← Book details Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 300

Sashe 107

Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*The book Imaan is not free, you read for free ur cup of coffee*🤷🏻‍♀️

It's 300 via Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp digit 07087865788 to be included in the payment group.

Umma ce ta shigo parlon da sallama, su Ummi da Rahma da Maimoon suka xauna kan kujera Inna ta kalli Umma sannan ta kalli akwatunan tace "Lafiya Rukayya?" Umma ta xauna kan lallausan rug din parlon tace "Ina yini inna?" Inna tace "Cewa nayi meye wannan, daga ina??" Hajiya Balaraba da Hajiya Saude dake tsaye su ma sun shigo parlon suka gaisheta, Inna ta xauna kan kujera a fusace tace "Oh oh Allah, ni da ban yini ba xa ku gan ni, akwatunan meye wannan ake shigo min parlor dasu?" Hajiya Balaraba tace "Na lefe da xa a kai ne" Inna ta xaro ido tace "Lefen wa?" Hajiya Saude dake d'an tabe baki tace "Wacce Mujaheed xai aura..." Inna tace "Wani Mujaheed din?" Shiru duk suka yi basu bata amsa ba, Inna ta dinga sakin salati a jere, can tace "Yanxu Mujaheed aure xai yi ban sani ba sai dai inga akwatuna ana kokuwan shigo min da su ace min xa a kai lefe? Yanxu Rukayya mancewa kika yi ni na haifi Uban Mujaheed? Ehh lallai Ikon Allah ya fi gaban haka" daukar waya tayi ta mika ma Umma tace "Kira min d'an nawa.." Umma da ta daure fuska ta karbi wayar tayi dialing number Abba ta mika mata, Inna ta karba ta kai kunne, Abba na daga wa Inna tace "Yanxu Ahmadu ko ba raina kai ba mai ambatan sunana bane kace.... Allah sarki Inna, gashi Allah yayi lkcn auran Mujaheed baki a doron kasa balle ki sa albarka ke ma, Amma duk da haka muna maki fatan rahaman Allah... balle da raina da lafiyata Ahmadu?? wai sai dai inga katuwar matar ka na shigo min da jakunkuna tace min xa su kai lefe, yanxu ko shi Mujaheed din da nayi bauta da shi yana tsumma na cancanci yaki fadi min xa a kai lefensa sai dai inji a duniya? Wayyoo duniya Ina xa ki damu...." Bata jira cewar Abba ba ta katse wayar ta jefar kan kujera ta fashe da kuka tace "Oh oh Allah, duniya dai ba gaskiya, mutane basa jin tsoron Allah..." Hajiya Saude tace "Hajiya ba fa kai kayan xa ayi ba yanxu, kawai dai an gama hada kayan ne aka ce bari a xo a nuna maki, Amma ko gaisuwa ma ba a kai ga kai ma iyayen yarinyar ba tukun" Inna ta daga kai ta kalleta tace "Ai Rukayyar nan da kike gani ba mutum bace, idan uwarta ce Hadiza xata mata haka, Ina ce ranan da xa a fara hada kayan lefen ya kamata ta tako ta xo ta sameni tace to Inna gashi gashi, amma da yake xuciyarta ba tsoron Allah ban ganta ba, ni dai ba ruwana, kowa yyi da kyau.. kansa, bari kuma Ahmadun ya shigo in ji ko shi yace a boye min har sai an gama hada lefen" tana fadin haka ta Mike tana kakkabe kujerunta, mikewa Umma tayi tana kallon kawayenta da su Ummi tace "Ku kwasa mu je" Inna ta juyo da sauri tace "A kwashi me?? Ai ba ke kika min wahala da Mujaheed din ba, kuma da kyar idan ba da ni xa a kai lefen ba ma, don haka kada warce ta taba jakunkunan nan duk kuyi ta kanku ku fita ku bar min parlona in goge, nakudar Mujaheed kawai kika yi da haihuwarsa amma ni na masa abinda ya fi wannan, irin wahalar da nayi da shi ba sai dai Allah ya saka min ya biya ni ba, kuma shima Mujaheed din xai shigo ya sameni, idan bai ma yi hankali ba ma sai ince na bar sa da Allah..." tsayawa Umma tayi tana kallonta bacin rai karara fuskarta, tuni su Hajiya Saude suka fice a parlon, Ummi da su Maimoon suka bi bayanta, Inna ta juya tana kallon Umma tace "Ki fita don Allah xan goge daudar da ku ka shigo min da shi Rukayya" juyawa Umma tayi ta fice, Tsaye ta tadda kawayenta suna jiranta, Hajiya Saude tace "Amma gaskiya Hajiya Rukayya kina fama, yanxu haka kike xaune da wannan