← Book details Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 84

Sashe 9

Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read

ki fita sha'aninta haihata haihata." Daga haka ta ja hannunta suka fice. Bance uffan ba, nasa tsintsiya na share wannan ɗan wake. Bance da mijinyawa bani na zubar ba, hannunshi naja muka shige ciki. Na ɗakko mana filet muka zuba tsire da masarmu, na samu ƙaramin kwano na zuba ma Nanno. In mun gama ci, sai ka kaima Nanno wannan ko? Sannan menene labari naga ka jima" Na soko hakanne dan in mantar dashi abinda ya faru, nikam bai dameni ba. Uwatale dai cikine da akace ina dashi ya dameta shi yasa take wannan ƙananun gulmammakin ba wani abun ba. "Hmmm Abdulƙadirine yazo da wata maganar banza da wofi wai Halima yake so zai aura" Masa da tsire ya haɗa, madadin ya cunkusa a bakinshi saiya cunkusamun. Shima ya ɗauka ya cunkusa a bakinshi. Dole muka hau tauna, nice harda lumshe idanuna dan daɗi. Wacece Halima kuma? " Saida ya kuma cika baki ya cinye kana yace. "A garinnan take kusan sa'armu ce tare muka yi wasa da'ita muna yara lokacin. To sai ta samu jarabawa wani saurayinta direban babbar mota ya ɗauketa suka shiga bariki fa. Ta bar gaban iyayenta. Da yawa ance ana ganinta tare dashi a maraba. Daga baya akace sun koma tafa, can wajajen ikko dandalin direbobin mota kenan. Kuma dandalin masu zaman kansu, dandalin ƴan tuwo tuwo. Ita kanta wai tayi sana'ar tuwon acan a lokacin da shi wanda ya ajjiyeta ya tsallaketa yaje yayi aurenshi. To itace ta dawo gida bayan taci maraba, taci tafa, taci Lagos wai ita Abdulƙadiri zai aura. Harma sun daidaita. Jama'a da yawa fa masu fita cirani kudu, suna dawowa da labarin sun ganta, a lokacin har ana zargin tabar Musulunci, duba da irin shigarta, da gashin doki da take sakawa. Akwai wani ɗan bariki a ƙauyennan namu mai suna Muntari ƙwallo. Ƙwallon ɗan duniyane gaya. To shima ance yayi zaman dadiro da halima a Ogere. Ya rasu amman, anata raɗe_raɗin ciwon sidane yai ajalinshi, wasu kuma suka ce tarin fukane yai sanadinshi. Ita dai Haliman ance har ƴa a haifa a bariki da'ita ma ta dawo ribar barikin kenan. To kinji zancanne Qasimu ya tareni dashi, kinga dole mu jima. Zaman garinnan fa gagarar hatta iyayenta yayi, sai Azare suka koma da zama, mahaifinta kunyace ta jama'ar gari tai sanadiyyarshi. Yanzu ma bayan Magriba zamu shigo dasu nan mu tattauna. Bai kamata mu ƙyale Abdulƙadiri faɗawa halaka ba, zamu iya iyacin iyawarmu, dan ganin mun daƙile wannan nema" Shiru nayi ina jujjuya lamarin gaskiya. Sabida dole abun dubawane. Amman me muddin ta tuba ai zai iya aurenta. Sai dai abun tsoron dake tattare da aure, yana da yawan gaske gaskiya. Ajjiyar zuchiya na ja tare da saukewa. Amman mijinyawa in dai da gaske yake sonta, kuma itama da gaske take ta tuba, zata yi zaman auren, ai tamkar jahadine wannan ko?" "Tutar so wannan gaskiyane. Amman shin wa yasan zuchiyarta ne wai. Sannan tafa jima a bariki kina ganin ta dace da Abdulƙadiri kuwa anya? Ni tsoronmu shine sha'ani na tarbiyyarta. Karfa azo ana ɗan daka ce ba'ai ba ni shine damuwata. Shi Abdulƙadiri harma ya fini sanyi da sauƙi. To yana zaman zamanshi kar yaje ya ɗakko kara da kiyashi. Kai ina Tutar so bama zamu amince da wannan lamari ba sam" Haka dai mukaita tattaunawa har saida akayi la'asar ya ɗauki kwanonnan ya fice dashi. Ni kuma na fito na soma haɗa itace zan ɗaura sanwar dare. Tuno Baraka yasa na fasa. Ai ko shida na yamma sai ga tuwon shinkafa da miyar kuka harda ɗanyen soyayyun kifi, suyar fulawa, da gani na masu siyarwane aka siyo ta watso mana biyu. Bayan magriba su Abdulƙadiiri suka shigo, nan sukaita tababa. Suna kwatanta mai, yana runtse idanunshi, shima yana kwatanta musu, Halima ta tuba, ta shiru. "Ta fa tuba, in ba'a aureta ba ruwa zata koma. Ai laifinta tsakaninta da mahaliccinta ne, shi yace yana ma bayinshi wanda su kai tuba na gaskiya gafara. To me yasa ba zamu mance komai ba. Mu matsalarmu shine, ko mutum ya tuba, bama iya dena kallonshi da fentin da yaima rayuwarta na baya. Ku tausaya mata mana. Tunda kuka ga Halima a gida ai ta tuba ne." Mijinyawa yai carab yace. "Ai bafa dole sai kaine kaɗai zaka aureta a samu yadda ake so ba. Ya idanunka suka rufe ne haka Abdulƙadiri? To ni dai Magawata ban yarda ba, ban yarda ba, ba kuma zan yarda ba wallahi." Qasimu shima ya cabke, suka buga shima dai ya buga, har yayi zuchiya ya fice ya barsu. Shi ya kafe yana son Halima aurenta zai yi, daya kammala gininshi ma kuwa. Suma sun kafe kai da fata akan basu amince ba. Haka dai akaita jiƙawa ana matsewa har ranar komawa asibiti yazo, kuma a ranarne zamu soma bin matakan ɗaukar yaro a gidan marayu tamkar yadda muka tsayar. Sassafe muka ci ɗumame da ruwan kokko sai Bauchi, amman da zummar zuwa makaranta ni na fita. Tun Juma'a na riga na ɗauki hutu. Ko da muka shiga Bauchi asibiti muka wuce kai tsaye kawai. Ni dai gabana sai bugawa yake yi dim_dim_dim matsala kam tabbas akwaita. Jiya dana kwanta nayi wani irin mafarki wanda nake zargin yana da alaƙa da sakamakon da zamu ji na asibiti. A jikina nasan sakamakon ba zai zama mai daɗi ba. Mrs BUKHARI Mu kwana anan sai zuwa gobe in mai dukka ya amince💪🏼MRS BUKHARI
Chapter 9 · 0% Book details