Sashe 143
Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daddy na kallon ta Rasulu a hankali yace "Yanxu Baaba don Allah baxa ki bata hakuri a daura auren nan ba saboda mutanen da aka tara??" Ta Rasulu ta xaro ido ta mike tace "Toh Asabe ga Bukar nan wai in baki hakuri a daura auren... da yake dama cikin 'ya ya ma akwai mai gudun bacin ranka akwai kuma wanda bai san ciwon ka ba kwata kwata, toh Bukar dai bai san ciwon ki ba, don da ya sani sai in da karfinsa ya kare a shakiyancin da Rukayya ta mana yau" Daga haka ta shige daki murya can kasa tana cewa "Ba ruwana.... Haka kawai ince Asabe ta hakura ta ji haushi na..." Mama Hadiza na kallon su Abba on a serious note tace "Wllh Yaya tun da Inna tace baxa ayi auren nan ba fa baxa ayi ba, nima kuma dama nace baxa ayi din ba, ba kuma abinda xai sa ayi, sai an nuna ma Rukayya duk fitinar uwar mu a haka muke sonta kuma babu shegen da ya isa ya taka mana ita ya xauna lafiya, babu shi a duniya wllh, tun wuri ku kira dangin amaryar ku sanar masu an fasa don su san nayi, tunda uwata tace baxa ayi ba baxa ayi ba, ni nayi Imani da Allah da kun ji irin cin mutuncin da tayi ma Inna yau baxa ma ku tsaya kuna bin maganar a sanyi sanyi ba, kuna shakku a ran ku, me aka yi aka yi Rukayya xata raina mana uwa mu kasa daukan mataki?? to wllh yau sai ta ga iyakarta sai dai idan ban haifu ba...." Tana kai wa nan ta mike a fusace ta fice a parlon, Umma ta tabe baki ta dauke kai, Mikewa Daddy yayi ya fice daga parlon shi ma, a hankali Mujaheed ya mike ya bi bayansa, Abba ya kalli umma da kyau yace "Ki bar gidan nan as soon as possible Rukayya bana son ganin ki..." tace "Toh xan tafi ai dama ba sai ka maimaita ba yallabai, amma dai kar ka manta yar gidan wacece Mujaheed xai aura, tsaf xa ku xubar da mutuncin ku da kimar ku a idonsu, da ma duniya gaba daya, barin kai da kake sanannen Barrister" tana magana tana matsar kwalla, har xata fita sai kuma ta tafi kofar dakin Inna, Bude kofar tayi ta durkusa tana goge kwallan idonta tace "Ina neman gafaran ku inna, ku yafe ni ku yi hakuri sharrin shaidan ne..." Inna ta mike a rikice tace "Auzubillahi, garin yaya aka bar ta taxo min nan ni Asabe, don Allah ki rufa min asiri ki fita ba don hali na ba, ki tafi don Allah Rukayya" Mikewa Umma tayi ta fita parlon.... Abba da Daddy ne xaune parlon Abba duk sun rasa abun yi gashi har sha biyun rana ya kusa, fasa aure gaskiya is out of the point yanxu, bai kamata bane kwata kwata amma basu san ta inda xa su billo ma al'amarin ba, Mama Hadiza ce ta shigo parlon da sallama ta dalilin kiranta da Abba yyi, Ta nemi kujera ta xauna tana kallon yayyin nata, Murya can kasa Daddy yace "Yanxu Khadija baxa ki taimaka ki ma Inna magana ta janye wannan batu na fasa aure ba, da dai ace daga wajen mu aka fasa daurin auren nan gwara hakan ya faru daga bangaren iyayen amaryar.... Ki dubi irin mutunta gidan nan da ake amma aga irin haka ya billo daga gidan, ga mahaifin yarinyar dattijon kirki ga kuma irin manyan mutanen da xai gayyato daurin auren nan, kaninsa kuwa wajen aikinsu daya da Sadeeq kuma suna mutunci....." Mama Hadiza ta katse sa tace "Toh ko in ja Innar mu tafi gidansu amaryar tayi abinda xai sa daga wajen su suce sun fasa daurin auren tunda dama kowa kallo masifaffiya mara hakuri yake mata?" A fusace Abba yace "Ji wata maganar banxa, kina ma da hankali kuwa Hadiza?" Mama Hadiza ta mike tsam tace "Ehh kwarai Ina da hankali Yaya, dama naga take taken ku, wato ku baku ma wani ji haushin abinda aka ma mahaifiyar ku ba saboda fitinarta ko, infact ba ku ma yarda cewar ita ke da gaskiya ba, to wllh bari ku ji in har baxa ku bi abinda tace ba toh ku xa ku yi ta ganin ba dai dai ba, ba ruwana, sannan duk fitinarta xan dauketa daga gidan mu tafi sai ku xauna da matanku ku ci karanku ba babbaka, ita ma Rukayyar sai ka ce ta dawo masifaffiya ta tafi" daga haka Mama Hadiza ta fice daga parlon a fusace, Daddy ya girgiza kai yace "Bata da hankali kwata kwata" Abba ya sauke ajiyar xuciya yace "Ni fa nasan duk abinda Inna ta fada Rukayya xata iya aikatawa, kuma ko wani hukunci tace in yanke mata yayi dai dai, amma not to the extent da xata ce a fasa daurin aure ranan daurin aure, meye laifin iyayen amaryar? Ina ce Rukayya ce ta mata laifi ba su, gaskiya Inna tana son ta samu cikin wani yanayi ne, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un..." Daddy da yyi shiru yana sauraren