Sashe 175
Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kai, Inna tace "Toh shi ya ga duhu wllh, tashi ki shiga kiyi wankan ki, shi yaga duhu" Imaan ta mike ta dau towel ta daura tana turo baki ta wuce bathroom, Inna tace "Kaji min gantalalle, Toh wani salon iskanci ne wannan xai shigo maki daki kin tu6e?? Ni dai ba ruwana, don mutum yyi aure kuma sai ya fiddo da fi'ilin iskanci iri iri, Toh wllh shi ya ga duhu" Tana fadin haka ta sa makulli a kofar tace "Ba ruwana" Tun daga wannan rana da imaan ta ga Mujaheed xata canxa hanya ta wani daure fuska..... Inna na parlor ta daura kafa daya kan daya da yamma tana kallon wani film Ummi ma na parlon ta gama mata kitso kenan, Inna sai tsine ma boss din film din da suke kallo take, duk ta cika parlon da muryarta, Ummi sai dariya take tana cin soyayyen nama da Inna ta yarfa mata a plate, sallama aka yi bakin kofa Inna ta amsa tana kallon kofar, Sadeeq ne ya shigo da leda a hannunsa, Inna ta mike da sauri tace "A'ahh sannu da xuwa Bukar, kai ne da yamma haka, Bisimillah" ya karaso yana murmushi ya xauna, Inna tace "Ya iyayen naka?" Ya xauna yace "Alhmdllh, suna gaishe ku" Inna tace "Tohh ina amsawa wllh, Ummi tashi ki debo masa ruwa a fridge da lemo, idan kuma baxa ki ba in tashi" Ummi dake kallonsa ta gefen ido ta mike ta nufi kitchen, ba a dau lkci ba ta dawo ta ajiye masa tray din drink da ruwa ya kalleta yace "Nagode" Ummi ta koma ta xauna tana kallonsa, Inna na kallon Ummi tace "Toh kiyi wucewar ki ai mun gama kitson ko? Allah maki albarka" Ummi ta wani hade rai sai kuma ta mike ta nufi kofa, ko ba a gaya ma Sadeeq ba yasan kanwar Mujaheed ce don kamar da suke ba na wasa bane, Inna ta tabe baki bayan ta fita tace "Toh sai ta wani xauna cikin manya, ai bai dace ba" Sadeeq na shafa kai yana murmushi yace "Dama Ina son xa mu yi magana ne Kaka" Inna ta gyara xama tace "Toh Bismillah, Ina jin ka Bukar in ji dai lafiya" Yace "Lafiya lau, dama Kaka Abbana ne ke min maganar aure tun da dadewa, na gaya masa yanda muka yi da ku a nan yana ganin kamar kawai xance nake masa...." Inna ta katse sa tace "Aa ba xance kake masa ba wllh su Ahmadu ne suka dakatar da kai, toh amma ni dama faduwa ta xo dai dai da xama, ba ruwana yau xan kira Ahmadun a gama magana, in sha Allah xuwa nan da Juma'ah ko lahadi xai ce ka turo magabatan ka, kwantar da hankalin ka Bukar in Allah ya yarda komai ya xo karshe, Sakandari?? An dade ba ayi sa ba in har xancen sakandarin xa su kara min, ni ba karamin aikina bane in tura ku kano gidan kawu Salisu ku kai gaisuwan da sadaki can" ya d'an yi murmushi, tace "Allah ba batun dariya ba, ai idan muka ci gaba da biye su Ahmadu da Bukar sai mu yi sa6o mu hallaka, haka kawai su ja mana fushin ubangiji kiri kiri suna fiffita abun duniya kan sunnar ma'aiki" a hankali Sadeeq yace "Toh nagode Kaka Allah ya kara girma" Inna tace "Atohh, duk ya ake ciki xuwa gobe xan kira ka kaji" Yace "Toh xan koma kaka" tace "Toh Allah maka albarka" ya ajiye mata ledan hannunsa yace "Ga turare na kawo maki Kaka" Inna tace "Kamar kasan bbu komai dakina sai fankon gwangwanayen turaren na jera gaban madubi" Yar dariya yyi ya nufi kofa ya bude, da sauri Ummi ta ja baya, sai kuma ta fara tafiya ko takalmi bata tsaya sa wa ba, Sadeeq ya bi ta da kallon mamaki bai dai ce komai ba ya fita ya sa takalmansa ya wuce, A gate ya kusa cin karo da Imaan xata shigo compound din hannunta rike da pack din bottle water, ta koma baya da sauri, ya wara ido ya fito murya can kasa yace "Baby" Ta sunkuyar da kai tace "Ina yini?" yace "Lafiya lau, where are u coming from?" Tace "Na je siyo ruwana ne" yace "Iyye bottle water kike sha kenan" murmushi tayi bata ce komai ba, yace "Toh kawo in taya ki kai wa ciki" ta girgixa kai da sauri tace "A'a nagode" Bata fuska yyi yace "Plss let me help" Bai jira cewarta ba ya kai hannu xai amshi ruwan, hannunsa na ta6a nata ta sake ruwan ba shiri, shima kuma da sauri ya janye hannunsa ruwan ya fadi kasa, dukawa