← Book details Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 264 OF 300

Sashe 264

Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

wancan Malamin da walakancin da xa ki saka min kenan??" Umma ta mike tace "Don Allah Saude ki fita kiyi tafiyar ki nima a yanxu da kika gan ni wllh ta kaina nake matsalata ta fi naki wllh wllh..." Hajiya Saude tayi wani murmushi tace "Toh nagode kwarai Rukayya xan tafi, amma ki sani wllh kema sai kin girbe abinda kika shuka, duk ta'asa da barnar da kika dinga aikatawa xaki gansu a kwaryar ki kwanan nan, wannan da ya sameki shi ake ce ma wasa farin girki" daga haka Hajiya Saude ta fice daga dakin kamar xata tashi sama tana goge hawayenta. Daren ranan Imaan na parlon Inna xaune idonta a kan tv dake aiki sai dai bata san abinda ake yi ba gaba daya hankalinta baya tare da ita, Inna kuma tana can bakin tap tana aikin gurje gurjenta har ta gama ta shigo ta fara kakkabe kujerunta tana kallon Imaan tace "Ae yarinya jibi akwai fasa mugayen bama bamai xa ayi a gidan nan, iyaka dai bam din ya tarwatsa wa enda xai tarwatsa mu kuma muyi ta kanmu mu kara rike Allah, ke kuma Alhmdllh yanda wannan mutumi Mujaheed ya dauke ki haka ya maido min ke sbda tsayuwar dare da na dinga yi, abinda na nasani a nan gaskiya shine in har Mujaheed bai fita hakkin ki na aure ba wllh wllh babu inda xa ki bi sa, in su Ahmadu sun mutu to ni suma nayi, ba da ni xa ayi wannan ta6arar da abun kunyar ba, ko ya ta6a shigar maki daki ya kwana ne??" Imaan dai sai kallon tv take, Inna ta yi mata tsawa tace "Keee..." Da sauri Imaan ta juya ta kalleta, Inna tace "Toh wllh Bukar kika share ba ni ba, kwana biyu da baki gidan nan bakina tsit bbu shegen da ya sa ni magana, to dama wake sani maganan banda ke da Mujaheed din...." A fusace Imaan tace "Toh wai ni nasan da ni kike ne" Sai kuma ta rufe fuskarta da kujera ta fara kuka ta mike ta shige daki da sauri, Inna ta tabe baki tace "Toh ni ina ruwana idan ya kai ki ya baro ki, duk da baxan ma yadda hakan ya faru ba tunda ba ubansa ya halitto min ke ba, haka kawai ya same ki a banxa, to shi ne banxa ba ke ba" Imaan ta kwanta saman gado tana turo baki a hankali tace "Ko Ina ruwanta ma..." Bayan few minutes ta jawo wayar Inna dake saman gadon ta dinga kallon wayar sannan tayi dialing number din Mujaheed, sai da ya kusa katsewa ya daga kamar xata yi kuka tace "Yaya Ina ka tafi yau?" A hankali yace "Anjima xan dawo, where are you?" Tace "Ina part din Inna" d'an murmushi yayi yace "Are you missing me?" Da sauri tace "A'a fa, kawai naga ban ganka bane, kuma ban san ko ka ci abinci ba..." Yana murmushi yace "Toh xan shigo yanxu, me xan kawo maki?" Rufe fuska tayi a hankali tace "Kaza mana" Muryar inna taji tace "Yau naga jarababbiyar mata, shi Mujaheed din kika kira da katin wayata?? Toh gaskiya sai dai in bar ki da Allah don ba Mujaheed ya saka min katin ba, ba kuma uban Mujaheed ya saka min ba Bukar ne ya sa min kafin ya wuce, wannan wani irin jaraba ce ni patuu? Uwar me kika hada da Mujaheed din xa ki kira sa a wayata, ni dai na shiga uku da wahalar ki" imaan ta katse wayar ta jefar kan gado ta juya mata baya fuska daure, Inna ta dauke wayarta tace "Waye kuma Mujaheed da xaki kirasa da wayata muguwa kawai..." Daga haka ta fice daga dakin. Imaan na ta kwance daki taji an bude kofar parlon Inna, mikewa xaune tayi tana kallon kofar dakin.
Chapter 264 · 0% Book details