← Book details Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 221 OF 300

Sashe 221

Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai kusan karfe goma da rabi Umma ta dawo gida daga gidan Mujaheed duk tayi wani wujiga wujiga da ita, tun magarib da ta fita ta je gidan nasa take ta xaune cikin compound wai ko xai dawo amma shiru har karfe goma da wani abu bbu shi bbu alamarsa hakan yasa ta baro gidan hankali tashe tana hawaye ga Hajiyan Marafa sai kiranta take a waya ba kakkautawa, daga karshe ma kashe wayar tayi gaba daya, direct part din Inna ta nufa tana share xufar fuskarta, kowa ya ganta yasan tana cikin tashin hankali ne ba na wasa ba, xaune ta samesu da Mama Hadiza, Mama Hansai da Ta Rasulu, sai Aunty, Umma ta rakube jikin kujera tana kokarin boye hawayen idonta kar su gani, ta gaishe su gaba daya, duk suka amsa banda Inna dake cin abinci, Umma tayi kasa da murya kamar ta kirki tace "Inna daga gidan Mujaheed nake yanxu, tun magariba nake gidan amma shiru shiru bai dawo ba ban san dalili ba, tsorona kada wannan hadin ya ja mana matsala mai karfi a xumuncin mu tunda Aisha kirikiri ta fito ta nuna bata so, ita ma Imaan din da kanta ba so take ba, shi kansa Mujaheed nasan tashin hankali ne yasa ya shiga duniya, kuma daxu naji ke da kanki kince sai an raba auren, to Mujaheed fa har ynxu bbu labarinsa wllh yanxu haka ma daga gidansa nake Inna...." cikin rawar murya ta kare maganar tana kallon Inna, Inna ta tura abincin gabanta ta kalli Ta Rasulu tace "Kin ji bala'i koh? Rukayya ni xa ki ma sharri kice nace a raba aure da raina a duniya ba wai na mutu ba, ni dai nasan daxu a parlon Ahmadu nace ba ayi shawara da ni ba na kuma nuna bacin rai na sosai, amma bayan wannan ban san komai ba, ban kuma ce komai ba, yo dama ai Mujaheed shine dai dai Imaan ganewa ne ba ayi ba da wuri, shi fa Sadeeq din nan dama ubansa ne mai kudin ba shi ba, kuma da kyar ma idan Mujaheed bai fi sa kudi ba, kudin uban yaron ke rarumowa ya xo nan yana mana burga yana yaudaran jikata wllh, lkci daya kuma Allah ya toni asirinsa, ai wannan auren da kike gani Rukayya mai raba sa kilan mutuwa kawai xai yi a banxa a hofi, kawai ni dai abinda na sani shine dolen Mujaheed ya hada akwatuna irin wanda su Bulasawa suka kawo mana da gwalagwalai idan ko ba haka ba wllh sai in ce a raba auren baki na a leko don jikata ba gantalalliya bace, sannan da kyar idan baxae karo Sadaki ba, ke dai da Aysha da wuya ku ga annabi wllh, ban ta6a ganin mutane irin ku ba a duniya, ita ta tashi ta gudu da yarinya kamar mahaukaciya ba don su Ahmadu da suka dakatar da ni ba wllh da naje da dauko jikata da daddaren nan" Umma da hankalinta ya kai kololuwa gun tashi ganin Inna ta juya xance gaba daya on like da safe da ta dage sai anyi saki ko tayi ma su Abba Allah ya isa, tasan kuma ai shkkn aikin gama ya gama tunda Inna ta canxa labari don dama wajenta kadai take da hope, ynxu kuma bbu hope din, mikewa tayi ta fice daga parlon da sauri, bata yi nisa tana tafiya ba ta xauna nan kasa kan hanya ta rushe da kuka sosai tace "Na shiga uku na lalace na cuci kai na, yanxu d'a na aka makala ma sauran ciwo ina ji ina gani?? Wllh sai na raba auren nan ko ta halin yaya, Mujaheed baxai taba hada jini da xuri'ar Aisha ba, da auren nan ya rayu gwara in mutu kawai, in sha Allahu sai ya saketa sai dai idan ba ni na haife sa ba, wato yana ma son auren kenan tunda har ya gudu ba labarinsa....." ta kuma fashewa da matsanancin kuka xuciyarta na mata xafi, ko mutuwar ubanta bata ji ciwonsa irin yanda take jin ciwon wannan auren ba, ji tayi dama ayi backward din komai ta bar Sadeeq ya auri Imaan, ko bakomai xata yi mingling da manyan mutane da dangin Bulasawa ayi hotuna su kai Imaan kantamemen gidanta, yanxu Imaan ta auri Sadeeq ba ma lallai taga irin rayuwar da suke da Sadeeq din ba balle ta ji haushi ko ya dameta, ita da ganin Imaan sai in ta xo gida, amma wnn wai yaron cikinta ne xai yi rayuwa da Imaan din tana ji tana ganin komai da idanuwanta, tashi tayi tana kuka sosai ta wuce apartment dinsu tana cewa "In sha Allahu sai ya saketa, sai in bani nayi nakudar sa ba, in sha Allahu bbu aure tsakaninsu, d'a na ya fi karfin sauran ciwo, ta ina xai fara rayuwar aure da ita ta talauta min shi da ciwonta" ranan dai Umma yanda taga rana a gantale haka ta ga dare, babban damuwarta da tashin hankalinta me xai faru idan gari ya waye, tasan da kyar idan Hajiyan Marafa baxa su taho gidan tare da duk