Sashe 197
Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tun da Inna ta fita parlon Mujaheed ke kallon Imaan dake tsaye ta wani hade rai tana kallon bakin kofa ita a dole Inna ta tafi kiran Sadeeq a fasa kawo kaya, satan kallonsa tayi ganin ynda yake kallonta ta turo baki ta juya xata fita yyi saurin rikota yana kallon eyeballs dinta yace "Don't say anything about what happened between u and my wife to Grandma" kin cewa komai tayi ta kwace hannunta ta fice daga parlon nasa ta sakko downstairs, a nan kuma ta ji shigowarsu Abba compound din gidan da maganganun da suke yi da Inna, Inna ta dawo parlor tana girgixa kai tace "Tunda uwata ta haifeni ban ta6a ganin irin haka ba, su Ahmadu dai sun shiga uku sun lalace tirrrr, yanxu ko Mujaheed kadai bai isa ya karbi auren imaan ba, amma kawai mutane don ba shi da lafiya kuyi masa wannan rashin mutunci, to da kyar idan girman ku bai fadi a idonsa ba gaskiya" Imaan dai sai kallonta take, Inna ta xauna fuska ba annuri tace "Tirrr" Abba yyi sallama bakin kofar parlon ya shigo sannan Daddy da Kawu Audu, Gaishesu Imaan tayi Abba ya amsa yana kallonta yace "Ina Mujaheed din?" Inna ta tabe baki ta dauke kai tana girgixa kafa, Imaan xata wuce sama Abba yace "Ina matar gidan?" Inna ta kallesa da sauri tace "Wace matar gida? Matar gida da ya kora daxu, koko wata daban kake nufi?? ai tuni yace ta wuce gidansu ba wanda bai san mayya bace, daga nan dama ni dai daukansa xan yi mu koma gida ya xauna bangarena ayi ta masa magani har yayi garau" Kawu Audu da ya buda ido sosai yace "Mayya kuma Yaya?" Inna tace "Xancen kake so D'an tsut, tun fa da aka yi auren nan yau lafiya gobe ba lafiya a haka yake kamar mai laulayi, to ina dalili da raina kuma da lafiyata snn ba gantalalliya ba...." Ta kalli Imaan tace "Ke tafi ki kirasa su gane ma idonsu yanda ya koma" Daddy yace "Ni ban fahimci xancen ki ba Inna, ita matar yace ta tafi gidansu ko wa?" Inna na kallon Imaan tace "Ke tafi ki kirasa su gansa bana son dogon surutu da Bukar, don ba hankali isasshe garesa ba wllh, kuma a gaskiya kada Bukar ya sani a bakin duniya ni ba ni na koreta ba da bakinsa yace ta tafi to tunda ba ubanta ya gina masa gidan ba ba dole ta tafi ba, har Rukayya fa a nan na sameta tana masu girki a kitchen daxu..." gaba daya dai sai kallonta suke don har sannan babu wanda xai ce ya fahimci xancenta, Imaan dai ta wuce sama tayi knocking kofar parlor din Mujaheed, sai da ta kara knocking har sau biyu sannan ya bude door din bedroom dinsa, tace "Abba yana kiran ka a kasa" yana gyada kai a hankali yace "You know what Imaan??" Tana kallonsa tace "What??" Yayi wani murmushi yace "I want you to keep this at d back of ur mind... all this ur pretence and everything you are doing... Billah ranan da xan rama yana nan xuwa, I will make u regret all this you are doing in sha Allah" on a serious note ya fadi haka, ta buda ido sosai tana kallonsa da mamaki tace "Pretending kuma? What am I pretending yaya? Ni ban gane ba" yace "Bana son ki gane dama" tabe baki tayi ta juya ta bar wajen ya bi ta da kallo har ta fita sannan yyi wani murmushi. Inna na kallonsu Abba tace "Ni fa ko rantsuwa nayi da kyar inyi kaffara Ahmadu, wai ya xa ku maida ni yarinya da bata san abinda take bane, komai na fada ku karya ta ni ne?? nace maku yarinyar nan mayya ce ita ta kama min jika yake ta ciwace ciwacen da ba na Allah...." Katse ta Daddy yyi ya mike yace "Ke dai Inna ki daina haka, don Allah ki rufa mana asiri ki daina, ni fa gaskiya ba ruwana idan kika jawo wata maganar, ya xa ki dinga kiran yar mutane da mayya kai tsaye, Haba inna.... kin san wannan ba magana bace karama kuwa??" Tagumi Inna tayi a hankali tace "Naga abinda ya isheni ni patuu... Me yasa Bukar ke min haka a rayuwa" Daddy yyi yace "Ni gaskiya nake gaya maki, kiyi hakuri ki daina wannan abinda kike ba shi da amfani, duk wanda kika ji bai maki ba sai kice masa maye?? Haba don Allah, ke kin xata maita karamin abu ne, wllh ki daina haka bai kamace ki ba kwata kwata, haka kawai ki dage kina ce ma yar mutane mayya ki dauko mana wata maganar, this is very wrong wllh" Shi dai Abba kansa na kasa, Inna dai bata kuma cewa komai tayi tagumi, kawu Audu yyi kasa da murya yace "Hajiya yanxu da xa a kai maganan nan gaba...." Tsawa tayi masa tace "Kai d'an tsut ka fita harkata, idan an kai sa gaba uwaka xa ayi?? kada wanda ya sani a bakin duniya gaskiya, da kansa ya kori matarsa ni ban koreta ba...." Shiru kawu