Sashe 151
Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
sannan ta kalli inna bluntly tace "Ba a kai ga sauke min gara na daga container da ya kawo ba, ba komai yanxu haka s gidan" Wani kallo Mujaheed ya dinga mata trying hard to control his temper, inna ta rike ha6a tana kallonsa tace "toh me ku ke ci a gidan ba a sauke gara ba ni 'ya su?" Safeenah tayi wucewarta sama, Mikewa Mujaheed yyi ya bi bayanta, yana shiga dakin ya kulle kofar yana nunata da yatsa cikin tsawa yace "Let me give you this warning Safeenah, idan baki son na fito maki da the other side of me you've got to respect that woman to the fullest, she is my grandma kuma albarkacin ta yasa kike gidana, wllh wllh xan yi taking action din da xai baki mugun mamaki idan baki maida hankalin ki ba, sannan breakfast ni nace ki tashi ki fita kije ki girka masu yanxun nan...." A tsawace ya kare maganan yana kallonta, Gaba daya ta gama tsorata sai kallonsa take tana komawa baya, lkci daya hawaye ya kawo idonta sai kuma ta fashe da kuka tace "Is this the real you dama Mujaheed?? me yasa tun farko baka yi encourage dina wajen ganin nayi kokarin hakura da kai ba, you are always telling me xaka koyi sona I shouldn't worry, dama ka aureni ne to make life a living hell for me, kasan irin mutanen da na ki amincewa da nace sai kai?? Kasan mutanen da na watsa ma kasa a ido nace sai kai, dama laifine son mutum da xuciya daya?? Tun da aka kawo ni gidan nan ka ki ko da xama na minti ashirin a dakina balle ka kwana, wllh ina sonka Mujaheed, ban aure ka saboda komai ba sai saboda Ina son kasancewa da kai, ka dai san irin gidan da na fito balle kace saboda wani abu naka na aure ka" dauke kai Mujaheed yyi xuciyarsa na bugawa, right from time a rayuwar sa na duniya ya tsani ganin hawayen mace, a hankali ya karasa inda take ya xauna gefen gadon ya jawota jikinsa cikin sanyin murya yace "I won't make my home a living hell for you Safeenah, and sure I will create a soft spot for you soon, but you've got to respect my family, duk abinda nace bana so kuma plss try to avoid that, Kinga ke yan uwanki baxa su xo in masu gaisuwar walakancin da kika ma grandma dita ba...." lamo tayi jikinsa tace "Amma kana ganin wannan yarinyar fa bata gaisheni ba ma" Shiru ya d'an yi, Sai kuma yace "Mind you sunanta Imaan, and kar ki damu xan mata magana" tace "Step sis dinka ce?" Ya girgixa kai a hankali yace "She is my cousin sis" daga kai tayi tana kallonsa, ya gyada mata kai, tabe baki tayi bata ce komai ba, yace "Toh for my sake kiyi hakuri ki hada breakfast din even if it's just Irish and egg, sai ki dafa ruwan shayi" Shiru tayi masa yace "Xa ki yi?" A hankali tace "Toh" murmushi yyi ya manna mata kiss a goshinta, ta lumshe ido don ba kadan ba taji dadin hakan, ya mike yace "Come out soon" daga haka ya nufi kofa ta bi sa da kallo, Allah yasan so ba na wasa ba take ma Mujaheed, Bata taba yi ma d'a namiji irin son da take masa ba, kuma xata iya yin komai a kansa. Mujaheed na dawowa parlor ya tadda Imaan kadai tana kallo, tun da ta kallesa sau daya ta dauke kai, ya isa kusa da ita yace "Me yasa baki gaida Safeenah ba?" Ta turo baki ta ki cewa komai, ya dafa kujeran da take xaune yana kallonta da kyau yace "Look, duk kika xo