yaranta su risketa ba, tasan Safeenah ta gama sanar masu duk abinda ya faru da yanda ta dinga kokarin hana auren Imaan da Sadeeq, Umma ta mike xaune ta rike kanta tana kiran Allah ya kawo mata dauki xuciyarta, ni kam nace lallai ma. A bangaren Ammi kuwa sllh ta dinga yi daren ranan don ita ma neman baccin tayi ta rasa rabonta da shiga tashin hankali haka har ta manta, da dadewa ta sha addu'ar kada Allah ya kaddaro masu rana irin ta yau tun daga lkcn da ta lura shakuwan Mujaheed da Imaan ya fara wuce hankali ya dauka, shi yasa ma ta dinga taka ma Imaan burki sai gashi lkci daya bbu notice abinda take gudu ya faru, da yau Yusuf aka hada da Imaan me xai dameta, sai ma ta fi kowa farin ciki da hadin amma Mujaheed kam ya fi karfin 'yar ta. Imaan na cikin duvet ita din ma ba bacci take ba sai juye juye kawai take, xuwa lkcn kukan ma ta kasa wani mugun xaxxabi take ji sosai, duk joints dinta ciwo suke mata ga headache da backache, tasowa Ammi tayi ta nufo ta bayan ta idar ganin juye juyen da take, ta cire duvet din jikinta tana kallonta kafin tace komai taji xafin da jikinta yyi ba kadan ba, Imaan ta mike xaune da kyar ta jigina da gado a hankali tace "Ammi bana jin dadi" Ammi tayi shiru tana kallonta, can ta mike ta wuce kitchen ta hado mata shayi sanin da daddare bata ci abincin kirki ba ta kwanta, ta dawo ta mika mata shayin tace "Ki sha in samo maki paracetamol yanxu" Imaan ta karbi cup din hannunta na rawa, Ammi ta fita xuwa dakin gwaggwo, sllh ta sameta take yi ita ma, ta bude gun da take ajiye magungunanta ta dau pain reliever da man xafi da ta gani ta fita, duk yanda Ammi tayi da Imaan ta sha shayin kin sha tayi wai amai take ji, hakan yasa ta bata paracetamol din ta shafa mata magani duk jikinta ta sa ta kwanta sannan ta lullube ta. Da safe Abba bai hakura da kiran layin Mujaheed dake kashe har sannan ba, lkci daya jikinsa yyi sanyi a nan kuma ya fara considering d'an nasa, to ko shi ma baya son auren ne, yasan dai ko Mujaheed baya so xurfin cikinsa ma baxae bari ya fada ba, shigowar Umma ya sa ya ajiye wayar hannunsa, Umma ta duka kan kneel dinta tana kallon Abba dake kallonta shi ma, Cikin rawar murya tace "Alhaji na xo neman alfarma ne a gun ka ba wai don na isa ba don ni din a ko da yaushe mai laifi ce na sani amma don Allah kar ka biye ta halina kayi ma girman Allah ka saurareni kuma ka min alfarmar da na xo nema" Abba na kallonta yace "Ina jin ki" tayi kasa da kai a sanyaye tace "Alhaji wannan auren da ku ka hada kayi ma girman Allah ka raba sa, na farko Aisha ba son auren take ba, ita Imaan din ma haka, shi kuma Mujaheed sbda tashin hankali kaga ba shi ba labarinsa, ban san inda ya shiga ba, don Allah ka yi min rai kayi abinda ya kamata a wannan batu..." Abba yace "i don't have any say on this matter any longer Rukayya, Sai abinda Inna ta ce, yanda tace haka xa ayi...." Umma ta fashe da kuka tana kallonsa tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, wllh Alhaji Mujaheed dina baya son auren nan, tun jiya fa har yau wayarsa a kashe bamu san inda yake ba" Abba ya mike yace "Yana lafiya in sha Allah" mikewa Umma tayi tana shessheka ta fita tana tunanin meye mafita, don ita da Mujaheed yayi aure da Imaan fa gwara ko da bata mutu ba ta yarda ta rasa komai nata a duniya. Karfe tara Abba da Daddy suka isa gidan gwaggwo, Gwaggwo ta fito daki bayan mai aikinta ta kirata, da fara'a ta amsa gaisuwar su tana masu sannu da xuwa, Gwaggwo ta xauna saman kujera tace "Ya aka ji da taro da hidindimu??" duk suka amsa da Alhmdllh an gode Allah, Gwaggwo tace "Toh madallah Allah maku albarka, Allah kuma yasa abinda ya faru shine mafi alkawari gare mu gaba daya" Abba yace "Ameen, dama xuwa muka yi mu baki hakuri a bisa wannan hukunci da muka yanke baki da masaniya, abubuwan ne suka xo a haka gwaggwo, ayi mana afuwa...." Gwaggwo tace "A'a ba komai wllh Ahmad, ai duk an xama daya, wannan aure kuma da ku ka hada Allah yasa shine mafi alkhairi, Allah maku albarka, su kuma Allah ya basu xaman lafiya, kada ku biye shiriritan matan ku, abinda ya dace shi ku ka yi, anjima in sha Allahu ni da kai na xan maida Fatimar gida, idan Allah ya yarda" Abba yace "Toh Alhmdllh Allah ya kara girma gwaggwo, ita Hajiya Aishar fa??" Gwaggwo tace "Ta d'an fita siyo mata magunguna da yake jiya da xaxxabi ta kwana amma da sauki sosai yanxu, bacci ma take" Abba yace "Toh Allah ya sauwake, xa mu koma Gwaggwo, mun gode
Chapter 221 · 0% Book details