← Book details Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 144 OF 300

Sashe 144

Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

ta shigo tace "Bari in kawo maka abincin bikin da aka fasa, ai ko yayi dadi har da na fitina, yana nan ta Rasulu ta jido mana har da nama ba iyaka, ni dai hakorana har ciwo suka fara yi saboda cin kaji, yanxu ma ta Rasulun ta shiga wanka ne..." Yana murmushin sa mai kyau yace "Kaka ni a koshe nake wllh kuma lkcn Juma'ah ya kusa sauran yan mintuna..." Inna tace "Toh yi maxa ka tafi idan an sakko sai ka dawo" Yana shafa kansa yace "Ehh xan tafi yanxu kaka...." Tace "Toh ko in dauko maka darduma, jiya na wanke sa tasss nasa Maimoon ta goge min na feshe sa da turare" yar dariya yyi yace "A'a kaka Ina da darduma a mota, xauna mu yi magana" Inna ta dawo da sauri ta xauna tace "Toh gani Bukar, in ji lafiya dai???" Yayi sunkuyar da kai yace "Na ji abinda ya faru ne daxu...." Bai kai aya ba Inna ta fashe da kuka tana kunce ha6ar xaninta cikin rawar murya tace "Wllh abinda ya faru kenan Bukar shine yasa nace baxa a daura auren ba, ba ruwana, yanxu haka an fasa duk nasa a sallami bakin da suka xo" Sadeeq yyi kasa da murya a hankali yace "Don Allah kaka kiyi hakuri, kinga su Abba da Daddy baxa su ji dadin kallon da jama'ah xa su masu ba, gashi ana ganin mutuncin gidan nan, babba dama shi da hakuri aka san sa, kuma wanda aka cuta shi ake ba hakuri dama..." da sauri Inna tace "Inaaa Bukar ai tuni an fasa daurin auren...." Yace "A'a na fa ce kiyi hakuri kaka, kuma ni dai na san ki da hakuri... Ke babba ce fa Kaka" shiru Inna tayi tana matsar kwalla, can tace "Wllh ni dai kunyar ka nake ji Bukar" Yana murmushi yace "Toh don Allah ki janye batun fasa auren" Inna ta d'an yi shiru, can tace "Toh ai shikenan, sun ma kansu ni dai ba ruwana, kuma na hakura aje a daura auren" Murmushi sosai Sadeeq yayi yace "Yauwa Kaka Allah ya kara girma, na ji dadi sosai da kika dau shawarata, Allah ya kara girma" Inna tace "Toh ai dama meye amfanin babban da bai daukan shawara, hakuri kuma ai Allahn da ya halicce mu ma hakuri yake da mu balle ni, na hakura wllh, ga waya sai ka kira min Bukar uban Imaan dama ya fi saka abun a kai uwa kanwar uwarsa ce amaryar, oho dai kirasa ince masa su je su daura auren hankalin su ya kwanta" Yana murmushi ya amshi wayar yayi searching sunan da tace anyi mata Saving lambar daddy da shi ya kira sannan ya mika mata, Daddy na dauka tace "Toh ni dai ba ruwana Allah ma hakuri yake damu, ku je ku daura auren ni na hakura Allah ya saka min da alkhairi" bata jira cewar daddy ba ta katse wayar, Inna ta kalli Sadeeq tace "Ni Rukayyar ma bata taba min irin haka ba gaskiya, ban dai san shaidanin da ya makale a xuciyarta ba yau, amma dai gaskiya tatattce ne d'an iska, ya cuceta ba kadan ba yau, nace to ko radion da suka kunna ya cika gida ne yasa shaidanin ya samu nasarar rudar ta, amma gaskiya ni bata tanka ni kwata kwata a gidan nan, kuma har xaunawa take idan xata gaisheni, shi kuma Ahmadu sarkin xuciya har ya yanke hukuncin ta tafi gida, ni sai ta ban tausayi ma wllh...." Sadeeq dai sai kallonta yake yana murmushi yace "A dai yi hakuri kaka" tace "Atohh, biyayya iya biyayya dai suna min ni baxan masu sharri ba...." Daddy ne ya shigo parlon tare da Abba da kawu Bala, Inna na washe baki tace "Sannun ku da xuwa" Sadeeq ya gaishe su gaba daya da ladabi, Inna tace "Toh gaskiya duk babban da yace baxai dinga daukan shawaran yaro ba yayi asara, me yyi min xafi da xan bari inyi asara, wannan yaro Sadeeq dai ya shigo ya ban baki kuma wllh na hakura aje a daura auren Allah ya sa albarka, kamar daga sama ya fado min yanxun nan, wato har labarin ya baxu duniya Kai jama'ah.... Kuma da kun san ta yanda xa ku bi da ni da xancen bai yi tsayi ba haka ba duk baku da wayo, ni dai na yafe, aje a daura auren" Abba ya d'an yi murmushi yace "Toh madallah mun gode Inna, Allah ya kara girma, xa mu je masallaci ynxu lkci ya kusa" Inna tace "Toh ku tafi Allah maku albarka, Bukari kai ka dawo in xuba maka abinci don Allah har da kaji xuka xuka" Sadeeq na murmushi ya mike yace "Toh in sha Allah xan dawo" Bin bayan su Daddy yyi ya fita, Abba na kallon Sadeeq yace "Maa Sha Allah, I am very happy at ur contribution Allah ya saka" Sadeeq yyi murmushi bai ce komai ba, a haka suka fita gidan Abba na kiran wayar Mujaheed, Mujaheed was so shock da ya ji wai ai Inna ta hakura, kuma wai Sadeeq Bulasawa ne ya bata hakuri, har reaction dinsa ya ba Abbansa da Daddy mamaki, haka dai suka wuce mosque ana sakkowa masallaci kuma aka daura auren Mujaheed Ahmad da Safeenah Usman, ko jira Mujaheed bai yi su gaisa da abokansa da suka taho daga nisa ba ya koma gida, direct part din Inna ya nufa, Imaan na tahowa daga part din innar rike da warmer xata sha corner suka kusa cin karo da shi, fixgota yyi wanda hakan yasa ta saki abincin hannunta a tsorace, yana mata wani mugun kallo da idanuwansa da suka rine cikin tsawan da ya raxana ta yace "Uban wa ya aikeki ki sa saurayin ki yaje ya ma Inna magana? Uban wa ya sa ki????"
Chapter 144 · 0% Book details