Audu yyi bai kuma cewa komai ba, Mujaheed ne ya sakko parlon cikin kananun kaya, Abba ya daga kai yana kallonsa ko kiftawa babu ganin yanda ya rame, Daddy ma kallonsa ya dinga yi da mamaki, ya karasa parlon yyi kasa da kai ya gaishesu, Daddy yace "What's wrong with Muhd?" Ya d'an yi murmushi yyi kasa da murya yace "It's just malaria amma da sauki sosai Abba" Daddy yace "Are u under medication?" ya gyada kai yace "Sure sir" Kallonsa kawai Abba ke yi shi dai ya kasa cewa komai, Daddy yace "But did you have any problem Mujaheed, wannan anya Malaria ne kadai..." Inna ta tabe baki ta mike murya can kasa tace "Har da kamun mayya ko kun ki ko kun so" daga haka ta nufi kofa fuska daure, Daddy ya bi ta da kallon gefen ido, sai bayan da ta fita parlon gaba daya Abba yace "Me ya hada ka da matar ka kace ta tafi gida??" ya shafa kai a hankali yace "Abba...." Sai kuma yyi shiru, Daddy yace "Bama son jin komai my friend, get her back immediately, am I clear??" Mujaheed ya kallesa ya kasa cewa komai da farko, can a hankali yace "In sha Allah Abba" Kawu Audu yace "Toh xa mu je asibitin ne yanxu??" Mujaheed ya kallesa yace "A'a ina amsan medication a gida kawu, ai da sauki sosai yanxu" Kawu Audu yace "Toh Allah ya kara lafiya Muhd, Allah ya yaye maka" Mujaheed yace "Ameen" Mikewa Abba yyi yace "Ka dai ji abinda aka ce maka yanxu, get her back today, sannan I want you to try all possible means of stoping ur grandma from coming to this house" murmushin karfin hali Mujaheed yayi yana kallon Abban nasa, daddy yace "That's just it" Daddy na kallon Imaan dake xaune yace "Ke kuma mai nuna mata hanyar xuwa gidan ko?" Mujaheed ya kallesa da sauri yace "A'a Abba ta san hanya ai...." Imaan ta sunkuyar da kai bata ce komai ba, Daddy yace "Toh tashi mu wuce" Mikewa tayi ta nufi kofa, Daddy yace "Allah ya kara lafiya M.A" Mujaheed yyi murmushi yace "Ameen" Abba yace "Anjima ka taho gida tare da matar taka" yace "Toh in sha Allah" Kawu Audu yace "Sai ayi ta hakuri ka ji?" Murmushi kawai yyi ya sauke kansa kasa, har bakin mota ya rakasu, Imaan ta shiga bayan motar tana kallonsa tace "Allah ya kara lafiya" ya gyada mata kai kawai bai ce komai ba, Daddy ya shiga front seat, Abba ya shiga maxaunin driver yana kallon Mujaheed yace "An kawo kudin auren kanwarka, we will talk later idan ka xo gida" A hankali Mujaheed na gyada kai yace "Toh Allah ya sanya alkhairi...." Abba yace "Ameen" Mujaheed ya kara masu sallama suka bar compound din ya juya kamar me counting steps dinsa ya koma parlor ya xauna saman kujera ya jinginar da kansa jikin kujerar ya lumshe ido yana jin xuciyarsa na masa xafi. Umma na barin gidan tare da Safeenah dama bata yarda Safeenah ta tafi gidansu ba, ta lallabata da kyar suka wuce gidan Hajiya Saude, Hajiya Saude ta sauke ajiyar xuciya bayan Umma ta koro mata duk yanda aka yi, ita dai Safeenah sai hawaye take tana jin da yau xa a mika mata wuka daga ita sai Imaan a daki babu fa abinda xai hanata ta kasheta, bata taba jin tsanar mutum kamar yanda take tsanar Imaan ba, wai a kanta Mujaheed ya daga hannu ya mareta har sau biyu, for what??? Hajiya Saude tace "Kuma har sun kawo lefen koh???" Umma na share xufar da ke keto mata cikin tashin hankali tace "Wlh muna hanya Ummi ta kirani wai ga kaya an kawo, akwatuna har sha biyu da sadaki kusan miliyan daya, ni abun duk ya kwabe min wllh" Hajiya Saude ta bude baki tana kallon Umma, can tace "Amma wannan uwar yaron anyi tsinanniya, wato hauka ta manna mana wai xa tayi shawara" Umma tayi tagumi bata ce komai ba, Hajiya Saude tace "To yanxu meye abun yi kuma??" Umma tace "Auren nan fa ko ana ha maza ha mata baxa ayi sa ba in dai ni Rukayya ina da rai, wato sun ma ci bulus kenan da uwarta idan na hakura aka yi auren" Hajiya Saude tace "Gaskiya kam gashi daga ita ba wata balle ace a hakura xuwa wani lkcn" Umma ta mata wani kallo tace "Toh ko da wasu 'ya yan an gaya maki haka nan kawai xan bar imaan ta tafi gidan da xata huta, duk fitsara da rashin kunyar da kakarta ta dinga sa wa ta dinga min ya tashi a banxa ya tafi a banxa kenan, inaaa ai sai dai idan ban haifu cikin uwata Hadiza ba, Imaan sae dai ta ji labarin jin ddin aure amma ba dai ita ta ji ba" Safeenah ta tabe baki tace "Ni dai babban damuwata ta daina xuwa min gidana gaskiya, a kanta har Mujaheed ya daga hannu ya mareni kuma ki hanani gaya ma Hajiyata" Umma tace "Haba Safeenah bai kai ki gaya ma Hajiyar Marafa ba, kin santa da xuciya ki bar