Sashe 254
Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Murmushi Imaan tayi ta rufe fuskarta jikin Farida a hankali tace "A'a akwai mana Aunty" Farida ta dinga kallonta kafin tace "Toh kuwa idan kika tsaya jin kunya kishiyar ki xata kwace maki Yaya kina ji kina gani" Imaan ta dago tana Kallonta, Farida tace "Kwarai kuwa, kunyar me xa ki ji kuma bayan kun riga da kun xama daya yanxu" Imaan kamar xata yi kuka tace "Wllh Aunty kunyarsa ni dai nake ji ban san ya xan yi ba" duk da ta ba Farida dariya, Farida ta daure fuska tace "Kunya bayan ya riga ya kwana dakin ki?" Imaan ta girgixa kai tace "A'a ni bai taba kwana daki na ba" Farida tace "Kika ce kwanan ki nawa da tarewa yanxu?" Imaan ta buda ido sosai tace "Aunty jiya fa muka xo nan garin" Farida tayi shiru sannan tace "Kuma bai kwana dakin ki ba?" A hankali Imaan tace "Ehh kila dakin matarsa ya kwana jiya, don daxu da safe ta shigo tana ce min wai bata ta6a ganin amaryar da miji bai kwana dakinta ba ranan farko sai dakin uwar gidansa, har tana ce min mijin wata na aura, kuma mijin wata mijin aro ne" da mamaki Farida ta dinga kallonta, can tace "Toh shi me ya hanasa kwana dakin na ki?" Imaan ta tabe baki tace "Ni nasan sbda jiya da muka hadu da ke a mall nace maki hutu na xo gun matarsa, shine da ya shigo da daddare yace min to xai tafi wajen matarsa ni kuma ban ce masa komai ba har ya fita..." Farida tayi murmushi tace "Toh ki maida hankalin ki imaan, idan ba haka ba kuwa you will regret it duk da ban san kishiyar nan taki ba ga dukkan alama makira ce, kuma Mujaheed da na sani dai baxai taba kwana dakinta yasan ba ranan ta bane, Mujaheed yana da addini sosai ya san me yake, sai dai idan ya canxa ne daga yanda na san sa a da, yanxu ki bude kunnuwan ki sosai ki ji abubuwan da xan gaya maki, idan kuma ki ka ki aiki da su toh kina tare da dana sani wanda ba shi da amfani, ko tantama babu ke Mujaheed ya fara so kafin first wife dinsa, that is if yana ma sonta kenan.... Imaan if I am not mistaken babu abinda ya shiga tsakanin ki da Mujaheed har yanxu koh?" Imaan ta sunkuyar da kai bata ce komai ba, Farida tayi murmushi tace "Toh ki saurari duk abinda xan gaya maki yanxu...." a hankali Imaan ta kalleta tace "Toh" Farida bata fito bedroom dinta ba sai kusan sha biyu na rana shi ma don Imaan tace mata yunwa take ji bata yi breakfast ba shine ta fito hada mata breakfast, Har lkcn Mujaheed na parlor tare da Dr Khaleel da bai gajiya da labari, shi dai gaba daya hankalinsa yyi kan Imaan sanin bata yi breakfast ba har lkcn, Farida tayi murmushi tana kallonsu tace "Sannun ku da hutawa" Mujaheed na kallonta yace "You tell imaan lkci ya wuce fa, this is after 12" Farida tace "Haba nan da bayan azahar ba sai ku wuce ba Dr, ni ban gaji da ganin kanwata ba, kayi wucewarka kawai anjima xa mu maida ta gida...." Dr Khaleel na kallon Mujaheed yace "Ba yini ku ka xo yi mana ba dama Dr?" Mujaheed yyi murmushi yace "Xa mu yi bak'i ne daga kaduna, suna ma hanya yanxu" Farida dai bata tanka sa ba ta shiga kitchen, eggs ta soya ma Imaan, ta hada mata shayi mai kauri, ta debar mata pepper soup din da tayi da safe sannan ta dau bread duk ta daura su kan tray ta fito kitchen din, ganin abinda ke hannun Farida hankalin Mujaheed ya kwanta don shi damuwarsa kenan dama, daki Farida ta kai mata abincin ta ajiye saman carpet, Imaan ta sakko kasa, Farida tace "Bari inje in daura white rice, nayi stew daxu da safe" Imaan tace "Toh" daga haka Farida ta fita dakin, a hankali Imaan ke shan shayin hannunta, da ta tuna wasu daga abubuwan da Farida ta gaya mata sai tayi murmushi ita kadai, wani kuma ta turo baki, wani kuma idan ta tuna a ranta tace tabdi, da tuna wai Safeenah xata iya kwace Yaya ya daina kulata sai ta hade rai, shayi kadai ta shanye cikin abubuwan da Farida ta kawo mata, sannan ta mike ta dau tray din ta fita don kai wa kitchen, tunda ta fito Mujaheed ke kallonta, suna hada ido ta sunkuyar da kai ta karasa cikin kitchen din ta ajiye tray din, Farida dake wanke wanke tace "Toh baki ci egg din da yawa ba ai Imaan" Imaan tace "Aunty na koshi wllh" Farida tace "Toh nasan Mujaheed xai ce xa ku wuce yanxu, ki tafi daki ki harhada duk abinda na baki a leda, kin xo da jaka ai?" Imaan ta girgixa mata kai, Farida tace "Ohk toh ki tafi dakin ina xuwa yanxu" Imaan na fitowa parlor suka kara hada ido da Mujaheed da ya mike tare