Sashe 203
Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
ba" Imaan ta sunkuyar da kai tana murmushi tace "Idan akwai xan gaya maki ai Ammi" Ammi tace "Toh ki kwantar da hankalin ki and keep praying, kar ki gaji da addu'a, kuma ki dinga cin abinci sosai kin ji" murya can kasa Imaan tace "Toh nagode Ammi" Ammi tace "Ko me kike bukata ki kirani a waya ki sanar min" Imaan tace "Toh bari in je ana jirana" Ammi tace "Toh ki kame kanki" mikewa Imaan tayi ta nufi kofa Ammi ta bi ta da kallo har ta fita ta kulle kofa. Tunda Imaan ta iso part din su Maimoon Umma dake xaune tare da Hajiya Balaraba kan fararen kujeru take kallonta ko kiftawa babu, ta sunkuyar da kai ta gaishesu a hankali Hajiya Balaraba ce kadai ta amsa a dakile, tuni kamshin da take ya daki hancinsu gaba daya, har ta fita gate basu daina kallonta ba, Da ba don Saleem da ya ki barin sa ba da tuni Sadeeq ya bar wajen ganin har bayan minti goma bata fito ba, tana fitowa sau daya ya kalleta ya ci gaba da danna wayarsa, Saleem ya mata murmushi har ta iso inda suke ta tsaya a gefe a hankali tayi masu sallama sannan ta gaishesu kanta a kasa, Saleem ya amsa yace "Hope an gama exams lfya?" Tace "Alhmdllh" Sadeeq ya maida wayarsa aljihu yana kallonta ta cikin glasses din idonsa a takaice yace "Wani shirin xa ku yi a nan gida?" Shiru tayi da farko, sai kuma ta kallesa taga wani direction yake kallo daban, tace "Nima ban sani ba" yace "Ohk then, on Thursday xa ayi dinner...." Yana magana ya bude mota ya fiddo hadadden IV mai yawa sosai ya mika mata ta risina ta amsa, shi dai bai yarda sun hada ido ba, yace "I think that's all, dama sbda IV din na xo, if there is anything I will call and let u know" daga haka ya bude driver seat ya shiga, ita dai sai kallonsa take, Saleem na mata murmushi yace "Toh mun gode amarya, ki shiga ciki xa mu koma" tayi murmushin karfin hali ta juya ta nufi gate, Saleem ya xaga ya shiga front seat, Sadeeq ya tada motar suka bar layin, suna hawa kan titi Saleem yace "Plss ka rage wnn xuciyar Sadeeq... I don't like the way u treated her gaskiya" Sadeeq dai sai driving dinsa yake bai ce masa komai ba, Saleem ya tabe baki ya fiddo wayarsa yana dannawa, Sadeeq yace "Raina min hankali take" Saleem yace "Meye abun rainin hankali" a d'an fusace Sadeeq yace "Baka ji abinda tace ba kenan, wai bata san abinda xa su yi ba a gida na biki, wato babu events da xa su yi kenan take nufi, which is a lie" Saleem ya tabe baki yace "Duk wannan xumudin da ka dinga yi kwanki kafin a saka bikin duk naga babu shi yanxu Sadeeq" Sadeeq ya rage gudun da yake yana shafa kansa a hankali bai dai ce komai ba....