai bread" ya wara ido yace "Da gaske?" Ta gyada masa kai yace "Toh mu je inyi breakfast din" suna isa dinning tace "Or should I fry you egg?" Yace "Xa ki iya?" Tace "Uhm" a tare suka tafi kitchen din yana tsaye bayanta ta gama soya eggs din ta kashe gas, ya juyo da ita ya daura forehead dinsa kan nata a hankali yace "Plss ki dinga min haka Imaan, wllh I want to be with you till eternity, baki San yanda nake ji dake ba ko kanwata? Ki daina bani wahala haka, one day you will know what I mean" Ko kadan abinda ya fada bai burge Imaan ba, Wai he just want to be with her, shi dai kawai so yake ya kasance da ita and nothing more, ta sauke idonta da ya kawo hawaye ya rungumeta ta tayi lamo jikinsa tana jin kamshinsa, lumshe ido yyi yana jin wani irin sonta da sha'awarta na daban, wanda dai dai da second daya bai ta6a jin sha'awar Safeenah ba sai in ita ta kawo kanta, tare suka yi breakfast din duk da bata wani ci da yawa ba ta rakasa har bakin mota kamar yanda ya bukata sannan ta koma ciki bayan ta kulle gidan, dakinta ta wuce ta kwanta lkci daya baccin da bai isheta ba ya dauketa. Karfe sha daya ta farka, babu 6ata lkci tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga na material, ta feshe jikinta da turare tana gyara gadonta taji an bude kofar dakin, a tsorace ta dago ganinsa ta turo baki ta xauna kamar xata yi kuka tace "Yaya ka bani tsoro" ya karaso cikin dakin yana murmushi ya cire necktie dinsa ya nufeta yace "Tsoro kuma sai kace ba takwarar Inna ba baby?" Turo baki tayi ya xauna kusa da ita yyi mata side hug yana murmushi yana kallonta murya can kasa yace "Kin yi kyau sosai wife, did you know I have been thinking about yesterday throughout yau a office" Bata yarda ta kallesa ba kuma bata ce komai ba, ya kai bakinsa kunnenta yace "Gaya min wa ya koya maki in masa kyauta" boye fuskarta tayi shoulder dinsa cike da shagwaba tace "Ni bana so fa Yaya" kwantar da ita yyi saman gadon ya kwanta shi ma yace "Ae kuwa xa ki so ynxun nan" sai kusan karfe uku Mujaheed ya bar gidan ya koma office Imaan na bacci bayan ya ajiye mata lunch a daki. Kiran la'asar ya farkar da ita ta bude ido a hnkli ta kalli gefenta ta mike xaune ganin bata gansa ba, farin takardan da ta gani gefen pillow ta dauka ta warware taga rubutunsa kamar haka "God bless you dear, sai na dawo anjima, I care..." Turo baki tayi ta ajiye takardan tana jin bayanta na d'an mata ciwo ta sauka daga kan gadon ta wuce bathroom. Da Mujaheed ya tashi dawowa around 5 na yamma da waya irin wanda Sadeeq ya ta6a siya ma Maryam ya shigo gidan, tana kitchen ta gama blending kayan miya ta ji shigowarsa gidan, leka parlor tayi suka yi ido hudu ya buda mata hannu yana murmushi, ta make masa kafada ta, a hankali yace "Toh shikenan" daga haka ya wuce sama ta bi sa da ido, ta gama fiddo nama a deep freezer sannan ta fito ta wuce sama, a hankali ta bude kofar parlonsa yanda baxai ji ba ta shiga ta karasa bedroom dinsa don a bude kofar yake, button din rigarsa ta samesa yana cirewa ta karasa dakin ta kwanta bayansa ta lumshe ido murya can kasa tace "Wlcm" ya juya da ita drawing her closer to him, girkin da bata karasa a lkcn ba kenan ta biye ma Mujaheed. Tana xaune saman darduma tana kallonsa bayan sun idar da sllhn Magrib, ya mike yace "Let go out and get something to eat" Tace "Ae yanxu xan yi girkin" yace "Noo I don't want to stress you anymore, mu tafi mu siya a eatry" Bata ce komai ba ya kama hannunta ta mike ya dauke darduman ya ajiye, ledan da ya shigo da shi daxu ya dauko mata ya kama hannunta ya mika mata yana kallonta, ta dinga kallon ledan sannan ta bude, lkci daya ta wara ido ta rungumesa gam tace "Waow nagode Yayana, thank you very much" ya lumshe ido yace "You are welcm sweet" ta turo baki ta 6ata rai tace "Ni dai ka daina ce min sweet bana so" yace "Ohh daxu da na gaya maki kin xata wasa nake ba sweet xan dinga kiran ki ba" ta make kafada tace "Ni bana so" ya dauketa Kamar yar baby yace "Toh sai ince maki Zuma" dariya tayi ta rikesa gam tace "Ni dai bana so" yyi kissing hancinta ya ajiyeta yace "Toh mu je idan mun dawo sai ki bude wayar" daga haka ya dau makullin motarsa ya kamata suka fita dakin. Lafiyayyen abinci ya siya masu da gasasshen kaji, suna dawowa wayarsa dake ajiye kusa da shi a mota ya fara ring, a tare suka kalli screen din, a hankali Imaan ta dauke kai ganin sunan Safeenah a screen din. Bayan few seconds yyi Picking call din ya sa handsfree ya ajiye yayi sallama, maimakon ta amsa murya can kasa tace "Dr wllh kaza nake son ci, tun safe nake ta amai bani da appetite na komai, yanxu kuma naji ina son cin kaza pls idan ban takura ka ba" Mujaheed yace "Ohk" tace "Kazar gida nake so fa kuma a
Chapter 286 · 0% Book details