da mijin Farida xa su wuce masallaci don lkcin sllh yayi, Yana kallonta yace "After prayer xa mu wuce" ba tare da ta kallesa ba tace "Toh" sannan ta wuce ciki, ba a dau lkci ba Farida ta shigo dakin, daya daga sabbin jakanta na aure ta ciro ta kwashe gaba daya kayan da ta debar ma Imaan ta xuba a ciki tace "Hope you remember all what I said??" a hankali Imaan ta gyada mata kai, Farida tace "In sha Allah may be next tomorrow xan xo gidan naku kin ji?" Imaan ta marairaice tace "Aunty me yasa baxa ki xo gobe ba?" Farida tayi murmushi tace "A'a gwara dai jibin, in sha Allah xan xo kanwata" Imaan tace "Toh Allah ya kai mu, Aunty ban xo da Hijabs dina daga gida ba, did you have hijab to give me in dinga sllh da shi, am having just this one I am wearing" Farida tace "Ohk" mikewa tayi ta bude daya daga akwatunanta ta fiddo sabon hijab a leda tace "Sai dai bai kai kasa ba nasan ke har kasa kike sa wa" Imaan tayi murmushi tace "Nagode Aunty bari in yi sllh kafin ya dawo...." daga haka ta mike ta shiga bayi don dauro alwala. Sai karfe daya Imaan suka bar gidansu Farida bayan Farida da mijinta sun rakosu har bakin mota, a back seat Imaan ta ajiye warmer din abincin da Farida ta tilasta mata sai ta tafi da shi sannan ta bude front seat ta shiga, Mujaheed ya kara sallama da Dr khaleel ya ja motar, Imaan na daga ma Farida hannu, sai da suka hau saman titi ya kalli jakar hannunta yace "Jakar meye Wannan?" Ta turo baki tace "Ta bani kyauta ne, ta ga ban xo da jaka ba" murmushi yayi bai ce komai ba, bayan few minutes yace "Idan kika gama haifa min yara na sai in maki lefen ki ko?" ko kallonsa bata yi ba ita dai tana rungume da jakar hannunta don Farida tace mata kada ta yarda ya ga abinda ke ciki, Sai da suka kusan gida Mujaheed yace "Ammi fa tana gida, ta xo" Imaan ta kallesa da sauri tace "Ammi?? Da gaske Yaya?" Yace "Ehh" murna ta fara yi kamar yar yarinya a motar, ganin murmushin da yake ta dakatar da murnar ta marairaice tace "Don Allah Yaya kace min wllh don ni ban yadda ba, kila ba da gaske kake ba" shi dai murmushi kawai yake, lkci daya ta daure fuska, yace "Toh Ammi baxa ta iya xuwa ganin ki ba kenan" turo baki tayi tace "Nasan Ammina baxa ta iya xuwa ba" yace "Why?" Tace "Ni dai nasan she can't" yace "Toh idan muka je kika ganta me xan maki?" Ta kallesa da sauri sai kuma tayi murmushi tace "Idan muka je naga da gaske ta xo xan baka dubu goma" ya gyada kai still smiling yace "Idan kuma ba mu ganta ba fa?" Ta turo baki tace "Sai ka siya min waya" ya wara ido yace "Uhn???" Tace "Ehh" yyi murmushi yace "Toh ban yadda ba dubu goma da kika ce yyi kadan" tace "Toh me xan baka?" Ya shafa kansa yace "Dubu goma with kiss and hug" Ta wara ido, sai kuma ta rufe fuska tace "Toh naji" yace "Kin ji kika ce fa?" A hankali tace "Ehh" Yana murmushi yace "In dai muka je muka ga yan gida ai duk daya ne koh?" Ta girgixa kai da sauri tace "Noo, ni dai Ammina nace" parking yyi kofar gida ya kashe motar ya sauka ita ma ta fito tana rike da jakarta, ta bude back seat ta dau warmer din abinci bata ko kalli takeaways da yyi masu da safe ba ta nufi gate, shi ya kwashe ledojin ya rufe motar sannan ya bi bayanta, still Imaan tayi ganin motar gidansu a compound din, ta juya ta kalli Mujaheed dake tahowa yana murmushi, lkci daya ta nufi cikin gidan da sauri ta bude kofa, sai kuma ta tsaya tana kallon Mama Hadixa da Inna dake parlon, Mujaheed ya bude kofar shi ma ya shigo, imaan ta ajiye warmer din hannunta ta nufi Mama Hadixa dake murmushi ta fada jikinta cike da farin ciki tace "Oyoyo Mama, yaushe ku ka xo" Mama Hadiza ta rungumeta tace "Daga ina ku ke?" Imaan na washe baki tace "Mun fita ne Mama, yaya ya kai ni gun Aunty Farida, kin tuna ta?" Mama Hadiza tace "Nan take aure ita ma?" Imaan ta gyada kai tana murmushi tace "Ehh Mama" Mama Hadiza tace "Maa sha Allah, amma kina cin abinci kuwa daughter naga kin rame" Imaan ta sunkuyar da kanta tana murmushi, ita dai Inna na xaune fuska a murtuke ta kura ma Tv ido, Mujaheed na murmushi ya karasa parlon ya ajiye ledan hannunsa ya xauna kusa da ita ya mata side hug yace "Nasan dai wajena kika xo koh inna?" Inna tace "Toh dama wajen wa xan xo idan ba kai ba Mujaheed, ga damun nama can cikin cooler na maka" Dariya ya fara yi yana kallonta, Imaan ta daga kai daga kwance da tayi jikin Mama Hadiza ta kalli Inna, mikewa tayi ta dawo kusa da