Sashe 273
Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gun Aunty suka fara wucewa a bedroom dinta, Mujaheed ya xauna gefenta yace "Aunty xa mu wuce" Aunty tayi murmushi tace "Toh maa sha Allah, Allah ya bada xaman lafiya ya kawo kazantar daki" murmushi Mujaheed yyi ya mike Imaan dai na durkushe kasa, Aunty ta nuna mata gefenta tace "Dawo nan daughter" Mikewa Imaan tayi tana share hawayen idonta ta dawo kusa da Aunty ta xauna, Aunty ta kalli Mujaheed tace "Toh sai ka bamu waje koh?" Juyawa yayi ya fita dakin yana murmushi. Nasiha me ratsa jiki game da xamantakewar aure Aunty ta dinga yi mata tana bata shawarwarin da xa su amfaneta, Imaan dai ta rufe fuskarta jikin Aunty hawaye na sauka idonta, Aunty ta dago kanta daga karshe tana kallon kwayar idonta tana murmushi tace "Allah ya albarkaci auren ki my daughter, ya kawo mana 'yan biyu da wuri" Imaan ta sauke idonta kasa hawaye na xuba idonta, Aunty ta mike ta dagota tace "Toh mu je yana jiran ki a waje" tana rike da hannunta suka fita dakin, Maimoon dake parlor ta mike ta rungume Imaan a hankali tace "Soon idan Maryam ta dawo xa mu je mu gan ki kin ji sis?" Imaan ta gyada mata kai hawaye wasu na bin wasu a idonta, Aunty na rike da ita suka nufi kofar fita tace "An kai maki duk kayan ki can gidan, a ko da yaushe ki xamo cikin kamshi duk da nasan ki ba baya ba, sannan ki xama mai tattala komai naki da na mijin ki, kin ji?" Kai kawai Imaan ke gyada mata, ganin Mujaheed tsaye jikin flower Aunty tace "Toh ga daughter na amana Muhd, though bani da fargaba nasan xaka rike min ita yanda ya kamata, sai kuma ayi ta hakuri, Allah ya baku xaman lafiya" ya sauke kansa kasa yace "In sha Allah Aunty, nagode" Aunty tace "Xa ku je kuyi ma Ammi sallama koh?" Yace "Ehh" Aunty tace "Ohk to sai kun fito" Mujaheed na gaba imaan na biye da shi har suka isa part din su, shi ya fara shiga parlon da sallama sannan ta bi bayansa walking slowly, juyawa yyi ya kama hannunta ganin ta makale bakin kofa ta warce da sauri, jin an bude kofa ya nufi kujera, Ammi ta fito daga bedroom dinta tana kallonsu, ya xauna kansa a kasa yace "Ina yini Ammi?" Tace "Lafiya qlau Mujaheed, ya aiki" yace "Aiki Alhmdllh" Imaan dai na tsaye bata bude fuskarta ba har lkcn, murya can kasa Mujaheed yace "Dama xa mu wuce ne yanxu Ammi" Ammi tace "Toh Allah ya kiyaye hanya" A hankali yace "Ameen mun gode" kallon Imaan da taki bude fuskarta tana shessheka yyi ya sauke kansa sannan ya mike yace "To mun tafi" Ammi tace "Allah ya sanya alkhairi, ya bada xaman lafiya...." Imaan ta nufi Ammi hawaye na sauka idonta, Ammi tayi murmushi tace "Ji shashanci...." Rungumeta Imaan tayi ta fashe da kuka, Ammi bata iya ta ce komai ba, Mujaheed ya juya a hankali ya fita daga parlon, Ammi ta dago kanta tana kallonta, lkci daya jikinta yyi sanyi tace "Ki xama me biyayya ga mijinki kinji Imaan, Allah ya albarkaci auren ku, ya baku xuri'a dayyaba, nasan baxa ki bani kunya ba" Kuka kawai Imaan take bata iya ta amsa mata ba, Ammi tayi karfin halin kin barin tayi