← Book details Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 300

Sashe 120

Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

bamu da kudin biyan kaji..." wani gentleman dake xaune wajen ne ya taso ya iso gun motar yana kallon Imaan yace "Lafiya kuwa?" Inna tace "Ina fa lafiya yaro an kacalcala kaji uku ba kudin da xa mu biya, nace ta mayar masu tsiyar su shine take kokarin tara min jama'ah wllh ko amsar ledan ma ni ban yi ba balle inji kamshin naman ciki, Toh a kan meye baxa su amsa ba? Dama haka ake yi?" Murmushi kawai mutumin yake yana kallon Imaan yace "Kazan guda nawa ne?" Da sauri Inna tace "Gudu uku ne wllh, daya nata daya nawa, daya na yan sa ido a gida..." Hannu ya sa a aljihu yana kallon Imaan, Mujaheed ya bude motar ya fita gun masu gashin kajin ya fiddo dubu biyar ya mika masu, daga Inna har mutumin da imaan bin sa da kallo suka yi, Inna tace "Kaga katon banxa ko? Ce mana yyi ba shi da kudi fa har sai da ya bari duniya ta gama sanin abinda muke ciki sannan ya fita wani zokai zokai da shi xai bada kudi, Toh Allah ya saka min kunyata ni da ya so yi gaban masu kaji da tona min asiri da yyi a gabanka" Dariya mutumin ya dinga yi yana kallon Inna da ta tsuke fuska tana kallon Mujaheed, imaan ta kalli mutumin gabanta ta mayar masa da kudin da ya mika mata tace "Mun gode" Yana murmushi yace "Don't worry...." Dawowa Mujaheed dake kallonsu yyi ya amshi kudin hannun imaan ya kamo hannun mutumin ya saka masa a ciki yace "Thanks for ur concern" daga haka ya bude mata front seat yana kallonta, ta sunkuyar da kanta ta shiga ya rufe motar, ya xaga ya shiga motar ya tada ya bar wajen. Inna tace "Ni dai duk wanda niyyarsa ya kunyata ni a duniya Allah ya min kantangar karfe da shi, kuma ya saka min" Shi dai Mujaheed bai tanka ta ba har suka isa gida. Shirye shiryen biki aka shiga yi a gidan ba kama kafar yaro barin bangaren Umma da kawayenta, ji take kamar an mata albishir da aljanna xata aurar da first and only son dinta xuwa ga 'yar masu kudi ba na wasa ba, shi ko gogan kamar ba shi xai yi aure ba babu Shirin da yake, idan ya fita aiki tun safe dama sai dare xai dawo don kawai bai son participating a shirin da ake a gidan, shi gaba daya bai fi sau uku suka hadu da Safeenar ba ma, kuma duk Umma ke tilasta sa sai yaje, ko da wasa bai taba dialing lambar Safeenah don kansa ba sai idan yayi missing call dinta, a rana kuwa tana kiransa fiye da sau goma, shi kansa mamakin irin son da take masa yake duk da yasan dole ta fahimci fa baya yinta amma duk class dinta bata nuna ta damu ba sai kara shige masa take. Tun ranan da Mujaheed yyi ma Imaan warning ko da wasa bata son Sadeeq ya xo kofar gidansu sai dai waya amma abinda ke bata mamaki yanda taga shi ma bai damu ya xo ba kamar da, da kusan kullum sai ya xo, sai dai suna kusan raba dare suna waya da shi cikin duvet yanda Ammi baxata ji ba, Duk Friday day kuma sai ya aiko wani worker din gidansu gun Inna ya kawo mata sako, Imaan dai ta tasan soon Mujaheed xai yi aurensa ya kara gaba sai taga ta yanda xai hanata tsayawa da Sadeeq kuma. Yau Friday da ya kama saura sati daya bikin Mujaheed da Safeenah Imaan ta fito daga dakinta ta shiga na Ammi, durkusawa tayi kusa da gado tana kallon Ammi tace "Ammi xan wuce yanxu" Ammi tace "Toh na dai gaya maki kar ki dade imaan" tace "Wallahi baxan dade ba Ammi" Ammi tace "Toh ki gaisheta Ina mata ya jiki" Imaan tace "Toh xata ji" mikewa tayi ta fita daga dakin ta shiga kitchen ta dauko wani leda mai dauke da can malt ta fito parlor ta dau jakarta sannan ta fita gidan, kamar mai tausayin kasa ta isa bakin titi bayan few minutes ta samu adaidaitan da xai kai ta GRA, tafiyar kusan minti ashirin suka yi, suka shigo gate din layin as usual ko ina tsit sai haushin karnuka, dai dai gate din kantamemen gidan Imaan ta sa mai adai daitan ya tsaya ta sauka ta basa kudin tana kallon masu gadi dake xaune bakin gate din gidan, gaishesu tayi daya daga cikinsu yace "Wa kike nema?" Tace "Mariya" Mai gadin yace "Toh ki kirata" shiru tayi tana kallonsa don kwanaki da dadewa da ta xo ae basu mata tambayar komai ba, ba musu ta fiddo wayarta a jaka ta shiga Kiran Mariya, Ba a dau lkci ba sai ga Mariya ta fito gidan, Rungume imaan tayi tace "Welcome frnd" tana kallon masu gadin tace "Kawata ce duk ranan da ta xo ku bar ta shigo babu interrogation" bata jira cewarsu ba ta ja hannun Imaan cike da farin cikin ganinta suka wuce ciki, Imaan tace "Dama kin ma ji sauki koh?" Mariya ta marairaice tace "Yau fa nayi getting self dina" Imaan na murmushi tace "Toh Allah ya kara lafiya" sai da ta fara kai Imaan dakin Mahaifiyar ta ta gaisheta sannan ta ja ta xuwa makeken bedroom dinta, imaan ta xauna tace "Siblings din ki fa?" Tana fiddo ruwa da lemo a fridge dinta tace "Sun fita da Yaya Annur shan ice-cream kinsan yau Friday" murmushi kawai Imaan tayi, Mariya ta ajiye mata drinks din tace "Me xa ki ci, akwai yam with sauce, cous cous with sauce, or kin fi son snacks?" Imaan ta girgixa kai tace "A'a na ci abinci a gida" Mariya ta harareta tace "A'a ni dai sai kin ci wllh" Imaan tayi dariya tace "Bayan nace maki na koshi, Ni la'asar kawai xan yi" Mariya ta nuna mata bathroom dinta tace "Kiyi alwala ga bathroom kafin ki fito xan kawo maki abincin" bata jira cewar Imaan ba ta fita da sauri, Murmushi imaan tayi ta mike ta cire Hijab din jikinta ta ajiye ta shiga bathroom din, tana gama alwala ta fito dai dai nan aka bude kofar dakin, still tayi tana kallonsa, kamar yanda shi ma ya tsaya yana kallonta, juya masa baya tayi da sauri tana xaro ido....
Chapter 120 · 0% Book details