Sashe 283
Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin rauni Safeenah tace "Haba Mujaheed, why don't you want to listen to me? Why ain't you picking my call bayan kuma kace xaka kira baka kira ba, you don't know why I am....." Imaan dake sauraronta ta katse tace "Ke dakata... What business do you have with my husband again?" Shiru Safeenah tayi jin muryarta, a mugun fusace tace "Uban me yasa xa ki daga wayata, ke na kira da xa ki daga min wayar mijina?" Imaan tayi wani dariya tace "Ehh lallai yanxu na sake confirming cewar ke babbar mahaukaciya ce, kuma kinyi mugun nisa a hauka, shi Mujaheed din ne mijin ki??" Dariya Imaan ta kara yi sannan tace "Toh bari ki ji in gaya maki, ko a mafarki da kyar ki ga Mujaheed a matsayin mijin ki, Mujaheed yyi maki nisa sosai, sai dai ki ajiye a tarihi kin ta6a auren Mujaheed, and let me drop u this last warning, keep from my husband Safeenah kike ko wa?? Wllh ki fita hanyar mijina, even by mistake kada ki sake kiransa don bashi da wani alaka da gantalalla mai tunanin dabbobi irin ki, tun ban nuna maki wacece ni ba maza maza ki goge number mijina daga shegen wayar, wahalalliya kawai mara xuciya, dama can mijin aro kika aura sai a ci gaba da zawarci kuma...." Safeenah bata yadda hawayen da ke sakko mata ya hanata fashewa da dariya ba tace "Ai kuwa ni ke da alaka da mujaheed fiye da kowa... don kuwa a yanxu haka ina dauke da cikin d'an sa ko yar sa, kin gane abinda nake nufi or you need more elaboration?" Imaan da taji wani diff ta bude ido sosai jin abinda tace, shock da taji bai hanata cewa "Ki nemo uban cikinbki amma ba mijina ba, karya kike wllh banxa kawai jahila, ke da Mujaheed bari in sake gaya maki wllh sai dai hange, shi ma daga nesa nesa, Allah ubangiji ya raba sa hada xuri'a da watsatsun tambadaddun family irin naku, duk sharrin ku da kulle kullen ku kuma a kan ku xai kare, xan ga kuma ta inda xa ki sake kiran mijina jaka kawai mahaukaciya" daga haka Imaan ta katse kiran ta danna mata block ta kunna data ta hau WhatsApp can ma ta danna mata block sannan ta goge lambarta gaba daya a wayar tana huci, xata ajiye wayar ta ji muryar Mujaheed a bayanta yace "Toh sannu! give me my phone" ta bude ido sosai sai dai bata juyo ba, yace "I said give me my phone Imaan" lkci daya ta juyo fuska a murtuke tana kallonsa tace "Baxan bayar ba, or do you have any business with the useless lady da xata dinga kiran ka a waya kana biye mata, har ta cancanci ka sake daga kiranta bayan abinda tayi ma mahaifiyar ka?? Ko har ka mance ne? Or is it because you didn't watch the scene? To ba ruwana wllh baxan yadda ba, kuma xan gaya ka da Abba...." karasawa yyi xai dau wayarsa ta dauke a fusace ta fice daga dakin kamar xata tashi sama ya bi ta da kallo, Imaan na komawa dakinta ta ji wani takaicin da bata san lkcn da ta fashe da kuka ba, ta rufe fuskarta da pillow, Lkci daya tayi tsit ta daure fuska jin budewar kofa, muryarsa taji yace "But did you know u just shouted at me Imaan?" Banxa tayi masa bata dago ba, ya karasa kan gadon yace "Imaan" tashi tayi a fusace xata bar wajen ya fixgota, ta fara buge hannunsa tace "Ni ka kyaleni, leave me alone" ya matse ta jikinsa yace "Listen to me now, bana son kina min magana haka, you don't know why I answered her call and I don't think you have the right to call her, sure Safeenah raised her hands on my mum amma na tabbatar wannan kuskure ne kin kuma san irin xuciya ta Imaan, i don't keep anybody in mind..." Katse sa imaan tayi tace "Ehh nasan kalan xuciyar ka amma ban san kalan yanda ka ba ma addinin ka muhimmanci ba, ban san irin fahimtar da ka ma addinin ka ba, ban san ko kasan illar tarayyar ka da mahaukaciyar ba tunda dama ita nasan jahila ce ba sani tayi ba" yyi gripping dinta da karfi yace "Ke xaki koyar da ni addini na? Do you have to? Are you thinking kin fini sanin addini ne? Safeenah is carrying my child so I have to listen to her no matter what, it's my responsibility or ain't you aware of that religious lady?" kasa cewa komai Imaan tayi tana kallonsa ko kiftawa babu, ya saketa yana kallon wani direction din, can ya juyo ya jawota xata kwace kanta ya kankameta giving her a romantic kiss all over her neck, wasu hawaye suka dinga sakko mata tana son kwacewa amma ba rikon wasa yyi mata ba, murya can kasa yace "I have to listen to her for the Kamar daxu hot romance ya shiga mata amma wannan karan she didn't even respond, bata kuma sake jiki