← Book details Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 119 OF 300

Sashe 119

Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ja baya Imaan ta dinga yi ganin kallon da yake mata fuskarsa a daure, ta 6ata fuska kamar xata yi kuka, a hankali tace "Yaya fita fa xan yi...." Bai tanka ta ba kuma bai fasa bin ta ba tana komawa baya, ganin kiris ya rage ya risketa ta koma can kusa da window din dakin ta tsaya xuciyarta na bugawa tace "Wayyo ni dai ka kyaleni in fita, me na maka" dab da ita ya tsaya, xata durkusa ya dago ta yace "Training da Ammi ta maki kenan na ba ma namiji hannun ki yayi kissing a bakin mota kina washe baki koh?" Ta wani xaro ido tana kallonsa, tsawa ya mata yace "Baxa ki bani amsa ba sai na baki dirty slap?" Tsorata tayi ganin babu wasa fuskarsa, kamar xata fashe masa da kuka tace "Ni fa Yaya...." Fixgota yayi lkci daya idanuwansa suka canxa yace "Ke fa me?" Kasa cewa komai tayi, ta hadiye abu da kyar tace "Don Allah kayi hakuri, ni bani na basa hannun...." Bai jira ta karasa ba ya buge mata baki da karfi, Ta kai hannunta da sauri bakinta, lkci daya hawaye ya kawo idanuwanta, cikin husky voice yace "I am making you this promise... babu abinda xai hanani gaya ma Abban ki sooner or later...." ta wani gwalo ido a rikice tace "Don Allah Yaya kayi hakuri wllh ba da gangan yayi ba shi ma bai sani ba" Bai san lkcn da ya kara buge bakinta ba, tayi tsit hawaye na sauka idonta, yace "Wato ke yanxu kina ganin kin girma kin isa tadi da maxa, har wani rawan jiki kike ki fita idan ya xo, har da jan sa xuwa parlon ku ki ajiye masa nama a gaba Saboda kinga Inna na goya maki baya, to bari ki ji abinda baki sani ba, as far as I Muhammad is concerned babu aure tsakanin ki da mutumin nan, you had better stop wasting ur time and face ur study, kamar yanda na xa6a ma Seeyama miji ke ma haka da kai na xan xaba maki mijin da ya dace da ke, duk ki gama rawan kanki xaki sha mamaki na, wannan mutumin da kike gani is just here to spoil and use you, ba so na tsakani da Allah yake maki ba, ki bar ganin yana kashe maki kudi ki xata wai son Allah yake maki, lalata maki rayuwa xai yi which I will neva allow, and let me give you this warning....." Ita dai hawaye kawai take xuciyarta na bugawa tana kallonsa, "Daga yau kika sake tsayawa kusa da motarsa sai na kusa sumar da ke wllh, duk karyar da xai maki ya maki a waya ba sai ya sake xuwa kofar gida ba, idan kuwa ba haka ba a gaban daddyn ki xan xane ki sai dai duk abinda Inna xata yi tayi..." Kuka kawai imaan take bata ce masa komai ba, strictly yace "Am I clear?" Ta gyada masa kai da sauri, muryar Inna suka ji tana cewa "Naga abinda ya isheni ni patuu na 6ata a gidan Mujaheed" sai kuma ta kwalo masa kira, bude kofar Mujaheed yyi ya fita ya jawo kofar, Imaan ta durkushe a dakin tana kuka a hankali, Inna na ganin Mujaheed tace "Alhmdllh, ni na xata 6ata nayi, Toh ita kuma matar ina ta shiga, har kasa fa na sauka ban ganta ba, kada ta shiga wani waje in shiga uku dama ga Bukar ya xama abun tsoro, ba da xuciya daya ya yarda ta biyo mu ba" Mujaheed yace "Tana waje, muje ki ga dakin dake kasa" Inna tace "Na waye dakin?" Yace "Baki" inna tace "Irin su Hansai da 'ya yanta knn idan sun xo" murmushi yyi ya bude kofar parlon yace "Har ke ai" Bai jira cewarta ba ya fice. Har garden sai da Mujaheed ya kai Inna ya xaga duk gidan da ita, tana kallonsa tace "Toh ai tun yanxu ya kamata mu shiga gun makota a san juna kafin mu tare, ko ya kaga?" Kallonta yyi ya dauke kai, tace "A'a ba xancen dauke kai ba yana da kyau in san su su san ni, ko haka mutum xai ta xama ba jama'ah a gida, ai mutane Rahama ne" Mujaheed yace "Sai ki jira idan kin ga dawowarki gidan" Inna tace "Wannan gaskiya ne, to ni na shiga uku ban fa yi la'asar ba Mujaheed" yace "Toh mu je ciki kiyi" parlon suka koma ya nuna mata dakin dake downstairs yace "Sai kiyi alwala a bayin ciki kiyi sllhn" tace "Toh dakin su Hansai kenan" shi dai bai ce mata komai ba ta wuce ciki, kallon agogo yyi sannan ya wuce sama, parlonsa ya shiga ya bude kofar dakin, durkushe ya ganta inda ya bar ta har sannan tana kuka, tana ganinsa ta mike tsaye, karasawa cikin dakin yyi, ta hadiye kukan da take ta sunkuyar da kanta, takawa yayi har gabanta ya tsaya ta ki yarda ta daga kai balle ta kallesa, ya dago kanta a hankali, ta kallesa sai kuma ta fashe da kuka ta juya masa