yyi ya dauka yace "Ohh Subhanallah, sorry plss" Murmushin karfin hali tayi ta shiga gidan ya bi bayanta, Xaune Imaan taga Umma da Ummi kan fararen kujera a can Balcony dinsu Umma ta bata attention gaba daya, Imaan ta dauke kai da sauri, shima Sadeeq hakan yyi har suka isa part din su Imaan, imaan na kallonsa tace "When did you come?" Yace "Some minutes ago, am tired Imaan na xo na sami grandma ne plss a ban ixinin in turo magabatana ko ba yanxu xa ayi biki ba..." ita dai Imaan bata ce komai ba, ya ajiye ruwan hannunsa a kasa, ta duka ta dauka tace "Toh nagode sai mun yi waya" daga haka ta wuce ciki, ya bi ta da kallo sannan ya wuce yana murmushi. Abba ne xaune parlon Inna tare da Mujaheed da xuwansa gidan kenan, har Inna ta kai aya a xancen da take Mujaheed sai kallonta kawai yake, Abba dai kansa na kasa, can Abba ya daga kai ya kalleta bayan tayi shiru yace "Toh ai jarabawan ma saura wata daya da sati biyu in sha Allah Inna" Inna tace "Ku kuka jiyo wannan kuma ni ina ruwana, ya xa ku dinga maida ni karamar mutum gaban yaron nan, gaskiya wannan karan bana son magana da yawa sabili da kar raina ya baci, ga abinda nace in dai kuna tsoron Ubangijin ku, meye kuma wata daya da rabi Ahmadu? Shi auren ake gudu kuma yanxu ana rirrike boko hannu biyu, Me yasa ku ke haka?? Ni dai idan na isa da ku gwara a hada bikin ma da na wannan yaron Isuhu tunda an ma kusa kai sadakinsa" Mujaheed dake kallonta har sannan yace "Don dai an jira wata daya da kwanaki ban ga wani damuwa ba, hanxarin me yake??" Inna tace "Amma gaskiya idan xan yi maganar arxiki Mujaheed ya daina shigo min parlona, a daina xuwa min da shi" wani kallo Mujaheed ya dinga mata, tana kallon Abba da karfi tace "d'an bakin ciki ne fa Ahmadu, ya xai yi aurensa yaje can yana morewa da figaggiyar matar sa amma ya dinga yi ma yar Uwarsa bakin ciki, haka yake so tayi ta xama a gida kamar ba mashinshini?" Mikewa Abba yayi yace "Toh shkkn, xa mu ba yaron ranan da xai turo magabatan nasa in sha Allah" a fusace Inna tace "Yaushe?" Abba yace "Nan da ko kwana uku in Allah ya yarda sai a hada bikin da Yusuf yanda kika ce" Inna tayi murmushi tace "Toh Allah ya kai mu lafiya ya maku albarka" kallon Abba da ya nufi kofa kawai Mujaheed yake har ya fita yana amsa maganar Inna da Ameen, can ya kalli inna da ta mike ta fara kakkabe kujeru, yace "Kin kagu ta bar gidan kenan??" A fusace tace "Ba ruwan ka, wai ma dai meye hadina da kai Mujaheed??? Ni dai nasan na haifi Ahmadu amma wllh da babu abinda ya hada mu gwara kayi ta kanka, kiri kiri ka dinga nuna ma jikata bakin ciki??" Yana murmushi ya mike yace "In sha Allahu wannan auren da kike ta 6arin jiki a kansa baxa ayi ba, kuma har tsayuwar dare sai na yi akan hakan" salati Inna ta saki tana kallonsa, sai kuma ta fashe da kuka tace "Baxa ayi ba?? Ehh lallai ka zama dan iska Muhammad, ita yar Bukar kake ma bakin ciki?? Me ta maka xaka mata wannan fatan" ko sauraranta bai tsaya yyi ba ya fice daga parlon, a hankali yake tafiya don shi kansa bai ma san lkcn da ya fada mata hakan ba. Abba na komawa dama ya kira Daddy ya gaya masa yanda suka yi da Inna, Daddy dai bai iya yace komai ba, Abba yace "So yanxu na yanke ranan Sunday as ranan da xa ace ya turo parent din nasa, kai kuma sai ka dawo Saturday or Friday" Daddy ya sauke ajiyar xuciya yace "Toh shkkn Allah ya kai mu, Allah yasa hakan ne mafi alkhairi" Abba yace "Ameen" daga haka suka yi sallama ya katse wayar. Washegari Abba ya kira Sadeeq ya kuma basa izinin turo magabatan sa ranan lahadi, Sadeeq was so happy, farin cikin da bai taba yin irinsa ba duk tsawon rayuwarsa ya dinga yi ma Abba godiya kamar ya masa albishir da aljanna, Mujaheed dai na xaune parlon shi ma don tun safe Abba ya kirasa, amma banda danna wayarsa babu abinda yake, lkci daya ya dago yana kallon Sadeeq suna hada ido ya dauke kai, ya mike ya kai wayarsa kunne yyi excusing kansa ya nufi kofa hakan yasa Abba ma ya bi sa da kallo kamar yanda Sadeeq yyi.