ba, har lkcn kuma hawaye take har da shessheka, hakan yasa ya kyaleta yyi kwanciyarsa ya juya mata baya, tun bayan aurenta da Mujaheed yau shine karo na biyu da Sadeeq ya fado mata, tasan Sadeeq baxai ta6a mata haka ba, he will never, dama kuma Mujaheed ai bai ce yana sonta ba kawai aura masa ita aka yi, dole ya nuna mata muhimmanci Safeenah gareta, tunanin hakan yasa ta fashe da kuka sosai shi dai bai ce mata komai ba. Daren ranan gaba daya Imaan ta kasa bacci, karfe biyu saura ta mike ta shiga bandaki ta dauro alwala ta fito ta fara sllh, sai uku saura taji bacci ya fara damunta tayi kwanciyarta nan saman darduman, haka yasa Mujaheed ya mike ya kashe Ac dake aiki a dakin ya koma yyi kwanciyarsa, daga nan kuma bacci ya dauketa. Da asuba bude kofar dakin da yyi ya farkar da ita, tana ji ya koma dakinsa bayan wani lkci ya fito ya wuce masallaci. ko da ya dawo sllh ya tadda ta tana yi, ya xauna gefen gado har ta idar, ta mike ta dauka qur'ani ta koma kan darduman ta xauna, duk yana bin ta da kallo ta gefen ido, ta fara karatun ta, bayan wani lkci ya mike ya fice daga dakin. Sai da gari ya fara washewa Imaan ta mike ta ajiye qur'ani ta dauke darduma ta fita dakin a hankali, bude kofar parlonsa tayi making sure bata yi making sound ba ta karasa kofar dakinsa da bai rufe ba gaba daya ta tsaya, waya ta ji yana yi calmly, sosai gabanta ya fadi tana sauraren abinda yake cewa, "What did you mean Safeenah, sure i will take care of you, I will take care of my child u are carrying, after that ba wani abu kuma..." Abinda Imaan taji ya fada kenan, da mamaki ta ji yace "Auren kisan wuta kuma?? Did you even know what you are saying?" Imaan taji gabanta yyi mugun faduwa taji ta ma kasa tsayuwa bakin kofar, mikewa mujaheed yyi yana kallon kofar jin motsi da sauri ta matsa ta jingina da bango, ya karaso bakin kofar ya bude suka yi ido hudu ta wani daure fuska, yace "We will talk later" daga haka ya katse wayar yana kallonta yace "Why do you derive joy intruding in my affairs imaan? gari ya waye common ki bude baki ki gaida mijin ki baki iya ba amma kin iya kishi da saka masa ido, do you have any problem? Meye amfanin kishin naki?" Kallonsa kawai Imaan take bbu ko kiftawa, yace "Bana son kina saka min ido a abinda nake yi, and I don't think it's necessary ki dinga shigo min nan da safe ba gaisheni kika xo yi ba..." juyawa imaan tayi ta nufi kofa ta fice daga parlon ta wuce dakinta, ita kanta tayi mugun mamakin yanda ta dake xuciyarta, ta cire kayan jikinta ta tafi bathroom kawai ta wanke baki ta hada ruwan wanka tayi ta daura towel ta wanke bandakin ta fito, sai bayan da ta gama shiryawa ta feshe jikinta da turare sannan ta gyara dakinta ta kunna turaren wuta. Tana goge goge a parlor Mujaheed ya sakko cikin shiri sai xuba kamshi yake, yana kallonta yace "What will you take for breakfast Imaan?" Ba tare da ta kallesa ba tace "I will sort that out" kofa ya nufa ta bi sa da kallon gefen ido har ya fita gidan ta ji fitar motarsa gaba daya. Sai a sannan wasu hawaye suka dinga sakko mata ta dinga jin wani xafi a ranta, tayi kukanta mai isarta ta gama goge gogen da take ta wuce sama ta kwanta, har sha daya bata fito daki ba balle ta nemi abinda xata ci gaba daya taji yunwar ma bata ji. Da rana tana kitchen ta na dafa indomie ta ji shigowar motarsa gidan, tana ji ya shigo parlor sannan ya karaso kitchen jin kamshin dahuwar da take yi, yana tsaye bakin kofar yana kallonta daga sama har kasa don skirt ne karami jikinta sai riga yace "Kin yi breakfast din?" Tace "Nayi" yace "Ohk ga lunch na kawo maki and you are cooking, amarya bata girki ai" Bata ce komai ba ya juya ya fita, har ta fito daga kitchen yana xaune parlor, ta wuce sama rike da plate din abincinta, kasa cin indomie din ta yi ta sha five alive da ta debo kadan ta tura abincin gefe tana jin wani xafi da xuciyarta ke yi mata, bayan wani lkci ta mike ta fitar da plate din har lkcn yana parlor xaune ya bi ta da kallo ta shiga kitchen ta fito ta koma sama, bata kuma sake fitowa ba har Magrib. Bayan Isha tana tsaye gaban press sanye da hijab har kasa xata fito da kayan bacci da xata sa Mujaheed ya shigo dakin, ko kallon direction dinsa bata yi ba ta ci gaba da ciro sleeping dress dinta, ya kulle kofa ya karaso ya ajiye ledan hannunsa yace "Ga abinci" shiru bata ce masa komai ba ya isa bayanta ya jawota jikinsa murya can kasa yace "Ni kike sharewa ko??" Bai jira cewarta ba ya fara daga