← Book details Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 208 OF 300

Sashe 208

Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali Imaan ke tafiya tana kallon Sadeeq da har ya kusa gate sbda saurin da yake, kafin ta fita kofar gida har ya shiga motarsa ya wuce, ta bi motar da kallo sannan ta juya a sanyaye ta koma part din inna, Mama Hadiza dai har lkcn ta ki sake fuska don ba karamin 6ata mata rai abinda Imaan tayi yyi ba, tana shigowa parlon kuwa ta dinga hararanta fuska daure, Imaan na ganin haka ta sunkuyar da kai ta wuce bedroom din Inna duk jikinta yyi sanyi, Inna ta bi ta da kallo sai kuma ta kalli Mama Hadiza tace "Toh ba shikenan ba har ta sallamesa ta dawo, amma kina neman maida karamar magana babba sbda rashin tsoron Allah, ai shi Sadeeq din ya fi kowa sanin tsakaninsu da Mujaheed, kuma yaro ne mai hankali da natsuwa, tunda nake ban taba ganin yaro natsatstse irin sa ba, gashi kwata kwata abun sa bai rufe masa ido ba, kyauta yake kamar bai san ciwon dukiyar ba, to bayan ni har ku ma baxa ku huta ba aka ce maki Hadiza??" Ita dai Mama Hadiza bata ce komai ba tayi tagumi, Inna ta tabe baki tace "Ni dai ba ruwana... A dinga kyakkyawan xato domin Allah, sai kace warce ta fada kan wani kato can a titi, wannan ae yayanta ne Mujaheed" Mujaheed ya mike yana kallon Mama Hadiza yace "Toh na gaishe ki Mama Allah ya huce gajiya sai na shigo gobe" Inna na kallonsa tace "Amma kai dai Allah ya xuba maka shegen rowa Mujaheed kamar uwarka, banda haka ina laifin ka riko mata Yar gasasshen kazar nan da yar lemo... ka wani shigo gansansan daga kai sai kai, inda Isuhu ya fi ka kenan gaskiya" Mujaheed dai bai tanka ta ba ya nufi kofa, tace "Toh nayi magana daxu baka ce komai ba, ina fa da labarin abinda kayi ma Seeyama lkcn bikinta, to ita Imaan ko don ba ubanku daya ba, naga har yanxu shiru baka yunkuro ba, kyansa dama kawai ka bata kudin ni nasan abinda xan mata da shi, kar ka siya mata komai ba abinda Ahmadu da Bukar basu yi mata ba, kudin xai fi mata amfani gaskiya" ya juya ya kalleta yace "In xan bata abu ae ba sai kin sani ba Hajiya, sai kace mahaifiyarta bata kusa....." Daga haka ya fice daga parlon Inna ta rike ha6a tana kallon Mama Hadiza tace "Ke me yake nufi kenan? Kaddai baxai ma yar uwarsa komai ba bikinta sukutum da guda?? To bari dai in xuba ma saurautar Allah ido, amma wllh in har Mujaheed bai bada gudunmawa mai kauri bikin Imaan ba lalacewa ta samesa duniya da lahira, kuma ban san da wani idon xai kalli ubanta ba" Washegari laraba da safe driver ya ajiye su Imaan saloon, Mai wajen da kanta tayi mata gyaran bayan ta gano amarya to be ce, Banda kallonta babu abinda ake yi a saloon din, don gaba daya she looks so new, tayi wani haske da fresh sai glowing ko ina na jikinta yake kamar balarabiya, dubu ashirin Abba ya basu na gyaran gashin su uku don Ummi da Rahma basu yarda sun biyo su ba, da kyar Maryam ta lallaba Imaan ta yarda ayi mata kitso a gashinta, imaan har ta mance rabon da tayi kitso, haka aka ta daure aka rangada mata kitsonta kanana mai kyau, sai kusan azahar suka kira driver ya xo ya maida su gida. Sosai gida ya cika da jama'ah na kusa da nesa duk da sai Juma'ah ne bikin amma kai kana ganin jama'ahn gidan kasan only child ce xa ayi ma aure, kuma ga biki ya hade biyu, gaba daya yan uwan Ammi suna gidan, daga su har 'ya yansu, Aunty ma duk yan uwanta na kusa da nesa sun iso, Bakin ciki kamar xai kashe Umma, kwata kwata taki yarda ta fito daga dakinta har da sa makulli daga ciki abun duniya ya taru ya mata yawa, anya auren nan baxa ayi sa ba kuwa?? Tambayar da ta dinga yi ma kanta kenan, wata xuciyar na assuring dinta baxa ayi ba ta xuba ido kawai. Su Imaan na komawa gida da awa daya mai lallin da Aunty ta kira ta xo gida yi mata lalle, Inna ta gama xuba ma imaan pepper soup din da Aunty ta aiko mata da abinci kenan mai lallin ta shigo tare da Maimoon, Maimoon tace "Inna mai lalli ce" Inna ta kalli mai lallin da damuwa tace "Naga jaraba, ko abinci fa bata ci ba kika xo lalle baiwar Allah.... Tun safe take garari a titi wai gyaran gashi ynxu kuma daga ta fito wanka na xuba mata abinci sai ki xo kice kin xo lalle baiwar Allah, ba fa ta ci komai ba" Mama Hadiza dake parlon ta kalli mai lallin tace "D'an yi hakuri ta ci abinci yanxu ta gama Aunty..." Mai lallin tace "Toh xan jirata a waje" daga haka ta fita, Inna ta harari Mama Hadiza ta gefen ido ta dau abinci ta tafi daki kai ma Imaan tana cewa "Abu dai munafurci munafurci