← Book details Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 300

Sashe 86

Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

kofa ya fita. Da Magrib imaan ta tafi kai ma inna abinci bayan ta sake boye wayar Mujaheed da kyau, duk kiran da aka dinga masa na Farida kawai ta daga, tun da ta fito compound dama gabanta ke faduwa, da sauri sauri ta karasa part din Inna, Yusuf ta gani xaune, ta wara ido ta ajiye abincin hannunta tace "Lahh ya Yusuf yaushe ku ka dawo?" Ya kalleta ya d'an yi murmushi yace "Daxu..." Inna tace "Baki ga da ya shigo ba daxu duk a kode wllh, ai yanxu ya washe a haka, Allah ya rufa ma ke da Mujaheed asiri ba ku je ba, baku da rabon wahala, amma wannan garin ae ba wajen xuwa bane tirr" Imaan ta duka kusa da shi tana dariya tace "Toh me ka kawo min ya Yusuf" ya shafa kansa bai ce komai ba, Inna tace "Yauwa ina maka xancen kirki kafin wannan mata ta shigo..." Ya sauke ajiyar xuciya a hankali yace "Ae ina ji" tace "Ko kai ya ka gani, wannan ba shawara mai kyau bace na kawo?" Da kamar baxae ce komai ba sai kuma yace "Da dai kiyi hakuri a bar xancen inna...." Ta katse sa da sauri tana gwalo ido tace "Xancen auren?" Calmly yace "Ehh" inna ta saki baki tace "Ehh lallai kai da Mujaheed kun xama abun tsoro, yanxu har kai isuhu bakin ciki kake ma yar uwar taka? Anya 'ya yan Ahmadu xa ku ga annabi kuwa? Ba kunya ba tsoron Allah ku fito kiri kiri kuna nuna ma yar uwar ku bakin ciki" Shi dai kallonta kawai yake, imaan ma sai kallonta take don bata gane kan xancen ba, Inna na tabe baki tana girgixa kai tace "Har abada in dai ni yar halas ce ba ni ba shawara da gantalallu irin ku, tun da haka ku ka xama gwara in yi ta kaina, to wai tsaya idan aka ki gabatar da ita jika ta xa mu yi mu baku ku shanye?" Nan ma dai bai ce mata komai ba, ta rike ha6a tace "Ai ni na shiga uku, lallai 'ya yan Ahmadu mugaye ne, sam ba alheri a ranku, to wai tsaya... ku xa ku aureta idan aka bar xancen?" Ya kalleta yace "Kika sani?" Imaan da ta fara dago xancen ta wani hade rai xata mike ta bar parlon Inna ta riga ta, tana kallon Yusuf cikin rashin hankali tace "Ku har kuna da kudin da xa ku rike min jikata? Ku a su wa kuma Allah na tuba, lallai kun cika marasa tsoron Allah, me kuma Imaan xata yi da kai ko Mujaheed Idan ba sa6o kake son yi ba, ka ja mana fushin ubangiji...." Murmushi kawai Yusuf yake, imaan ta nufi kofa xata fita, still tayi jin kamshin Mujaheed, juyawa tayi da sauri ta nufi dakin inna tana cewa "Kar ku ce masa ina nan" Mujaheed ya shigo parlon bayan few seconds, inna ta xauna tace "Imaan dai bata nan idan ma ita ka xo nema" Mikewa Yusuf yyi ya nufi kofa ya fita. Bedroom dinta Mujaheed ya nufa direct, inna tace "Da dai ka kinkimota ku fito don na share dakina tasss ba ko kwayar datti, kada a bata min a cuce ni ba uban wani ke min gyaran ba" Imaan na jin dama inna tace masa bata nan tasan dole xai shigo dakin, ta shige bayi da sauri ta sa makulli, Mujaheed ya murda kofar bathroom ya ji a kulle, juyawa yyi ya dawo parlor yana kallon inna yace "Kiyi mata magana ta ban wayata kada in sa ta kuka" Inna tace "Ikon Allah ya fi gaban haka, lkcn da wayar ya fita hannun ka ya shiga nata sani nayi Mujaheed? Kaji min raini dai, ni dai ta fito min daki gaskiya don ba Aisha bace ta share min" ya gyada kai ya juya ya fita parlon, Da kyar Imaan ta yarda ta fito bayan tafiyarsa da kusan minti goma, Inna dake tsaye bakin kofar bathroom din tace "To uwar me kike masa da wayar sa ya taba ki ya taba alakakai ya taba jaraba, ke dai ki daina tsokanan mutane kiyi ma kanki fada Imaan" Imaan