baya, xagawa yayi gabanta ta rufe fuskarta tana shessheka, d'an murmushi yyi, kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "ki dinga jin magana ta idan baki son na dinga sa ki kuka" ta kara juya masa baya cikin kuka tace "Ni bana soo" xagawa ya kara yi gabanta ya jawo ta kusa da shi, ta kuma fashewa da kuka, ya d'an hade rai yace "Toh baxa ki yi shiru ba" kin cewa komai tayi, ya ja ta xuwa bathroom, ruwa ya bude yana kallonta ta madubi a hankali yace "Wash ur face now" ta turo baki ta ki cewa komai, tara hannunsa yayi ya debi ruwan ya dukar da ita ya shiga wanke mata fuskar, yana gamawa ya ciro handkerchief dake aljihunsa ya fara goge mata ruwan fuskar, yana kallonta ta madubi yace "Promise me xaki fara jin magana ta daga yanxu...." Kin cewa komai tayi ya hade rai yace "I am talking to you" da kyar tace "Na ji" yace "Kin ji me?" A hankali tace "Abinda ka ce" mayar da handkerchief din yyi aljihunsa ya juya ya fita bathroom din, murguda baki tayi ta juya tana kallon kofar bayin. Parlor Mujaheed ya xauna yana danna wayarsa har Inna ta fito dakin da ta shiga yin sllh, tace "Wai Mujaheed ni fa ban ji motsin Imaan ba.... A rufa min asiri mu dubota" Mujaheed yace "Tana sama ai" Inna tace "Toh ni dai mu je in ganta" bata jira cewarsa ba ta nufi stairs ya mike ya bi bayanta, dakinsa ya shiga da ita suka ganta tsaye jikin window waya kare a kunnenta, tana jin an bude kofa tayi saurin dauke wayar daga kunnenta tayi tsuru tsuru, kallonta Mujaheed ya dinga yi, Inna tace "Toh ke daga ganin gida sai ki shige dakin matar mutane ki xauna, jira xa ki yi Allah ya kawo lkcn naki da Bulasawa ae" Juyawa Mujaheed yyi ya bar bakin kofar, Inna tace "Toh fito masu a daki yi hakuri haka" imaan bata tanka ta ba ta nufi kofa gabanta na faduwa ta fita, Inna ta bi bayanta, balcony suka tadda Mujaheed suna fitowa ya kulle gidan da makulli ya tafi gun motarsa, imaan bata yrda ta kallesa ba ta bude front seat ta shiga kamar munafuka Bayan Inna ta shiga baya, ya ja motar ya fita compound din yyi ma Mai gadi sallama. Suna hawa saman titi Inna tace "Ni dai Mujaheed da dai in samu kaza in siya, naji raina na so sosai" Mujaheed yayi parking dai dai gun masu gashin kazan da ta gani ya sa tayi magana, tana washe baki tace "Allah dai ya maka albarka" Bai ce komai ba sai ma jinginar da kai da yayi da kujeran motar ya lumshe ido, Inna tace "Toh ko ta fita ta amso?" Ba tare da ya bude idon ba yace "Ehh" inna tace "Toh guda nawa?" Jin bai ce komai ba Inna ta gyara xama tace "Ko guda uku ai yyi, Ni daya ita daya, yan sa ido kuma sai in kacalcala masu daya" Mujaheed yace "Ohkk" Inna tace "Yi maxa ki sauka imaan, kice masu su xabo manya don Allah na tsohuwa ce kuma ba miji gareni ba" Imaan ta bata fuska ta juya tana kallon Inna, inna tace "Naga Ikon Allah, ko in sauka da kaina ne? Me mutanen xa su maki ko ina ruwanki da su" bude motar Imaan tayi ta fita ta tafi gun masu gashin, Mujaheed ya bude ido ya bi ta da kallo daga cikin motar, ba laifi akwai maxa a gun, imaan na sunkuyar da kai ta amsa tambayar da masu wajen ke mata tace "Guda uku" tana ta tsaye har aka gama packaging kajin a leda daban daban ta amsa ta nufi gun mota ta bude back seat tana kallon Inna tace "Wai dubu hudu da dari biyar" Inna tace "Toh ni xa ki gaya ma? sai ki gaya ma me siyan ai" Ta madubi Mujaheed ya kalleta yace "Waye me siyan ban da ke?" Inna ta gwalo ido tace "Ban gane ba" ya buda ido sosai yace "Ko sisi bani da shi, ban fito da kudi ba" Inna ta saki salati mai tsayi tana xaro ido tace "Nima ko sile ban fito da ba Mujaheed" Mujaheed ya daga kafada yace "Sai ki san abinda xaki ce masu" Inna ta kara sakin salati tace "Yau babu lafiya ni patuu an kacalcala kaji uku ba kudi" shi dai Mujaheed bai sake ce mata komai ba, ta kalli Imaan da xaro ido tana kallonsu, Inna tace "Maxa maida masu tsiyar su kice basu da girma an fasa siya, maxa koma" Imaan ta wani xaro ido tace "Iyyee, bayan an yanyanka wllh ni ba inda xan je" a fusace Inna tace "Da aka yanka ci muka yi? Ni naga abinda ya isheni, ki juya ki mayar masu kayansu ba mu da halin biya" Imaan duk ta rikice barin yanda taga duk mutan wajen na kallonsu tace "Na shiga uku, wllh Inna baxan iya komawa dubi fa maxa a wajen da yawa" jaraba Inna ta dinga yi inda take shiga ba nan take fita ba tace "Mazan banxa maxan hofi ina ruwanmu da su
Chapter 119 · 0% Book details