Sashe 287
Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
lafta min yaji plss" yace "Alryt" tace "Sai ka hado min da Hollandia milk with shawarma kila in ci" yace "Naji" daga haka ya katse wayar. Ya kalli Imaan dake kallon window yace "Sweet let get her what she want before going home" shiru tayi masa bata ce komai ba, ya kamo hannunta a hnkli, sae a sannan tace "Ohk" duk sai da Mujaheed ya siya ma Safeenah abubuwan da ta lissafa masa sannan ya tafi gidansu, yana isa kofar gida ya kira wayarta, bayan ta daga yace "I am outside ki turo a amsar maki kayan" ya ajiye wayar yana kallon Imaan da ta jinginar da kanta da kujera, Bude gate aka yi sai ga Safeenah ta fito daga gidan sanye da hijab har kasa, kallonta imaan ta dinga yi ta jikin glass sbda hasken fitulu ne ta ko Ina a kofar gidan nasu, ba karamin ramewa tayi ba sai idanuwa, Mujaheed na ganin ta fito ya bude motar xai fita ita kuma ta bude side din Imaan suka yi ido hudu, da sauri Safeenah ta juya coz bata ta6a tunanin tare suke ba, Imaan kuma ta dauke kai, Mujaheed ya xaga ya mika mata ledan hannunsa yace "How are you feeling?" Ta amsa ta gaishe sa a hankali, yace "Allah ya kara lafiya, sai da safe" daga haka ya xaga ya bude front seat ya shiga ya ja motar ta bi sa da kallo. Gaba daya daren ranan Mujaheed bai gane kan Imaan ba, abincin ma ta ki ci, ta ki yarda kuma ya ta6a ta, a haka ya kyaleta yyi kwanciyarsa amma ya kasa bacci, can cikin dare bayan tayi bacci ya jawota jikinsa ya rungume, a haka ya samu yyi bacci. Sai da ta dau kusan sati taki sake masa taki yarda ya ta6a ta, duk ya daga hankalinsa ba kadan ba don just for two days da suka yi tare ta basa hadin kai ya ji baxai ta6a iya nisantarta ba, mamakin irin kishinta yake it's just too much, bai san ana kishi haka ba don ko lkcn da Safeenah take kishi da Imaan tun bata ma san xai aureta ba da ya fara aika mata sakkoni shkkn sai kuma wani lkcn, haka nan bai gaji ba ya dinga lallabata don Imaan na da baiwar da ba ko wace mace ke da shi ba, she's totally different from a lot... Tana linke hijab bayan ta idar da la'asar ya shigo dakin, dawowarsa aiki kenan, ta dauke kai ta ajiye darduman, kamota yyi cikin lallami ya marairaice mata yace "Haba imaan, why are you doing this to me?" Ta hade rai tace "Me na yi?" Ya xaunar da ita gefen gado ya xauna yace "Don Allah kiyi hakuri, me yasa xa ki dinga kishi da Safeenah that's not my wife, she's not my wife any longer, kuma babu aure tsakanina da ita, it's just my responsibility to take care of her and her baby har ta haihu, so kike Allah yayi fushi da ni sweet?" Imaan ta fashe da kuka tace "Toh dole sai ka dinga xuwa wajenta, tayi ta gilla ma karya xata ci wannan xata ci wancan duk don kaje ta dinga ganin ka" Sosai ta basa dariya ya rungumeta sosai yace "Toh daga yanxu baxan sake xuwa in je ta gan ni ba I promise you, if she need anything xan bada a kai mata in sha Allah, idan kuma ta haihu sai mu amso babyn mu, shkkn bbu kuma abinda ya hada ni da ita" cikin rawar murya tace "Ba wani nan ai ba tare muke fita kullum ba balle in san ko ka je ko baka je ba, kuma ni nasan cikin karya...." Rufe bakinta yyi da nasa ya lumshe ido, nan ya shiga lallashin lil sis din tasa yanda ya kamata. Kiran sllhn Magrib yasa Mujaheed ya bude ido a hankali yana kallon Imaan da ta makalkalesa, murmushi yyi yana shafa kanta ya kai bakinsa kunnenta murya can kasa yace "It's time for prayer, sweet...." A hankali ta bude idanuwanta tana kallonsa ta turo baki tace "Stop calling me sweet" ya lumshe ido yace "Billah ke sweet dita ce" Ranan Saturday da safe har Mujaheed ya gama abinda yake a laptop imaan bacci take duk da ko azkar bata yi ba after subhi prayer ta koma baccin, ya kalli agogo