← Book details Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 146 OF 300

Sashe 146

Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kasa cewa komai Imaan tayi tana kallonsa don ba karamin tsorata tayi ba, cikin tsawa yace "Ba tambayar ki nake ba sai na baki dirty slap?? Who sent you, waye ya aike ki??" Hawaye ya cika idonta ta sunkuyar da kanta bata dai ce komai ba, saketa yyi ya jingina da bango xuciyarsa na bugawa, ta tsallake abincin da ya xube ta wuce da sauri tana goge idonta ya bi ta da kallo har sannan kirjinsa bai daina bugawa ba, hade kai yyi da bango yana Kiran Allah a ransa, ya fi minti biyu a haka sannan ya juya da kyar ya nufi bangarensu yana jin idanuwansa na juya masa. Imaan na kwance daki da yamma idonta a lumshe duk da ba bacci take ba, wayarta dake kusa da ita ya fara vibrate, bude ido tayi tana kallon wayar, tun abinda Mujaheed yyi mata daxu take daki taki fitowa duk nacin da Maryam tayi da ita ta fito, gaba daya she is moody, a hankali ta dau wayar tayi picking ganin Sadeeq ne ke kiranta, sallama yayi mata daga daya barin, murya can kasa ta amsa, yace "Are you okay dear?" Shiru ta d'an yi sai kuma tace "Bana jin dadi" yace "Subhanallah baki jin dadi kuma, kin yi stressing kan ki da yawa kenan, what's wrong? I mean me kike ji ke damun ki?" Cikin sanyin bemurya tace "Ache all over" yace "Subhanallah, kin sha drugs din ki?" Ta gyada kai kamar yana ganinta yace "Ohk toh xan kawo maki wani yanxu sai ki sha shi da daddare, you will feel much better" tace "Toh" yace "Xan kira ki idan na iso" daga haka yyi mata sallama ta katse wayar ta ajiye ta rufe idonta. Biyar saura ya sake kiranta yana waje, Hijab ta saka har kasa, xata fito ta tuna birthday gift dinsa ta koma ta dauko flower din da cards ta saka cikin hijab ta fito, Few visitors ne a parlon nasu, ta tafi dakin Ammi ganin bata ciki ta fito, a balcony ta tadda Ammi da Mama Hansai, Ammi na kallonta tace "Ina xa ki?" Ta sunkuyar da kai tace "Ammi ba dadewa xan yi ba ana kirana a waje ne" Ammi na kallon hannunta dake cikin Hijab tace "Meye wannan kike boyewa a hijab?" Murmushi tayi kanta a kasa tace "Ammi ba komai bane, sako ne fa" Mama Hansai na dariya tace "Yi wucewar ki kinji" wucewa imaan tayi tana murmushi, Yana tsaye jikin motarsa idonsa sanye da glass ya sa kananun kaya, sunkuyar da kai tayi ta isa kusa da shi, da damuwa yace "Ya jikin" tana d'an murmushi tace "Da sauki" ya dauko wani leda a gaban motar ya mika mata yace "ki sha tablets daya each each kafin ki kwanta" Bata amsa ba ta fiddo hannunta dake cikin hijab ta mika masa flower din hannunta cikin sanyin murya tace "Happy birthday dear" still yyi yana kallon flower din ko kiftawa babu" lkci daya ya karba yana wara ido so happy yace "Waowww Thanks soo much baby I love it...." Ita dai murmushi kawai tayi, a hankali tace "i am happy u love it...." Ko bai fada ba she can see how happy he is, yana wara manyan idanuwansa yace "But baby how did you know I love flowers plss?" Ta langwabar da kai tace "I only guess" lumshe ido yyi murya can kasa yace "I feel like hugging you sweetheart" d'an murmushi kawai tayi ta dauke kai tace "Ni xan koma ciki, and I am sorry I won't be able to attend ur party saboda bana jin dadi" a sanyaye ta kare maganar, cike da damuwa yace "Ai na maki uxuri dear, Allah baki lafiya thanks a lot, I will give you a call later" a hankali tace "Ameen ngd" daga haka ta juya ta koma cikin gida ya bi ta da kallo still smiling. Mama Hadiza ce xaune parlon Inna tare da Ta Rasulu, cikin rashin jin dadi Mama Hadiza tace "Yanxu fisabilillahi kin kyauta min Inna, duk yanda na takarkare a kan an ci maki mutunci sai ki watsa min kasa a ido??" Inna tayi kasa da murya tace "Toh Hadiza shikenan ana ta bani hakuri ana hada ni da Allah sai in botsare kamar shaidaniya? Babba fa dama da hakuri aka san sa, baki ga yanda aka cika min parlon nan ba daxu ana bani hakuri har da su Audu d'an tsut, daga karshe sai kuma ga Bulasawa da kansa shi ma ya tako har parlon nan ya ce inyi hakuri, to idan dai ni ba tsohuwar banxa bace mai kunnen kashi mara jin magana Hadiza ai ya ci ace na yayyafa ma raina ruwan sanyi in hakura, kuma ni dai gaskiya Rukayya bata ta6a min irin haka ba, hau ne ya fada mata...." Ta Rasulu na nuna Inna ta kankance ido tace "Ke dai Asabe ki dinga jin tsoron Allah, nan kika maida mu mahaukata muna bambami daga karshe kika watsa mana kasa a ido wai kin hakura, Toh ai ina gida xa ki