← Book details Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 300

Sashe 52

Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

gadon ya fara hada alluran yana gamawa ya juya yana kallonta yace "Kee" tayi nisa baccin dama gata mai nauyin bacci, sanin haka ya ja hancinta yace "Imaan" bude ido tayi da kyar xata kara rufe idon yace "Baxa ki tashi ba?" A hankali tace "Yaya me xan yi kuma" Ta bude ido sosai ganin abinda ke hannunsa ta mike xaune da sauri tana jan rigar ta xuwa chest dinta tace "Yaya wa xaka ma alluran?" Yace "Gado" kamar xata yi kuka tace "Ka mance na sha magani ne" yace "Kar ki bata min lkci my frnd" ta fashe da kuka tace "Na shiga uku Ammi ni ban ce a min allura ba" Tana fadin haka xata mike ya fixgota ya kwantar da ita ya daga rigar jikinta ya mata alluran ya mike ya fice daga dakin, sai da Ammi ta shigo dakin tana mata mugun kallo sannan ta hakura da kukan ta koma ta kwanta nan da nan kuma bacci ya dauketa. Imaan na dawowa schl ranan litinin taga calls har biyu da ta yi missing, bayan ta idar da sllh tana xaune kan darduman ta dau wayar tayi dialing number din, har ya katse ba a dauka ba, few seconds later sai ga call din ya shigo wayarta, dagawa tayi ta kai kunne, sallama aka yi daga daya bangaren cikin cool voice, tayi shiru da farko, can kuma tace "Waye ne?" Yace "Baki amsa sallama ne?" Tace "Not a must in amsa a fili, who are you" yayi murmushi yace "Ohk then, how are you?" Tace "I asked who are you first?" Yace "Tsoro kike ji?" Tace "Sorry i think it's a wrong call" yace "Why do you say so?" Tace "Because without any doubt I know it's only my dad, mum.... and very few dat have my contact" yace "Ohk... Muhsin ya sa in kira in ji ko kin shiga gida lafiya" ta d'an bude ido da mamaki amma ta kasa cewa komai, yyi murmushi a hankali yace "How are you Imaan?" Murya can kasa tace "Alhmdllh" yace "I guess yanxu kika dawo schl?" Tace "Sure" yace "Alryt, sai islamiyya ko?" Tace "Eh" yace "Ohk then Allah ya kiyaye hanya, amma tare xa ku yi sauka da su Mariya?" Tace "In sha Allah" yace "Saura wata nawa?" Tace "Two months" yace "Maa sha Allah, we will talk later kar kiyi latti" tace "Sai anjima" daga haka ta katse wayar ta mike ta fara shirin Islamiyya. Bayan Magrib Mujaheed na xaune parlon Abbansa da duk yan gidan, Yusuf ma dake xaune wayarsa kawai yake ta dannawa a parlon, Anty duk ta fiddo ankon bikin Seeyama suna nuna ma Abba, Umma dai na xaune ta hade rai don gani take kamar Anty shishshigi kawai take mata, Anty tace "Toh Abba ga kaya nan, gaba daya kala uku ne" Mujaheed yace "Toh duka kala ukun xa su yi?" Anty tace "Ehh ko kana da damuwa da hakan??" murmushi yyi bai ce komai ba, Yusuf ya daga kai yace "Amma fa Anty yayi yawa sai kace su ne..." Mugun kallon da mahaifiyar tasa tayi masa yasa yyi shiru ya ci gaba da danna wayarsa, Abba yace "Kice expenses ne ba na wasa ba, to da wanne ku ke son mutum ya ji, ina laifin ma kala biyu?" Umma tace "Haba Alhaji, abu dai na rana daya lkci daya, ni fa da cewa ma nayi kala hudu hudu Amina tace a bar shi a kala uku kawai" Abba ya gyada kai bai dai ce komai ba, Anty tace "Idan ma baxa ka siya masu ba ga yayyinsu sai su masu" Umma tace "Atoh dai" Yusuf yace "Mu dai sai dai muyi masu kala bibbiyu" Anty tace "Toh ka rike kudin ka" Dariya yayi yace "Shikenan ni sai in ma Rahma da Ummi M.A yayi maku sannan yayi ma Maimoon" Umma tace "Sai kayi ma Kakarku ko kala biyu ne ita ma, shikenan it's settled" Yusuf ya dinga kallon Umma bai ce komai ba, Abba yace "Toh mamana fa?" Anty ta buda ido tace "Ai kuwa Imaan... kaga na ma mance wllh, shikenan sai Mujaheed yayi mata kaga hakan ma is settled" Abba yace "Ehh sai Mujaheed yayi mata" Umma ta yi ma Anty wani kallo tace "Wani Mujaheed din, shi Yusuf me ya hanasa yi mata?" Anty tace "Saboda kince yayi ma Kakarsu, kinga Mujaheed sai yayi ma Imaan" A fusace Umma tace "Toh an ruguje wannan