ba a son fadin gaskiya, na ma mata maganar gaskiya kin kwantar da murya kina mata magana salon ta min kallon fitinanna" Imaan ta gama saka kaya kenan Inna ta shigo tace "Ki ci abincin ki a nutse kafin ki fito wani shegen lalli, ba ruwana da gantalewa, ko lallaba maki lallen bana yi da kaina ba cikin dare" daga haka Inna ta juya ta fita. Maryam na kallon Imaan dake tsakuran abincin da Inna ta ajiye mata tace "Ki bani number Sadeeq in kirasa ai shi ya kamata ya baki kudin lalle da kitso ba su Abba ba" Imaan ta kalleta, sai kuma tayi murmushi tace "A'a just leave him... There is no need ai Abba riga ya bada" Maryam tace "Like seriously tun xuwan mu kasar nan ban ga ya kiraki ba Imaan, there is something wrong somewhere bai kamata kiyi shiru ba gashi jibi daurin aure ki cuci kanki" Imaan ta tabe baki tace "Am not saying anything Maryam, kika san uxurinsa" Maryam tayi shiru tana kallonta da mamaki, Imaan ta mike ta rufe abincin don gaba daya ta kasa ci, tun last week tayi loosing appetite dinta gaba daya, a hankali Maryam tace "Baki ci komai ba a abincin Imaan" Imaan tace "Mai lallen tana ta jirana, anjima xan ci" daga haka ta fita dakin, Maryam ta bi ta da kallo, bayan few minutes ta dau wayarta ta shiga duba number Sadeeq, tana gani tayi dialing, har ya gama ring bai dauka ba, ta sake kira nan ma bai daga ba, kwashe lambar tayi a nata wayar ta ajiye ta mike ta shiga gyara ma Inna daki, tana gamawa ta dawo ta xauna ta dau nata wayar tayi dialing number din Sadeeq, ba a dau lkci yana ring ba ya daga, shiru tayi da farko sai kuma tayi masa sallama, ya amsa, tace "Sadeeq?" Yace "Yes..." tace "Why the sudden change of attitude toward ur financee Sadeeq?" Ya d'an yi shiru kafin yace "Wait! Who is this?" Tace "You answer my question first..." Yace "I don't think you are in the rightful place to..." A d'an fusace tace "Kar ka gaya min magana malama, wato kai a silly thought dinka ka riga da ka sameta xaka fara walakantata tun bata shiga gidanka ba ko?? to wllh karya kake Imaan ta fi karfin haka, you are mistaken malam, domin ka kawo sadaki kuma jibi daurin aure ba yana nufin har ta xama taka ba...." Ya katse ta shi ma yace "Toh ki ce mata tayi xuciya ta gaya ma iyayenta ta fasa auren kawai, sai su maido min da sadakina.... I think this will be better than you calling and saying nonsense on phone to me madam" daga haka ya katse wayar, Maryam ta dinga kallon wayar da mugun mamaki nan ko xuciyarta cike yake da tantamar anya Sadeeq din da ta sani ne wannan, Anya Sadeeq din da ya siya mata latest phone da take mafarkin mallaka kwanaki da suka xo Nigeria kawai don tayi masa addu'ar Allah ya bar sa da Imaan ne wannan, mikewa tayi very shock ta fita dakin, a parlor ta tadda imaan mai lalli na mata lallin, Inna ta matsar da kujerunta gaba daya ta lullube su, ta kwashe carpet dinta kada a goga mata lalli a cuceta kamar yanda tace, Xaunawa Maryam tayi tana kallon Imaan, lkci daya taji tausayinta ba kadan ba ya kamata, kawai mikewa tayi ta fice daga parlon daga karshe.... Sai kusan Magrib Imaan ta wanke lallenta da yyi kyau ba kadan ba ta tafi part din su dauko Hijab don Inna ta wanke mata gaba daya wanda ta taho da, Shirye shiryen Mothers day da xa ayi gobe kawai ake yi a gidan, bata ga kowa part din su ba ta wuce daki ta dauko hijab ta fito, Muryar Maryam taji tace "Imaan" da sauri ta kalli direction da taji muryata ta ganta xaune ita kadai a dinning, karasawa tayi tana kallonta tace "Me yasa kika ce baxa ki yi lallen ba?" A takaice Maryam tace "Nothing" Imaan tace "Amma fa jiya kince xa ki yi" Maryam tace "Fasawa nayi, xauna mu yi magana Imaan" Imaan ta ja kujera ta xauna tana kallonta, Maryam ta d'an yi shiru sai kuma tayi kasa da murya tace "You know what imaan?" Imaan ta girgixa mata kai gabanta na faduwa, Maryam tace "Plss ina son ku xauna da Inna kiyi mata magana yanda xata fahimce ki, ki ce mata don Allah tayi ma su Abba magana a daga bikin nan xuwa wani lkci" Kallonta kawai imaan ke yi, Maryam ta girgixa kai tace "This is not the Sadeeq you know before imaan, ki rufa ma kanki asiri ki yi ma Inna bayani ita kadai xata iya ma su Abba magana su daga bikin nan, wllh idan kika auri wannan Sadeeq din you are going to live a miserable life in his home, gaba daya gadara yake yana ganin ya gama samun ki, dama boye maki real him yyi tun farko, kinsan yanda muka yi da shi a waya daxu da na kira in ji dalilin Change of attitude dinsa?" Imaan da
Chapter 208 · 0% Book details