← Book details Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 300

Sashe 13

Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ba isa a maki fada ba shine kika kwana kuka ido ya kumbura koh?" Ta fashe da kuka tace "Ni Ammi don Allah kar ki sake ce min in kai mata abinci kullum sai tayi ta ma mutum sharri alhalin ba abinda nayi mata" Ammi tace "Ko ban baki abinci kin kai ba ma da kanki naga kike kwasan kafafuwanki kije can din ko da kuwa koranki tayi" Imaan ta hade rai tace "Yesterday was the last day da xan je part dinta, har abada baxan sake xuwa ba" Ammi tace "Toh bari dai ya ji ki gashi can ya fito, ni ba ruwana" shiru Imaan tayi tana juya shayin da Ammi ta hada mata, Daddy dake tsaye parlon yace "Madam me yasa ba a kai ma Inna breakfast ne wai?" Ammi tace "Breakfast kuma?" Yace "Ehh ai ya kama ta ne" tace "A'a don Allah yallabai kar ka hada ni da ita, kullum sai Abba ya tura mata bread, tana da kayan shayi kuma tana da heater ta iya amfani da shi, meye breakfast din dama idan ba shayi da bread ba sai kwai wani lkcn, lunch da kanta tace bata so a daina kai mata wai jagwalgwalon yara ne" Tuni Daddy ya xauna ya sa news channel, Ammi ta shiga kitchen ta ci gaba da abinda take, Imaan ta gama breakfast din ta mike ta iso cikin parlor ta durkusa ta gaida Daddyn nata, sau daya ya kalleta ya amsa ya ci gaba da kallonsa, ta mike ta tafi kitchen ta amshi kudin makarantar ta gun Ammi ta fito ta dau jakarta bayan ta sa takalmi da safa tayi ma daddy sallama ba tare da ta kallesa ba ta fice daga parlon, kiranta daddy yyi ta juyo ta dawo ta sunkuyar da kanta tace "Ga ni" room freshener har biyu ya nuna mata dake ajiye yace "Dauka ki kai ma Inna kafin ku wuce" shiru tayi tana kallonsa kamar xata yi kuka, bata dai ce komai ba ta durkusa ta dauka sannan ta fita xuwa part din inna, Inna na ta goge goge bayan ta gama share ko ina fesss, banda kamshin turaren wuta babu abinda ke tashi a parlon, imaan bata kalleta ba ta ajiye abun hannunta fuska daure tace "Ina kwana" xata fita inna tace "Me ya sami idonki ni Asabe? An umaki wani abun ne" Imaan da har ta kai kofa ta juyo lkci daya ta fara kuka tace "Kawai sai kije kice ma daddy ina maki rashin kunya yaushe rabon da in xo nan...." Tana fadin haka ta fashe da matsanancin kuka, Inna da ta saki baki tace "Shine ya maki me?" Cikin kuka tace "Fada ya dinga min mana yace zai yi magani na" Inna ta dau dankwalinta ta fita parlon imaan ta bi ta da kallo tana share idonta, Ko sallama babu inna ta bude kofar parlon, daga daddy har Ammi suka daga kai suna kallonta, tace "Bukar dama yaro ba lallabasa ake yi ba a rayuwar nan, daga mun yi magana tsakanina da kai sai ka taho ka far ma yarinya da bala'i, to ae gwara ita sau dubu a kan sauran, Imaan bar ta da son jikinta amma wllh wllh bata da matsala, haka kawai ka ja mata wani cutan dama gata mai cuta iri iri kamar ta kashe d'an mutum, yanxu da kasa ta kwana tana kuka idan wani abun ya sameta me xa ka gaya ma Allah, kai dai wllh ka cika bala'i, ba haka yayanka Ahmadu yake ba, ba ruwansa da irin wannan hali, to wai ma me ta min da xafi haka da xaka sa ta kuka haka, ga abun duka can Mujaheed me nuna ni da yatsa, mai ce min Hajiya, ni tunda nake wllh xan iya kirga sau nawa Imaan ta mayar min magana shima kuma duk laifina ne....." Ammi dai tuni ta shige kitchen, Daddy kuma ya kasa cewa komai, Inna ta juya ta nufi kofa tana cewa "Wannan dai ba yi bane, kamar ba kai ka haifeta, yar gata daga ita sai ita amma kuma ka takurata, da wanne xata ji da rashin karo mata kanni da ba ayi ba har yau ko kuma da fitinar mahaifinta, kuma ka tashi ka kawo min turaren bature da ko kamshi babu wai in fesa a daki, to uwata bata ce min je ki kya gani ba turaren wuta tsadadde mai kamshi nake nufi, sai ka ba matarka mai kumewa a daki kamar matar liman ta fita kasuwa ta siyo min" daga haka ta fice ta kulle masu kofa. Dama imaan direct gun mota ta nufa bata yarda ta ma bi ta part dinsu ba. Yusuf ne ya ajiye su islamiyyar, karfe sha biyu Anty ta dauko su, A hankali Imaan ta bude kofar parlonsu tana lekan ciki, babu kowa hakan yasa ta shiga ta rufe kofar ta nufi bedroom dinta da sauri, tana kokarin cire Uniform dinta Ammi ta bude kofar, Imaan ta gaisheta kanta a kasa, Ammi tace "Amso min card waje kafin ki cire uniform din" Imaan ta amsa tana kallonta tace "Ammi daddy fa?" Ammi tace "Yana daki" Imaan ta marairaice