Sashe 218
Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mikewa Inna tayi ta shige daki tana cewa "Ni dai ba ruwana, kiyi tafiyar ki ke kadai amma bbu inda imaan xata je, kawai Allah ya rufa mana asiri mu kuma mu ki rufa ma kanmu?? kaji min mata dai" Ta Rasulu na kallon Ammi tace "Haba Shatu, ke ma fa Mujaheed din nan d'an ki ne, ko yana da wani mugun hali ne wanda ke kika sani ba mu sani ba??" Inna ta leko daga daki tace "Ina fa ta Rasulu kawai samun waje irin na bafillatani, mai mugun hali ai a bayyan 'yar ta imaan yake, ni wllh sai ince ma cutar Mujaheed aka yi da aka hada sa da Imaan bayan ga matarsa Safara'u, Imaan fa ko girki bana jin ta iya, banda Mujaheed din wanene xai iya da ita, kuma daga an rufa ma juna asiri sai ki nemi ki tona mana, ni dai ba ruwana kiyi ta kanki Aisha, ko kinfi Ahmadu da Bukar sanin abinda suke ne, kawai mata kina nema ki lalata mana xumuncin mu sbda rashin tsoron Allah" Mikewa Ammi tayi ta fice daga parlon, Inna ta rike ha6a tace "Yau naga bafillatana dai..." Ta Rasulu ta tabe baki tace "Ni dai ban taba ganin irin wannan xumunci ba tunda uwata mai salati ta haifeni, gida duk ya rikice daga hada aure na xumunci" Inna tace "Wllh idan xuciya ta debeni sai in iya ce ma Mujaheed ya ki sakinta mu ga ta tsiya, idan an bi komai a hankali kuma Allah ya dora mu kansa ai sai ya saketa tunda a gaskiya Imaan ta fi karfin sa sai irin su Bulasawan dama, amma mata kya xo kice min xa ki tafi da Imaan...." Ammi na komawa part dinsu ta shiga dakinta ta sa Hijab ta dau purse ta fito ta bude dakin Imaan, Mama Hadiza ce xaune dakin ta rungume Imaan dake kuka kamar ranta xai fita cikin tashin hankali take cewa "Yayana ne shi fa Mama, ya xa ayi ace wai an daura mana aure da yaya, wayyo na shiga uku mama dama Yaya na auren kanwarsa?? don Allah ki gaya ma su Abba Yaya na ne, wllh ni dai yayana ne...." Mama Hadiza ta kasa ce mata komai, jin har jikinta ya dau xafi sosai ta dago kanta tana kallonta fuska daure tace "Wato ban isa ince kiyi shiru kiyi ba koh?" Maryam dai na xaune dakin tayi tagumi, Maimoon sai hawaye take duk jikinta a sanyaye tana kallon Imaan da duk ta fice hayyacinta, Mama Hadiza ta sake Imaan ganin Ammi ta mike ta fita daga dakin, Ammi ta karasa cikin dakin tana kallon 'yar tata tace "Dauko Hijab din ki" tashi Imaan tayi ta dau hijab dinta tana shessheka tace "Ammi plsss kice ma Daddy su yi hakuri wllh yayana ne shi, ba aure tsakanin mu, don Allah kar su ce sun daura mana aure" Fixgo hannunta Ammi tayi suka fita daga dakin trying hard to control her tears, Imaan ta dinga bin ta tana kuka sosai har suka fito compound dake cike da jama'ah sai dai fa duk an hada groups ana kananun surutai tunda har sannan ba a fito ance ga abinda ke faruwa ba a gidan, sun dai ga families din na ta kai komo bbu annuri, mutane dai dai ne yanxu basu san an fasa auren Imaan da d'an gidan Bulasawa ba, sai dai duk bbu wanda yasan an daura auren da Mujaheed, Safeenah ce tsaye rike da plate din abinci ta cika uban nama tana kallon Mama Hansai dake ma wasu yan uwanta da wasu mutane dake xaune sun hada group bayanin abinda ke faruwa fa a gidan, duk aka saki baki ana kallonta, tana girgixa kai tace "Toh Yaya Ahmadu na ganin haka sai kawai ya daura auren da d'an sa tunda an riga an tara jama'ah kada a ji kunya, shine fa hankalin kowa ke tashe a gidan, kusan dai bbu wanda yyi na'am da auren nan da aka hada...." Hajiya Bari'a kawar Aunty dake wajen ita ma a xaune ta ce "Wani d'an nasa a ciki, shi angon ko kuwa??" Mama Hansai ta tabe baki tace "Kila da da angon ma aka auran da duk matsalolin dake faruwa yanxu bai faru ba, da d'an ita Hajiya Rukayya aka daura auren, wato dai Mujaheed....." Safeenah dake tsaye tana ta saurarenta ta sake plate din hannunta a hankali, lkci daya ta fixgo Mama Hansai tana gwalo kwala kwalan idonta tace "Wani Mujaheed din????" Mama Hansai ta juya da sauri tana kallonta don bata ma san ita ce matar Mujaheed ba, Cikin yanayi na tashin hnkli da rikicewa Safeenah ta dinga jijjigata tana cewa "Wani Mujaheed din kike nufi, ki gaya min wani Mujaheed? mijina aka daura ma aure da Imaan din???" Mama Hansai dai sai xaro ido take ta kasa cewa komai, Safeenah ta saketa a hankali tana tariyo reaction din Umma daxu da irin gigicewan dake tare da ita har da fita waje babu hijab, da kuma Mujaheed da ya fito parlon mahaifinsa hawaye a idonsa, wani karan da ya tsorata mutanen