← Book details Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 292 OF 300

Sashe 292

Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

kanta ta cuta ba ni patuu ba" da mamaki Aunty tace "Me ya faru Inna?" Hawaye cike idon Inna tace "Yanxu sbda rashin tsoron Allah Amina sai da yarinyar nan ta amince da wannan mutumi har ya kai ta ya baro babu kayan aure, cikin d'an mutum ne da ita fa Amina, wllh tllh danyen ciki ne shataf da ita, ni naga yarinya tayi wani haske kamar danyen nama, sai kirji da suka cicciko, to sai kuma ga amai naga ta kirba daxu a bandaki daga tayi ido hudu da tuwo, yanxu kuma daga uwar ta kawo mata danwake da mai da yaji ta kai loma biyu baki sai amai shaaaa duk karni, kaiiii Amina lallai sai dai a kyale yaran yanxu, amma ba a ta6a kunyata ni irin yanda Imaan ta kunyata ni ba yau" Aunty dai sai kokarin danne Dariyarta take tace "Haba Inna, yarinya da mijinta kuma...." A fusace Inna tace "Ke dalla rufe min baki, Mujaheed ne har xa a kira miji, dama jira kawai yake yyi mata ciki ashe ni ban sani ba, ita kuma jarababbiya kawai, oh oh toh ba ruwana ya xo ya tattara ta ya mayar da ita gidansu su je can su karata da aman su ba da ni ba xa ayi wannan gagarumin kazantar ko 'yar cikina Hadiza lkcn da take da cikin d'an ta na farko ban amince ta xauna da ni ba sbda amai da yawu balle wa ennan kareren, duk kawai a bata min gida da k'arnin aman ciki, Aa wllh duk inda yake ya xo ya dauketa ko kuma uwarta ta maida ta bangarensu suje can su karata wllh wllh ba ruwana, ba dani ba, duka duka yaushe aka yi auren har ta yadda da shi ciki ya shiga idan ba fitina ba" Aunty ta fita dakin tana girgixa kai tana murmushi, Ammi dai ta gama gyara mata jikinta a bandaki ta fito da ita dakin tana rike da hannunta Inna ta basu hanya da sauri fuska daure, Ammi ta fita dakin, ta dau cooler din danwaken suka bar parlon ta wuce part dinta da yar ta.
Chapter 292 · 0% Book details