tsarin kowa tayi ma 'yar ta, Inna kuma Alhaji ko baban ita Imaan din su yi mata" Abba yace "Ba tsarin da ya ruguje Hajiya, Mujaheed yayi ma ke, Amina... da maimoon sai Imaan, Yusuf kuma yayi ma Ummi, Rahma da Inna, kuma a cire ma imaan nata a kai mata yanxun nan" Anty ta cire ma Imaan kala uku, Abba ya kalli Mujaheed yace "Dauka ka kai mata" Mujaheed ya kalli Umma da ranta idan yayi dubu a lkcn ya baci, Anty tace "A'a jira, yi min transfer din kudin Imaan din yanxu tukun, sauran ko daga baya ne sai ka yi" Mujaheed ya kasa cewa komai, Anty tace "Malam ka min shiru ina maka magana m" ya dau wayarsa gabansa na faduwa sai dai bai yadda ya kalli Umma da ko ba a fada masa ba yasan kallonsa take, ya gama danne dannensa yace "Anty ina jin ba network...." Ta mike ta isa kusa da shi ta amshi wayar tace "Baxa ka raina min hankali ba" sanin Gtb yake amfani da lkci daya ta danna transfer code dinsu tayi komai ta sa har account number dinta bayan ta sa amount sannan ta mika masa tace "Sa min pin" Karba yyi ya sa pin din ta amshe wayar, duk ya kasa kallon Umma, sai da Anty ta ga transfer din yayi sannan ta basa wayarsa ta koma ta xauna, lkci daya aka turo masa debit ya bude ya ga 30k ta yi transfer, Abba yace "Toh ka dau kayan ka kai mata sai kace mata kai ka siya mata" Kasa tashi yayi, Abba ya hade rai yace "Are you stupid ina maka magana kana xaune, wato abinda kake nufi shine baka jin maganar kowa gidan nan sai na uwar ka koh, ina fa lura da kai kuma nake sharewa" Tashi Mujaheed yayi ya dau ledan kayan ya nufi kofa, Umma ta mike fuu ta wuce sama, Anty tayi wani murmushi a ranta tace "da sauki ai tunda ba bin sa xa ki yi ba" A hankali Mujaheed ya murda kofar apartment dinsu Imaan ya shiga da sallama murya can kasa, Imaan ce durkushe parlon da yar ves sai skirt iya cinya, nose mask na hancinta tana goge gogen kayan da ke daukan k'ura a parlon, ta mike ta cire abun bakinta tana kallonsa, Ammi ta fito parlor jin an shigo, yyi kasa da kai ya ajiye ledan hannunsa kan kujera yace "Abba yace a kawo mata" daga haka ya juya ya fita ya kulle kofar, Imaan xata bude ledan Ammi ta mata tsawa, dakatawa tayi da sauri, fuska daure Ammi tace "Kina ganin ya shigo amma kika ki wucewa daki da wannan shegun kayan jikin ki koh, tun daxu nake maki magana ki nemi kayan arxiki ki sa ko don saboda ciwon ki sannan kada wani ya fado amma kin maida ni mahaukaciya, ke kam wace irin yarinya ce Allah ya bani, in ji hankalin ki ya kwanta da ya shigo ya ganki a haka?" Imaan sai kallonta take da mamaki tace "Ammi yaya ne fa" Bude baki Ammi tayi tana kallonta, can tace "Sai aka yi ya don shi ne?" Tace "Toh Ammi shi ne fa ba wani ba ya shigo, dama dai ya Yusuf ne kin san baxan tsaya haka ba" Ammi ta kasa daina mata kallon mamaki tace "Shi yayan muharramin ki ne Imaan?" Imaan ta xaro ido tace "Ammi yaya fa har wanka ya taba min ina karama, kuma da ba shi ke sa min kaya ba ma idan ban sa ba, ni dai bana jin kunyarsa wllh, dama dai yaya Yusuf ne shi ko dankwali bana tsaya kusa da shi ban sa ba, shi kuma yaya ni xan ma iya cire kaya a gabansa, toh har yau ba yana shafa min magani a kafana da bayana ba, ko wajen inna idan yana nan ina....." Ammi taga bude baki fa ba nata bane ta dau daya daga pillows na kujera ta jefa mata a mugun fusace tace "Ban taba sanin ke shahararriyar mahaukaciya bace sai yau, wato iskanci yasa kike cewa ya shafa maki maganin xafi koh, to in sake gani sai na ci uban ku ke da shi, kuma kar ki fasa cire kaya gabansa tunda ke shashasha ce, sai kace warce bata taba shiga ajin islamiyya ba wai kina cire kaya gaban namiji da ba muharramin ki ba" Imaan ta nufi daki kamar xata yi kuka tace "Ni fa ba yanxu nake cewa ba Ammi, da da nake nufi, kuma naga ai yayana ne shi tunda ba ni da wani yayan" ganin Ammi ta yo kanta ta shige dakinta da gudu ta sa makulli tana turo baki kamar xata fashe da kuka.
Chapter 52 · 0% Book details