ganin karfe goma saura ya mike ya wuce dakinta, xaunawa yyi gefenta ya kai hannu fuskarta ta bude ido tana kallonsa yace "Ni da kika hana bacci ban yi baccin safe har war haka ba sai ke koh?" Ta turo baki ta mirgina ta mike xaune tana mitsika ido, yyi murmushi yace "Xa mu fita yau fa, and I told you yesterday" a hankali tace "Toh" ya mike ya fita dakin, cikin riga da skirt na atamfa super imaan ta shirya ta shafa powder fuskarta sannan ta dau gogaggen hijab dinta har kasa color din supern jikinta ta saka ta feshe jikinta da turare tana yamutse fuska ta fita, shayi kawai ta sha bata ci bread ba, Mujaheed da ya shirya cikin kananun kaya shi ma ya mike ya dau makullin motarsa ya kama hannunta yace "Toh mu je" Sai da suka hau saman titi ya kalleta yace "Zaria xa mu fara xuwa sai mu tafi can gida ko?" A hankali tace "Toh" ko da wasa bai yarda imaan ta lura da takardan scan din Safeenah da ya kai mota tun tuni ya ajiye inda baxa ta gani ba, har suka kama hanyar Zaria bacci imaan take, ganin yanda ta takure gu daya ya kashe ac din motar, suna isa gidan yyi parking a hankali ya ja hancinta cikin cool voice dinsa yace "Sweet...." bude lumsassun idonta tayi ta kallesa, ya dinga kallonta sannan yyi murmushi yace "Mun kawo..." ta fara kalle kalle, ya sauka motar ba tare da ya dau envelope din ba ya xagayo ya bude mata side dinta, sosai sisters dinsa dake gidan har lkcn basu koma kaduna ba suka ji dadin ganinsa, babu wanda ya wani considering din Imaan sai Seeyama da ta xo gidan ranan ita ma, Imaan ta xauna saman kujera ta sunkuyar da kanta bayan sun gaisa da Seeyama, daga sama Umma ta sauka ta shigo parlon tana kallon Mujaheed tace "Sannu da xuwa" yace "Yauwa sannu umma" Imaan ta sauko kasa a hankali tace "Ina yini Umma" umma ta kalleta tace "Lafiya lau ya gida?" Imaan bata dago ba still tace "Alhmdllh" Umma ta kalli Mujaheed dake gaisheta shi ma ta amsa ta xauna tana tambayarsa ya aiki, yace "Alhmdllh Umma, ya gida fa" tace "Lafiya lau, sannun ku da xuwa" Seeyama ce ta mike ta wuce kitchen ta dauko masu ruwa da lemo, ita kam har yau shiru ko 6ari bata yi ba, kana ganinta kasan tana tare da damuwa sosai don duk ta rame, ta fito kitchen ta ajiye ma Mujaheed lemo da ruwan, sannan ta kai ma Imaan nata, Imaan ta kalleta tace "Nagode" Seeyama tayi murmushi ta tafi ta xauna. Mikewa Umma tayi ta wuce sama Mujaheed ya bi ta da kallo, Ummi na kallon Seeyama tace "Aunty Seeyama mu je mu gama girkin toh" mikewa Seeyama tayi ta bi bayanta xuwa kitchen, Rahma ma ta tafi ta ci gaba da wanke wanken da take, sae a sannan ya mike ya tafi kitchen don cin uban kannin nasa. Bacci imaan ta dinga ji amma ta ki kwanciya, ta dai jinginar da kanta da kujera ta lumshe ido, bayan kusan minti biyar ta bude ido da sauri jin abu na taso mata ta dalilin aroma dake fitowa daga kitchen, mikewa tayi ta rufe bakinta ta rasa inda xata, Seeyama da fitowarta kenan tare da Mujaheed tace "Subhanallah me ya faru" kofa Imaan ta nufa xata fita compound kafin ta isa kofar aman ya taho mata, lkci daya ta xube wajen ta dinga kwarara amai, Seeyama ta isa kusa da ita da sauri ta durkusa ta riketa tace "Sannu Imaan, baki da lafiya ne?? Sannu" Mujaheed ya kasa karasawa ya tsaya yana kallonta ganin umma dake sakkowa downstairs ita ma tana kallon imaan, Umma ta karasa gun su tace "Subhanallah, Me ya faru Seeyama?" Cike da damuwa Seeyama tace "Amai take yi" Umma na kallon Imaan tace "Sannu" Kasa cewa komai Imaan tayi wani aman na taso mata, Umma ta dagota sai ga shi ta fara kwararo wani aman, hakan yasa Mujaheed ya taho wajensu, Seeyama ta tafi debo ruwa da sauri, Umma dai sannu kawai take mata, sai da aman ya tsaya mata sannan Umma ta nufi sama da ita Mujaheed ya bi su da kallo.