compound din Safeenah ta saki da karfi, dai dai fitowar Ammi da Imaan, Safeenah na hada ido da Imaan dake kuka Ammi na rike da hannunta ta sulale wajen sumammiya, duk aka yo kanta ana salati masu debo ruwa na debowa, masu fiffita nayi, Ammi dai tuni ta ja Imaan suka fice compound din gaba daya.... Gidan Gwaggwo Ammi ta wuce tare da Imaan, parlor suka tadda gwaggwo suna jimami da yan uwanta biyu a parlon, Ammi ta gaisheta da mutanen parlon ta wuce ciki Imaan ta na biye da ita kanta a kasa, Gwaggwo ta bi su da kallo can ta mike ta bi bayansu, gefen gado ta tadda Ammi a xaune tayi tagumi, Imaan kuma ta kwanta kan gadon tana kuka a hankali, Gwaggwo ta xauna kan carpet dake shimfide dakin tace "Toh me kuma ku ka xo yi nan Aisha ko baku yarda da kaddara bane? Komai bawa ya ga a rayuwa fa rubutattce ne daga Allah, dama can Allah ya rubuta Sadeeq ba mijin Fatima bane, abun da ciwo amma hakuri kawai duk xa mu yi, daxun nan Muhsin ya bar gidan nan shi ma duk abun ya damesa gashi ko sanin inda Sadeeq din yake bai yi ba wayoyinsa ma duk a kashe wai, ni ban taba xaton haka daga Sadeeq ba, ko me ya samesa haka Allah ma fi sani, amma gaskiya wannan ba lafiya ba ranan daurin aure ka xo kace ka fasa ba laifin tsaye balle na xaune, ban taba ganin haka a xuri'ar mu ba... Na kuma samu labarin hadin da yayan mijin ki yayi Allah ubangiji ya sa hakan shine mafi alkhairi, ai matar mutum kabarinsa...." Ammi ta katse ta tace "Alkhairi fa kika ce Gwaggwo, wllh auren nan ba alkhairi babu alamarsa, in dai basu sakar min 'ya ta ba barin garin nan xan yi da ita, Allah baxai taba sa 'ya ta ta hada jini da irin Rukayya ba, bana fatan haka kuma in sha Allahu hakan baxai ta6a faruwa ba...." Gwaggwo ta bude baki tana kallon Ammi da mamaki, can tace "To ai baki da iko da 'yar su Aisha, ke har xa ki bude baki kiyi wannan mummunan furucin kin mance halaccin uban yaron nan, gaskiya ban san ki da mance alkhairi da rike sharri ba, Ina ce saboda ke Ahmadu har sakin Rukayya sai da yyi wanda sai da tafi shekara uku bata gidan, ko don ubansa ke kya bude baki kiyi wannan furucin Ammi, meye aibun Mujaheed yaro mai hankali da nutsuwa to wllh ni ko ranan laraba sai da ya shigo gidan nan gaisheni, da kyar ayi wata daya ko sau daya bai shigo min ba, kaji min Aisha dai, 6ata masu xumunci kike son yi ko me? Ke dai ba kawai kiyi ma yar ki addu'a da fatan alkhairi da xaman lafiya gidan mijinta ba tunda ga yanda abubuwa suka kasance, da Rukayya Fatima xata xauna ko Mujaheed? Haba Aisha sai kace ba matsayin uwa kike gare Mujaheed ba, gaskiya banji dadin rashin hankalin nan naki ba, daga ubansa yyi kokarin fidda ke da mijin ki kunya sai ki rufe ido ki nuna masu ke baki da hankali baki da kirki??" Ammi ta girgixa kai tana murmushin takaici tace "Dama ba lallai kowa ya gane abinda nake nufi ba ba kuma lallai kowa ya ga abinda nake hangowa ba, Rukayya ta wuce tunanin ku gwaggwo, wllh Rukayya...." Katse ta gwaggwo tayi ta mike tace "Toh sai ki mayar masu da 'yar su ki dawo mu xauna ba shikenan ba, ai bamu da iko da ita, maida ta ki kwaso kayan ki mu xauna nan tunda ke shashahsa ce..." Daga haka ta fice daga dakin. Duk kiran da Abba ya dinga yi ma Mujaheed layinsa gaba daya a kashe suke, daga karshe gidan nasa kawai Abba ya wuce nan mai gadi ya sanar masa bbu kowa a gidan, yayi reverse kenan xai bar layin kiran Daddy ya shigo wayarsa, da kamar baxai daga ba sai kuma ya daga, Daddy yace "Kana Ina Barrister?" Abba yace "Ina hanya" Daddy ya fada masa eatry da yake son su hadu a lkcn don bbu inda xa su xauna su ke6e su yi magana, Abba yace "Alright" kusan a tare suka isa eatry din, Daddy ya sa waitress ta kawo masu just table water, Abba ya bude ruwan ya sha kusan rabi sannan ya ajiye sauran, Daddy na kallonsa yace "First of all I will like to say I am sorry Barrister, duk da dai you misunderstood me amma ina mai baka hakuri still, ko kadan Barrister Auren Imaan da Mujaheed da ka hada ba wai ban yi farin ciki da hadin naka bane, abun farin ciki ne sosai don ko bbu komai mun kara karfafa xumuncin mu, babban damuwata a auren nan shine mahaifiyar mu... nasan baxata ta6a na'am da hadin ba, Dole xata yi maganganu da bai kamata ba a kan mu, sannan Barrister bamu san ko shi Mujaheed din xai yi na'am da auren ba, we don't know ko yana da ra'ayin mata biyu, infact duka duka yaushe yyi auren ba, beside bai ta6a fitowa ya nuna yana son Imaan ba banda