ta fice a dakin, inna tace "Da dai ya kama ki ya nakada maki shegen duka da xai gigitaki in ga me ce masa don me a gidan nan, yarinya kawai kamar yar aljanu, wannan iri ta Bukar Allah ka raba mu da ita lafiya, duk da dai lkci ya kusa" A hankali Imaan ta bude kofar parlorn inna ta fita, ta gwammace tayi xagaye da ta bi normal route, da gudu ta shige parlon su ta sa makulli tana murmushi. Karfe tara da wani abu Ammi ta shigo dakin Imaan, Imaan dake xaune gaban madubi ta fito wanka kenan tace "Na xaton fa kinyi bacci" Ammi tace "Ki ji da ni kwanciya xan je inyi" mikewa tayi ta hau saman gado Ammi na kallon wayar kan gadon tace "Wayar waye wannan?" Imaan tace "Na yaya ne" Ammi na mata wani kallo tace "Me wayarsa yake a nan?" Kamar xata yi kuka tace "Ammi to ya dauke min nawa wayar ya ki ya bani" Ammi na kallonta da kyau tace "Kin san Allah idan baki kame kanki gidan nan ba kin raba kanki da Mujaheed sai na sa6a maki Imaan, yaushe ke da shi ku ka fara shirin da har xa ki dauke masa waya?" Imaan dai bata ce komai ba, Ammi ta hade rai sosai tace "Let me make it brief, daga yau na datse sabon alakar ku na gulma da Mujaheed, duk kika kuskura naga sabanin abinda nace wllh sai kin sha mamaki na, ko dama kin hada wani abu da shi ne ban sani ba? Kuma maxa ki kai ma inna wayar ta basa kayansa, naki kuma idan ya ga daman baki toh, idan kuma bai baki ba ki bar sa, hope am clear?" Kai kawai Imaan ta daga mata a hankali, Ammi tace "Shegantaka kawai, wai wani yaya, A'a ba yaya ba yayo, in sake ganin kin kalli inda yake a gidan nan idan ban tsole maki idanuwa ba" daga haka ta shafa mata lotion din maganinta sannan tace "Ki rage fan din, sai da safe" daga haka Ammi ta fita ta kulle mata kofa, Imaan ta saka kayan baccinta ta koma mirror tana shafa lotion a kafarta taji ana bude window, mikewa tayi da sauri tana kallon window din, ido hudu suka yi da Mujaheed ta dauke kai, strictly taji yace "Bani wayata" Ta make kafada tace "Nima ka bani nawa first" Yace "Na fara maki wasa a gidan nan koh?" Ta ki cewa komai ta daura kafarta kan stool dake gaban mirror tana shafa lotion dinta, jin shiru ta juya, kallonta taga yana yi da lumsassun idanuwansa, ta hade rai tace "Yaya yanxu idan sauro ya cije ni na fara rashin lafiya fa? Dubi yanda ka bude min window fa, ni dai ba ruwana idan na fara ciwo" calmly yace "Kar ki bari in shigo gidan nan, wllh xan sa ki kuka, give me my phone I want to use it" yar dariya tayi ta dau turare tana fesawa, yace "OK kina xaton baxan iya shigowa bane?" Ta wara ido tace "Toh ai bance maka kar ka shigo ba" Tana fadin haka ta karasa saman gado ta kwanta ta rufe da duvet, rufe window din yyi yana gyada kai ya bar wajen. Mujaheed xai shiga parlon su suka hadu da Daddy, gaida sa yyi da ladabi daddy na tambayarsa ya aiki yace "Alhmdllh" yana tsaye har daddy ya shiga gun Abba, ya d'an yi jim, can ya tafi apartment din su imaan, ya fi second goma tsaye ya kasa bude kofar, A hankali ya murda kofar ya shiga yana kallon cikin parlon, babu kowa sai tv dake kunne, dakin Imaan ya nufa ya bude kofar, kwance ya ganta har ta yi bacci, ya dinga bin dakin da kallo ya karasa kusa da ita, daukar wayarsa da ta ajiye bedside drawer yyi yana kallonta, gaba daya ta takure waje daya saman gadon sleeping peacefully sai dai ta cire duvet din, dauka yyi ya rufa mata ya tafi gun switch din fan din dakin ya kashe fan din gaba daya ya juya xai fita yaga Ammi tsaye bakin kofa, still yyi ya kasa cewa komai, lkci daya ya sauke kansa ya fara kame kame yace "I... I came to take my phone"
Chapter 86 · 0% Book details