Sashe 124
Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
durkushe a nan nake aiki babu mai taimakona, baki ji bayana ba kamar ya balle in huta...." Maryam ta hade rai ta shige parlonta, Imaan tace "Maryam ce fa Inna" Inna tace "Waye kuma Maryam" Dariya kawai Imaan take tana kallon Inna, Inna tace "ita ce ta xama kamar zal6e?" Imaan ta xauna a balcony din tana dariya, Inna ta tabe baki tace "Ku dai baku son gaskiya a gidan nan, yanxu da ba don wannan yar albarkan Maimoon ta gaya min a boye ba daxu da baxan ma san Hadiza xata xo gidan nan ba, Toh kuma kya taho min da yarinya tsigi tsigi kice Maryam, Yar da aka haifa hannuna ce aka ce maki baxan gane ba, ni fa na mata wankan farko kuma a gabana aka yayeta..." Inna ta tabe baki tace "Ni dai ba ruwana" Fitowa Maryam tayi daga parlon ta yi wucewarta, Inna ta bi ta da kallo ta kyabe baki tace "Ubansu dai ya cuce su ya hallaka su, ya kwashe su ya tafi kasar tsinannu yayi kaka gida, toh tana ma jin hausar kuwa" Imaan dai ta kasa cewa komai sai dariya take, Inna ta gama dauraye bakin tap din ta mike ta shige cikin parlonta tana cewa "Bukar dai ya haifi jaraba, ba don naka naka bane ai ni bana bari a cuci Bulasawa a lika masa ke ba, to banda haka ni sa'ar uwarki ce xaki xauna bakin kofa kina babbaka min dariya kamar mahaukaciya?? ita ma Hadizar dama kada ta kuskura ta xo min nan xan koreta tunda bata maida ni bakin komai ba, banda haka ta kamo hanya rai kwakwai mutu kwakwai baxata gaya min ba in mata addu'a, wannan ba shawarar kowa bace illa wannan mutumi Bukar don shi ne me irin wannan tunanin na marasu nutsuwa, Amadu baya haka" mikewa Imaan tayi ta bar wajen ta koma part din su... Bayan magrib tare Abba suka tafi gun Inna da Maryam, Inna na xaune parlon tare da Mama Hadiza da Mujaheed, Inna na ganin Maryam ta washe baki tace "Yanxu nake rokon Mujaheed ya tashi ya nemo min ke don tun saukan ku bamu hadu ba kin xo daxu ina gurje bakin pampo ke kuma baki jira in gama ba kika yi wucewar ki" Maryam ta xauna ta gaisheta babu walwala, Inna ta amsa da fara'a tace "Kun sha hanya, sai kawai naga kin kusa kamo imaan a tsayi..." Maryam dai bata tanka ta ba, Mama Hadiza sai murmushi take, Abba ya gaida Inna ta amsa tace "Ae gwara da ba a gaya min suna hanya ba Ahmadu da baccin kirki ma ni baxan yi ba, amma da na gansu kamar daga sama ai yafi ko" Abba na murmushi yace "Gaskiya ne" Mikewa Mujaheed yyi ya fita parlon Maryam ta bi bayansa, a jere suke tafiya tace "Ya M.A kaga abinda Inna ta min daxu kamar bata taba ganina ba" Dariya Mujaheed yyi yace "Xata maki fiye da haka ma, so take it off ur mind plss haka nan take, ya karatu?" tace "Alhmdllh...." Ya kalleta yace "Hope baki kula samari sai kin gama karatun" tayi dariya tace "Kai ya M.A, bayan ga Imaan ma tana da saurayi, ta ma ce min xai yi birthday soon and his frnds will be celebrating it for him, wai in bata shawarar abinda xata basa" Tsayawa Mujaheed yyi yana kallonta, can yace "When tace maki birthday din?" Ta wara ido tace "I didn't ask her, mun ma gaisa da shi a waya yace xai xo gobe ya gaisheni, his voice is cute..." Tana murmushi ta kare maganar, Shiru yyi bai ce komai ba ya ci gaba da tafiya a hankali tana biye da shi, Xaro ido tayi tace "Wait... Am I even suppose to tell you this??" Yar dariya yyi yace "Me yasa kika ce haka?" Tace "Naga irin kamar you are surprise.... Kila ma baka san tana da saurayin ba ni ce na maka revealing koh?" yace "Yes.. boye mana take, Amma kar fa ki ce mata kin gaya min she won't be happy" Maryam ta marairaice tace "Toh nima kar ka mata magana about it she won't be happy with me...." Yace "Sure I won't" suna isa part din su Imaan tace "Am spending the night here, ka ce ma su Maimoon, Ummi da Rahma su xo muyi hira plss" yace "Ohk xan gaya masu" daga haka ya wuce, tafiya yake amma gaba daya abinda Maryam ta gaya masa ne ke yawo a ransa... Wani murmushi yyi ya shiga sashin su.