bala'eyyiyar tsohuwar nan har yau? Har yanxu kin rasa yanda xa ayi da ita ne?" Umma ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Ku bari kawai, yanxu ina tanka ta abinda xata tsara ma d'an ta daban, shi kuma duk hakurinsa kika kuskura kika taba masa mahaifiya to babu xaman lafiya ranan, shi sa nake mata shiru" Hajiya Balaraba tace "Ke ma dai wllh, toh kin kasa yin komai a kanta ne?" Umma tace "So nawa kuma, sai dai Allah ya kyauta kawai, Amma wannan matar da ku ka gani ku kyaleta haka kawai" Hajiya Saude tace "A'a baki dai yi abinda ya dace bane, nima fa haka uwar mijina take a da amma ba yanxu ba kuma wllh, duk da nata bai kai na tsohuwar nan ba ma, Amma wllh ynxu sai labari, gaba daya gidan sai yanda nace ake yi, ina xan iya wahala??" Umma tace "Toh mu je ciki sai inji ya xa muyi, wllh na gaji, ita ce babban matsalata a gidan nan" Hajiya Balaraba tace "Toh kayan da ta hana fitowa da su fa?" Umma tace "Kayan xa su dawo hannuna in sha Allah, Mujaheed ne kadai ya isa ya fiddo da kayan daga parlon nan ko ubansa bai isa ba, kuma shi xan sa bari dai ya dawo" Hajiya Saude tace "Toh yaushe xa a tafi kai gaisuwar ne?" Umma tace "Uban cewa yyi sai kaninsa ya dawo Abuja, ae tuni na rufe bakinsa shi ma, komai nace cewa yake tohh" Duk suka kwashe da dariya suka shiga cikin gidan. Da magrib Imaan taje kai ma Inna abinci ta dinga kallon akwatunan da Inna ta jera a parlonta gwanin ban sha'awa, Inna ta shafe addu'an da take tace "In fiddo maki sabuwar wayar taki ne yanxu" Imaan tace "Inna wannan akwatunan fa?" Inna ta tabe baki tace "Daxu wannan mata Rukayya suka shigo da su wai ashe har xa a kai ma Mujaheed lefe bani da labari, Ina nan xaune kamar fanko" Imaan ta xaro ido tace "Aure xai yi Inna?" Inna tace "Ai shine nake jira Ahmadu ya dawo mu ji idan bola aka maida ni a gidan nan ban sani ba" Imaan da har sannan ke kallon akwatunan da surprise tace "Waow wllh sun yi kyau sosai, yanxu gidansu Aunty farida xa a kai kenan" Inna tace "Toh wacece dama banda ita, duk da dai iyayenta yaku bayi ne yarinyar na da hankali kuma ban jin xata gaji da ni idan na koma gidan Mujaheed da xama, lafiya xa mu xauna da yarinyar, ke kuma duk sati sai ki dinga xuwa kafin lkcn naki da bulasawa yayi" Imaan ta fara dariya ta xauna Inna tace "Toh bude mu ga tsiyar da suka xuba mata" Imaan na murmushi ta dinga sauko da akwatunan, sannan ta bude daya daga manyan ciki, xannuwa ne tsadaddu kwance a ciki, Imaan ta dinga fiddo su tana ajiyewa Inna na dauka tana duba kasan xannuwan don ganin ko babba ne ko karami, can ta tabe baki tace "Kin san Rukayya akwai shegen karya, ko sata xata iya sa Mujaheed yyi don tayi fafa, Toh xannuwa dai gasu duk masu tsada sai a xo a fidda min nawa da na takwarata a ciki" Imaan dai bata ce komai ba sai murmushi kawai take, ta bude wani akwatun, ta shiga fiddo laces masu suna lace, Inna ta rike ha6a tace "Ehh lallai Rukayya makaryaciya ce, wnn ai sai ta talauta min jika, Toh wannan ma sai a fidda min daya inyi doguwar riga, idan kyalle ya rage in baki a maki joni" Imaan dai bata ce komai ba ta bude akwatuna mai dauke da jallabiyoyi tsadaddu, Inna tace "Ki xabi wanda ya maki a ciki...." Imaan ta xaro ido tace "Innaa?" Inna ta hade rai tace "Toh sai su fidda min in baki" Akwatin dake dauke da takalma da jaka Inna ta bude, ta fiddo wani takalmi mai kyau sosai tana kallon imaan tace "Gwada wannan mu ga" imaan ta wani xaro ido a fusace Inna tace "Don Allah ki gwada" mikewa Imaan tayi xata sa takalmin aka bude kofar parlon Mujaheed ya shigo da sallama.

Afuwan it's short, gobe da safe xan yi update in sha Allah, I was kinda busy gaba daya yau ne. Tnxx.

Imaan isn't free, it's 300 via Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah.
Chapter 107 · 0% Book details