yayan nasa yace "Ko xaka kira Bala da su Jibril su mata magana?" Abba yace "Sai kace baka santa ba ai ni har yanxu ban ga wanda ya isa ya sa Inna ta canxa ra'ayin nan ba sai dai wani Ikon Allah" Abba ya jinginar da kansa jikin kujera yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, where are we to start from coz gaskiya babu xancen fasa aure, duk hukuncin da tace ayi ma Rukayya xa ayi amma banda fasa aure don iyayen yarinya basu san hawa ba basu san sauka ba xa mu kunya ta su a idon duniya" Daddy ya tallabi chin dinsa thinking of a way out also. Karfe sha biyu Abba da Daddy da su kawu Bala da Jibril da wani kanin Inna da suke uba daya suka kara komawa bangaren Inna don su bata hakuri ta janye batun fasa auren Mujaheed da Safeenah, kora irin ta kare Inna ta masu da maficin hannunta, har kawu Bala na neman faduwa saboda saurin ya fita a parlonta, Inna ta rakosu har bakin pamponta tana huci tace "Munafukai kawai" Su dai basu juyo ba, amma daddy gaba daya ransa ya gama baci, Abba dai ne ke murmushin karfin hali, su Bala da Jibril ba bakin magana sai yan idanuwa, kanin Inna Alhaji Audu ne ya dinga cewa "Tun da muka fito lafiya Alhmdllh, Asabe ba kyau" Daddy na isa part dinsa ya shiga ko sallama bai masu ba, Imaan da Maryam na dinning xaune Imaan na bata labarin abinda ya faru parlon Inna kasa kasa, Mama Hadiza na daki tare da Ammi, Ammi ta fito jin an bude kofa ganin daddy ne tana kallonsa ta xauna saman kujera bata dai ce komai ba don Mama Hadiza fa na kan bakanta na cewa babu xancen daurin aure ranan har ta gama hada kayanta, Daddy ya jinginar da kansa da kujera yace "Inna na son bata sunan gidan nan ta kunyata mu a idon duniya ne kawai, ta mance cewa bayan Mujaheed akwai yan baya da xa su yi aure, ta mance gaba daya akwai Yan baya.... wani interpretation take son mutane suyi ma gidan nan, auren namiji ma ga abinda ya faru balle mace?? This is very serious...." Ammi dai ta kasa cewa komai sbda Mama Hadiza, Imaan ta taso ta dawo parlor don a rayuwarta na duniya bata son abinda xai 6ata ma Daddynta rai, Durkusawa tayi gefensa a hankali tace "Daddy ku yi hakuri" Daddy bai iya yace Komai ba.... Can Ya kalli agogon wrist dinsa yace "Ya Allah, just an hour remaining, Me xa mu ce ma mutanen nan fisabilillahi??" Ammi dai ba bakin magana, Mikewa Daddy yyi ya fita parlon, duk suka bi sa da kallo, Ammi ta sauke ajiyar xuciya, imaan ta mike a sanyaye ta wuce daki. Hijab dinta ta saka ta tafi part din Inna, suna xaune tare da ta Rasulu sun cika faranti da shinkafa jollof ga kaji kusan goma ana ta ci, turo baki tayi ta xauna tana kallon Inna a hankali tace "Inna don Allah ku yi hakuri ku bari ayi auren nan, kuna son a dinga ma su Abba kallon kananun mutane ne a garin nan?" Inna ta ajiye cinyar kazar dake hannunta tana kallonta baki bude tace "Shi Uban naki ne ya aiko ki in tafi in samesa yanxu?" Imaan tace "Ni ba wanda ya aiko ni" Inna na nuna mata kofa tace "Toh maxa kiyi ta kanki, tunda ba uwar ki aka xaga ba dama me xai dameki, gantalalliya ki ma je ki ji da lalurorin ki xa ki dinga tsoma baki a xancen manya kina yar yarinyar ki da ke...." A fusace Imaan ta mike ta fice a parlon, part dinsu ta koma ta shiga dakinta ta tadda Maryam a dakin, Maryam tace "Ina kika je?" Imaan ta xauna gefen gado tace "Wajen Inna mana, naje na mata magana ta xageni" Maryam tace "ke me ya kai ki, ni fa am happy gwara a fasa auren gaba daya... yarinyar da ta walakanta ni ranan farkon da muka hadu, I sooo hate her with passion" Imaan tace "Toh reputation din su Abba da Daddyna fa? Ae shine abun dubawan ba fasa auren ba" Maryam tace "It's just for sometimes dear, ke kina ga akwai wanda ya isa ya sa Inna ta canxa ra'ayin ta?" Shiru Imaan tayi, can a hankali tace "Na san me xan yi, I pray it works" Inna na bakin tap tana wanke kwanukan da suka ci abinci da ta Rasulu tana yan wakeken su shata na tale tale ta daga kai jin tafiya, Mikewa tsaye tayi tana washe baki tace "A'ahhhh sannu da xuwa Bukar, Sannu da xuwa...." Sadeeq dake sanye da tsadadden Gezna fari kal sai walkiya yake ya iso inda take yana murmushi yace "Sannu kaka, ke kam baki gajiya da aiki...." Inna ta xaro ido ta rike ha6a tace "Huuuu in gaji da aiki in mutu cikin wari Bukar, Allah ya tsareni... maxa shiga ciki gani nan tahowa na ma gama ae" Sadeeq ya cire takalmansa ya shiga parlon dake ta kamshin turaren wuta ya xauna saman lallausan rug din, Inna