hawayen ita ma ta kama hannun Imaan har bakin kofa tace "Allah ya tsare" daga haka ta sake ta Imaan ta fita daga parlon still crying, Parking space ta tadda Mujaheed tsaye ya rungume hannayensa ya kafeta da ido, kin karasawa gun sa tayi ta tsaya, ya bude mota sannan ya nufeta ya kamo hannunta ya bude front seat ta shiga ya rufe motar, ya xaga ya shiga maxaunin driver yyi horn mai gadi ya bude masa gate ya fita gidan da motar, yana hawa saman titi ya kamo hannunta a hankali cikin sanyin murya yace "Ki daina kukan nan haka plss, tare da yayan ki fa kike" Kamar ya kara tunxurata yin kukan hakan yasa yayi shiru, har ya tsaya gun masu siyar da fruits ya siya ya dawo motar Imaan bata bude fuskarta ba, ya ci gaba da driving dinsa, bayan kusan minti goma ta xame hannunta a hankali daga fuskarta tana kallon titin gabanta, da sauri ta kallesa tana goge idonta tace "Ina kuma xa mu je yaya?" Ya kalleta murya can kasa yace "Zaria xa mu je" kallonsa ta dinga yi ko kiftawa babu, ya kamo hannunta cikin sanyin murya yace "Xa mu je mu gaida Umma" Imaan dai tayi shiru bata ce komai ba, and the rest of the journey was very silent har suka isa garin Zaria, horn yyi bakin gate, sabon Mai gadi da ya sa a gidan ya fito ya bude gate din ya shiga da motar yayi parking, imaan dai gabanta sai faduwa yake sosai, ya kashe motar ya sauka ita ma ta bude side dinta a hankali ta sauka tana bin gidan da kallo, Rahama ce ta fito daga cikin parlor ganinsa ta nufesa da sauri cike da murnan ganinsa tace "Sannu da xuwa Yaya.... Mujaheed yace "Yauwa sannu" tunda Rahama ta kalli Imaan bata sake kallonta ba ta amshi ledan hannun yayan nata ta wuce ciki, Rufe motar yyi yana kallon Imaan yace "Mu je" ta sunkuyar da kai bata ce komai ba ya kama hannunta suka nufi entrance din parlon, ko ba a fada masa ba he notice duk a tsorace Imaan take, though shi ma dai karfin hali kawai yake don bai nuna ba har suka shiga parlon, xaunar da ita saman kujera yyi sannan shi ma ya xauna, sosai xuciyar imaan ke bugawa, yana kallonta murya can kasa yace "Relax plss imaan..." Tayi masa murmushin karfin hali tana karanto addu'a a xuciyarta, Ummi ta leko daga kitchen ta fito tana murmushi tace "Welcome Yaya" yace "Thank you, Umma fa?" Ummi tace "She's upstairs" Bata rufe baki ba sai ga Umma, Imaan ta daga kai suna hada ido ta sunkuyar da kanta da sauri, Umma ta karasa shigowa cikin parlon ta xauna, Imaan ta xamo kasa ba tare da ta yadda sun hada ido da ita ba murya can kasa tace "Ina yini Umma" Umma bata kalleta ba tace "Lafiya lau, Alhmdllh" Mujaheed yyi kasa da kai yace "Ina yini Umma" Umma tace "Lafiya lau ya gida" yace "Alhmdllh" tace "Ya aiki fa" yace "Alhmdllh Umma" Umma tace "To madallah" kallon Ummi tayi tace "Kin gama girkin ne?" Ummi ta nufi kitchen tace "A'a na kusa dai" Mujaheed na kallon Umman tasa yace "Aunty Mariya ta koma ne?" Umma tace "Aa taje kasuwa xata dawo" Mujaheed yace "Ohk..." Ummi ta dawo rike da tray mai dauke da table water daya da goran coke daya da cup ta ajiye kusa da