gidan nan ko kika ganta a wani waje dolenki ki gaidata coz she is my wife... Kin ji abinda nace??" Ta hade rai tace "Toh ai ita ma ba da respect ta gaida Inna ba da ta sakko, so why will I greet her, why??? beside she is suppose to tell me... Sannu da xuwa kafin in gaisheta, amma ko kallona bata yi ba so nima naki gaisheta din ai ba wajenta muka xo ba...." Kallonta kawai yake ganin yanda take maganar cike da tsiwa tana xare masa ido, ya dauke kai ya d'an yi murmushi, can dai ya mike ya nufi kitchen jin muryar Inna kasa kasa ita kadai tana magana, tsaye yyi bakin kofa yana kallonta tana duke tana fere dankali tana cewa "Idan ba jaraba ba da safen ma ya wani bi figaggiyar mata kamar xabiya daki bayan kwana da yayi a dakin daren jiya, to meye xasu shige daki kuma da safe bayan nace masu ban karya ba ga 'yar mutane na taho da ita, ita ma bata karya ba, dama da ya iyayenta suka yarda ta biyoni, ni dai ba ruwana..." Dariya sosai ta basa, tana ganinsa tayi shiru tace "A'a har ka fito Mujaheed" yace "Dankali kike ferewa da kanki kuma?" Inna tace "Yo baxan fere ba tunda na kwaso yunwar cikina Mujaheed, ga Imaan ma bata karya ba da kyar Bukar ya yarda ta biyo ni... Abu dai da raina da lafiya ta, ita wancan matar dake xaune parlor tace ba ruwanta baxata shiga kitchen din mutane ba, ni ban gane ma wannan abun ba gaskiya" ya shafa kansa yace "Yanxu Safeenah xata xo ta hada maku kayan karin" inna ta ajiye wukar tace "Toh amma anya ka ce mata nice na raine ka kuwa...." Safeenah na sakkowa parlor ta dinga yi ma Imaan wani kallo sak na tsana tana tafiya, suna hada ido Imaan ta tabe baki ta dauke kai.... Tsayawa Safeenah tayi tana kallonta xuciyarta na tafarfasa tace "Beware a gidana kike.... you had better respect ur self ki maida hankalin ki" Kallonta Imaan tayi da sauri tace "Gidan ki ko gidan yayana? Gidan ku na can kin baro sa malama don haka baki isa ki min warning a gidan Yaya ba...." Da sauri Inna ta karasa fitowa kitchen jin muryar imaan, Mujaheed ma ya fito ya tsaya kallonsu da mamaki, Inna tace "Lafiya?? me ya faru??" Imaan tace "Wai inna ki ji ce min take in shiga hankalina wai nan gidanta ne, wllh ba abinda na mata daga sakkowarta ta fara min fada tana min warning" sake baki Inna tayi tana kallon Safeenah tace "Ba lafiya, ta shiga hankalinta kuma? Kinsan wacece ita kuwa yar nan, to bari kiji wllh wannan da kike gani ta fiye ma Mujaheed ke so dubu dari, kaji min mata kamar zabiya dai, ita da gidan yayanta kice ta shiga hankalinta sabida baki da tsoron Allah?? To wllh a kan Imaan sai Mujaheed ya kora ki gidanku yanxun nan, gwara ma ki xageni da ki ta6a min imaan gaskiya, duk da dai kin ma xageni tun daxu kawai dai ni me hakuri ce na ja bakina nayi shiru, kaji min mokadaddiyar mata dai xata sa min jika a baki in shiga uku???" Mikewa Imaan tayi kamar xata yi kuka ta nufi kofa tace "Ni sai kin dawo Inna baxan xauna ba...." Inna ta saki salati tana tafe hannu tace "Na shiga uku ni patuu, Mujaheed ya auri jaraba tunda ta ta6a imaan, ke me ya kai ki kinsan wacece kuwa, ita kenan fa uban ya haifa a duniya, ko kallon banxa ba a mata balle a mata fada... Shi Mujaheed din bai xaunar da ke ya sanar maki bane??" Bin bayan Imaan Mujaheed yyi ganin har ta fice parlon.