tace "Ni fa ban gaya ma inna ya min fada ba, kawai taga idona ne haka" Ammi tace "Wannan ya rage naku ke da shi, ni kiyi sauri ki amso min card din" imaan ta maida Hijab dinta ta fita, kiosk din is just a house from theirs, ta amso card din ta juyo ta shigo gida, Umma ta gani tsaye parking space alamar xata fita, Mujaheed ya iso wajen ya bude mata back seat, sannan ya shiga driver seat, Imaan na hada ido da Umma dama ta dauke kai tayi wucewarta, Mujaheed ya bi ta da kallo ta madubi, Umma ta shiga cikin motar tace "Wllh duk ranan da ka gaida uwar yarinyar nn ko da mistake a gidan nan ban yafe maka ba Mujaheed, duk kanninka ma na karanta masu haka nasan kuma sun dauka...." Yana kallonta ta madubi yace "Haba Umma kema kin san....." Ta karasa masa da sauri tace "Baxa ka iya ba ko? tunda ga ta kanwar Ahmad ko kanwata, Mara tunani kawai da bai san ciwon uwarsa ba, to mu xuba da kai wllh, ba dai makiyana su ne mutanen arxikin ka ba a gidan nan, ka ci gaba, a ta dalilin munafukar uwar yarinyar nan na bar gidan ubanka for good 5 years, ta hade kai da kishiyata suka yi ta kulla min makirci har ubanka ya sakeni, da yake akwai sauran xamana a gidan na dawo few years back na tarar baka da masoya da ya wuce makiyana, ka maida Aisha uwarka, ka nuna duk gidan nan baka da kanwa da ya wuce yarinyar Aisha, yarinyar da bata gaisheni a ynxu ko idona xai makale a nata saboda uwar ta hanata, da kyar da siddin goshi da rokan Allah na rabaka da su, ni da ba a kan idona na haifeka ba kuma ina haihuwar ka aka ajiye min kai a gefe na da wllh bbu abinda zai sa baxan ce canjen ka aka min a asibiti ba, sam baka san mutunci na ba, ace makiyana su ne masoyan ka Mujaheed? Anya kana son gamawa lfya kuwa?" Shi dai ya kasa cewa komai, ta gyada kai ta bude motar ta fice tana cewa "Ga ka ga su ai, daga ynxu ma ka tatttara yanaka yanaka ka koma bangaren nasu" a hankali yace "Umma I have avoid a lot of things a gidan nan kema kin sani, wllh ko kadan bani son abinda xai bata maki rai, don Allah kiyi hakuri...." Ko saurarensa bata yi ba ta fice daga compound din ya sauka ya bi bayanta da sauri. Washegari har Ammi ta gama hada breakfast ta fito daga kitchen imaan bata fito daki ba, ta kalli agogo ganin bakwai da quarter ta nufi dakin ta bude ta shiga, kwance ta ganta ta dukunkune cikin bargo, Ammi ta karasa da sauri ta cire bargon tace "Are you okay Imaan?" Ta bude ido kamar xata yi kuka, Ammi ta dinga kallonta don jikinta ya dau xafi sosai, a hankali tace "Ina ke maki ciwo kuma?" Kafafuwanta ta nuna mata da kai, hawaye cike idonta tace "Ammi duka jikina ciwo, jiya ban yi bacci ba" Ammi ta kamo hannunta cikin sanyin murya tace "Ba ki sha magani ba jiya da daddare ko daughter" ta nuna ma Ammi magungunanta a side drawer tace "Na sha Ammi" saketa Ammi tayi ta mike ta shiga bathroom ta hada mata ruwan wanka ta fito tace "Toh shiga kiyi wanka sai ki kara shan maganin" da taimakon Ammi ta sauka kan gadon, Ammi na rike da ita suka shiga bathroom, bayan ta wanke baki Ammi ta taimaketa tayi wanka ta fito, barin ta tayi ta sa kaya ta tafi hado mata shayi, Daddy na xaune parlor yana dube dube a laptop, ta tsaya bayan kujerar tace "Yallabai jikin imaan fa kar ya rikice mana ko xa aje asibiti tunda likitan ma baya nan" daddy ya mike yace "Bata jin dadi ne" Ammi tace "Nima yanxu na shiga ganin bata fito ba, her temperature is high tace bata yi bacci ba" daddy ya d'an yi shiru, Ammi tace "Kwanakin baya ciwon ya lafa sosai, as from some weeks ago yanxu duk sai ya tasar mata ga xaxxabi da ciwon kai kuma tana shan drugs dinta" Daddy yace "Toh ta shirya mu tafi asibiti" Ammi tace "Toh" komawa yayi ya xauna, ita kuma ta wuce dinning don hada mata shayi. Kwance ta sameta bayan ta sa abayar da ta fiddo mata, da kyar Imaan ta sha shayin, Ammi ta fesa mata turarrukan ta ta bata veil din abayar sannan suka fito parlor, kwanciya tayi kan kujera tana gaida daddy dake rike da makullin mota yana jiransu, ya amsa yace "Sannu mamana, tashi mu je to" mikewa tayi ya kama hannunta suka nufi kofa Ammi na masu Allah ya kiyaye hanya, A hanya daddy ya hadu da Abba ya taho daga part din Inna, gaisawa suka yi, Imaan ma ta gaishesa a hankali, Abba yace "Jikin ne ya tasar mata?" Daddy yace "Wllh kuwa, xa mu je asibiti ne yanxu" Abba yace "Subhanallah tana shan magunguna kuwa" Daddy yace "I think so" Abba yace
Chapter 13 · 0% Book details