sa a kirani ki kawo min karar Rukayya, ba kuma ruwana wllh don baxan saurare ki ba, ke kuma Hadiza me xai dame ki?? Ai kadan da aikin Asabe kenan baki biyu, ni ban yi mamaki ba, ni ba dai ruwana ban ce komai ba in yi magana ta kullace ni, amma banda haka me aka yi aka yi wani shegen Bulasawa da har xai bata hakuri ta hakura? Bayan abinda tsinanniyar matar nan Rukayya ta mana, Kai Asabe Allah ya baki lafiya, ya kuma shirye ki, ni dai kin ga tafiyata nan...." Inna ta tsuke fuska tace "Toh ai ni ba gantalalliya bace da xa ayi ta ba ma hakuri in ki hakura kamar kafurar Bayan tsauni, ehe... Bulasawa kuma ni ya fi min kowaaa, yaro mai hankali da natsuwa mai magana irin ta manya, duk sai da ya fada min maganganu masu dadi da kwantar da xuciya wanda su Amadu suka kasa, toh ni ko me xance ma yaron Banda Allah ya masa albarka, ai in dai bai auri Imaan ba to sai dai in ni Asabe bana numfashi, Imaan ta sa ce in sha Allah, Bai fi min wasu 'yan uwan nawa ba ma ni Allah na tuba, Rukayya kuma ai tuni tana akurkin gidan da ta gina ma iyayenta sai kace ba ni ta ma rashin mutunci ba da xa a bar ta ta kwana gidan nan...." Ta Rasulu ta mike tace "Ni dai tunda kika kunya ta ni, kika kunyata Hadiza Allah sai ya saka mana ya bi mana hakkin mu, Rukayya kuma mu dai je xuwa muna nan dake xata dawo gidan nan...." Inna tace "Ke ni fa ban hakura da abinda Rukayya ta min balle ta dawo, ai Rukayya yar iska ce, aure ne dai nace aje a daura kada 'ya yana su ji kunya" Ta Rasulu tace "Oho dai ni kin ga tafiyata sai ki saka Bukar gaba ya bada kudin nan na laluran Imaan a san abun yi...." Daga haka ta fice daga parlon, Inna tace "Toh Allah bar xumunci ta Rasulu, Allah ji kan mai salati da jikan shehu, Allah ya saka da alkhairi ai ni kin gama min komai a duniya wllh kin fi min kowa ma, Allah ya bar mu tare sai kuma kin dawo bikin Imaan da Maimoon in sha Allah, Kai ae xan taho har gida maki ban gajiya, Bari dai 'yan kauyen nan su koma kauyukansu xa ki gan ni" Mikewa Mama Hadiza tayi ta fice daga parlon rai ba dadi, Inna ta bi ta da kallon gefen ido tace "Toh meye kuma axumi uku da xa ki yi, sai kace warce bata axumin Ramadan, Ni dai ba ruwana dama ban aike ki kiyi ta rantse rantse ba...." A ranan Mama Hadiza bata kwana gidan ba ta tafi gidan wata yayar Mai gidanta dake nan garin kadunan. Imaan na parlon Inna bayan isha tare da Maryam suna cin abinci aka bude kofa, kallon kofar suka yi Mujaheed ya shigo da sallama murya can kasa, wani daddadan kamshi ya gauraye parlon, yayi wani kyau na daban cikin milk shaddar jikinsa dake ta talli, Maryam na murmushi tace "Groom dama har yanxu baka tafi ba?" shi dai bai ce mata komai ba ya xauna, Imaan dai bata kalli inda yake ba tun bayan da suka hada ido shigowarsa, ta dinga cin abincinta a hankali, daga cikin dakin Inna tace "Mujaheed ne?" Maryam tace "Ehh" da sauri Inna ta fito ta marairaice tace "Tun daxu nake cigiyar ka Mujaheed, nace to ko har ka tafi wajen amaryar ne ba sallama ni patuu...." Kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Yanxu xan tafi" Xaunawa Inna tayi ta fashe da kuka a hankali tace "Shikenan yanxu Mujaheed sai dai ka xo ka gaishe mu ka tafi?? Shikenan ba kai ba kwana cikin gidan nan yanxu balle ka xo da sassafe ka gaisheni, wa xai dinga shigo min nan muna hira? Shikenan tafiya xaka yi ka bar ni yanxu, dama ba kowa gare ni ba sai Allah sai kai, kaine me debe min kewo gashi yanxu kayi aure xaka tafi gidanka ka barni ni kadai raina..." Mujaheed bai san lkcn da yyi murmushi ba sai dai bai ce komai ba yana danna wayarsa, Inna na share hawayenta cikin rawar murya tace "Rayuwa kenan, lallai sabo turken wawa, Allah ubangiji ya ba ku xaman lafiya da matar, in sha Allah xuwa nan da kwana biyu imaan xata rakoni don baxan gane gidan ba in xo ganin daki in sa albarka kuma in maku nasiha da amaryar, Allah ya sanya alkhairi... Ni dai baka taba min komai ba Allah maka albarka" Mujaheed na murmushi a hankali yace "Ameen" Mikewa yayi yace "Toh sai da safe" Inna ta kara rushewa da kuka har da rike kai, Maryam ta kasa ci gaba da danne dariyar da ke cinta, Imaan kam kin dago kanta tayi tana juya shinkafar gabanta, Cikin kuka sosai Inna tace "Shikenan kuma, wayyo rayuwa kenan...." Maryam na murmushi tace "Allah ya bada xaman lafiya Ya M.A, sai mun xo ganin dakin Aunty amarya" Mujaheed ya d'an yi murmushin karfin hali ya gyada mata kai ya juya ya nufi kofa, Inna na kallon Imaan da ta
Chapter 146 · 0% Book details