Mujaheed, kallonta kawai Mujaheed yake har ta mike xata wuce Umma tace "Ruwan daya ya rage a gidan?" Ummi bata ce komai ba ta xumburo baki ta koma kitchen sai ga ta ta dawo da wani table water guda daya ta ajiye kan tray kusa da Mujaheed ta wuce, Umma tace "Ya su Maimoon fa?" Mujaheed yace "Suna lafiya" Umma tace "Daxu Yusuf ya xo, bai jima da wucewa ba ma, shekaranjiya ma ya xo" Mujaheed ya mike yace "Ohk, ban yi la'asar ba Umma, xan je in yi sllh" sosai gaban Imaan ya fadi jin xai fita ya barta ita kadai, ta dinga kallonsa bata dai ce komai ba, Umma tace "Toh ka tafi masallaci, ita baxa tayi sllhn ba?" Mujaheed ya kalli Imaan yace "Kin yi sllh ai?" Girgixa kai tayi da sauri duk da tayi a gida, Umma tace "Toh ta tafi sama" mikewa Imaan tayi ta nufi stairs xuciyarta na bugawa, Mujaheed ya bi ta da ido sannan ya kalli Umma dake kallonsa yace "Sai na dawo Umma" Umma tace "Toh sai ka dawo" daga haka ya fita parlon. Imaan ta bude daya daga dakunan ta shiga, sosai gabanta ya fadi ganin jakunkunan Umma a dakin wato dai dakin Umma ta shiga, tana shawaran xata fita daga dakin aka bude kofa sai ga Umma ta shigo, kasa kwakkwaran motsi tayi inda take tsaye, kallo daya Umma tayi mata ta dau wayarta dake gaban mirror ta fita dakin, Imaan ta sauke wani ajiyar xuciya har lkcn gabanta bai bar faduwa ba, darduman da ta gani shimfide kasa a dakin ta nufa ta xauna a kai tana ci gaba da karanto addu'o'i a ranta, ta fi minti goma xaune dakin aka bude kofa, kanwar Umma Hajiya Mariya ta shigo dakin, da fara'a take kallon Imaan tace "Ashe amarya ce a gidan yau, sannun ku da xuwa" Imaan ta kirkiri murmushi tace "Ina yini Mama" Hajiya Mariya tace "Lafiya lau Imaan, ya ku ka baro mutan gidan?" Imaan tace "Alhmdllh" Hajiya Mariya tace "Toh madallah, Allah ubangiji ya sanya albarka a auren nan, ya bada xuri'a dayyaba" Imaan ta sunkuyar da kai bata ce komai ba, Hajiya Mariya ta ajiye handbag din hannunta ta fita dakin. Imaan na ta xaune dakin har shidda saura na yamma, Rahma ta bude kofar dakin tana kallonta tace "Ance ki sakko ki ci abinci" daga haka ta juya ta wuce, a hankali Imaan ta mike ta dauke pray mat din ta linke ta ajiye sannan ta nufi kofa ta fita walking slowly har ta isa downstairs, Mujaheed na xaune parlon da Umma dake dibar masa abinci a plate, Hajiya Mariya ma na xaune parlon tana answering din call, Imaan ta karaso parlon kanta a kasa ta xauna a kasa jikin kujera, kallonta kawai Mujaheed yake, Umma ta ajiye masa abinci kusa da shi, ta dau wani plate din ta xuba wani ta kalli Imaan, kafin tace komai Mujaheed na kallonta yace "Ga abincin ki" mikewa Imaan tayi ta nufi Umma ta duka ta dau abincin a hankali tace "Nagode" sannan ta koma ta xauna duk da ba yunwa ta ke ji ba, hira kawai Mujaheed ke yi da kanwar mum dinsa, Imaan sai juya abincin gabanta take, Hajiya Mariya tace "Toh ko xa ki wuce dinning ki ci abincin Imaan?" Imaan tayi murmushi tana kallon direction din dinning din, Hajiya Mariya tace "Tashi ki je can ki xauna kin ji" mikewa Imaan tayi ta dau abincin da