Sashe 47
Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da hankali sai a baku yaro ku mai wanka ko? Baku isaba to kunji" Ni wallahi wankana na dingayi, jikina na wani irin mazari makaraina na shirin tashi. Ni wannan masifa dame tayi kamane. Ina jin Luba na ta ban haƙuri ita da su Halima. Wallahi cikin ƙanƙanin lokacin ɓarayina ya cika maƙil da mata, harda maƙota. Azgar ɗinma har an gama mishi wankan fa. Ga ruwan samannan duk a kansu yake sauka. Muryoyin su Yaya Salihu da mijinyawa Babba, da mijinyawa, dasu Qasimu dama sauran da ban riƙe muryoyinsu ba nake ta jiyowa. "Kuyi haƙuri Nanno wannan fitina a barta haka. Tunda basason wankan a bar musu ɗansu. Mijinyawane ya nuna musu tun fil azal danginshi basu da martaba. Da ba dan haka ba, hakan bama zata faru ba. To tunda naka shi ke ba da kai sai ayi haƙuri. A barsu da abinsu. Ai duk wani sha'ani in aka haɗu Mijinyawa da matarshi to dole sai sun nuna isa" Yaya Salihu kenan wanda ya kamata ace ya yayyafama ƙura ruwa, saima ya zaɓi tayar da'ita ta bule kowa. "Aa Yaya Salihu kar kace haka. Wannan rikicin na matane. Magawata babu ruwanshi. Mu fa hayaniyace muka ji tayi yawa shine muka ce bari muzo. Magana ta domin Allah babu ta inda magawata ya nuna danginshi basu da kima. Tunda basason wankan a haƙura dan Allah. Kuma ai ba'a kyauta ba, da aka kasa zuwa a duba Hindu a gida ko a Asibiti. Mufa faɗama kanmu gaskiya. A cikin gidannan abubuwan da akema Mijinyawa sun wuce misali. Kun wareshi tamkar ba ɗan gida ba. Duk abinda zai yi yana tsoro a ɗarare yake yi. Saɓanin Nawats da zai yi komanshi gaba gaɗi shi da matarshi. " "Dallah rufa mana baki. Ai kai ko kisa abokinka yayi kana bayanshi. Shima ai waremu yayi shi yasa. Uwatale kuma ai jininmu ce dole mu sota sama da Hindu. Nanno ku tawo muje a barsu da halinsu. Hindu dai ba zata je wankan ma gida ba tananan anan ƙauyen, abinda yake damun iyayenta kenan. To wallahi babu inda zata je tananan" Cewar Yaya Jamila da yanzu naji muryarta. Murmushi kawai nayi. "To tunda kece mijinta ko uwarta da ubanta ai dole. Ku ku fice mun da gani kafin in muku ɓarin makauniya wallahi" Akaita rikici, ɗauki babu daɗi iri da kala. Na gama wankana fes na fito babu wanda na kalla, nayi shigewata ciki abuna, Luba dake tsaye na jawo muka shige ciki an barmun yaro shi kaɗai yanata kuka bawan Allah. Ɗaukan abuna nayi na saka mishi umma. Babar su Qasimu ce ta dinga basu haƙuri, tana ba Innah haƙuri tana riƙeta, zata daki Innah Kulu harma ta zabga mata mari wai ɗankwalinta ya cire. Daga ƙarshe dai tace ita zata amshi wankan jaririn. Shikenan rikici ya lafa. Innah tace. "Ai Barakannan data nuna kulawarta, wallahi itace zata ci gaba da yin wankannan har zuwa lokacin da zamu tafi wankan gidan da ko mutuwa zasu yi sai dai suyi. Ni banƙi sanadin wankan gidanma auren ya mutu uban kowa ya huta ba. Banzaye gidadawa" Shigo da'ita Baba tayi. Su Nanno kuma suka rufu akan Mijinyawa sukaita zazzagarshi. Sai da makaraina suka tashi, Innah Yahanasu ma ta hau makarai, babu shirin gayyar ta watse harda masu fita da gudu akace. Dan wajen ruwan zafin dake kan wuta ta nufa, dole taron ya watse, ƙurar ta lafa dan dole. Amman su Nanno sun ƙullaci wannan hanasu wankan jariri da akayi gaya. Kuma rikici lafawa yayi, ba ƙarewa ba. Ni banma sake sanin inda nake ba sai washegari da safe. Ina buɗe idanuna naga mijinyawa a jingine a fuskar gado ga Qur'ani a hannunshi, yana ta gyangyaɗi. Motsinane ya farkar dashi. "Alhamdulillahi. Innah ta farka. Sannu Hindu kinji" Innah tayi saurin shigowa rungume da Azgar. "Sannu Hindu, kiyi haƙuri kema kinsan bazan iya ganin wannan iskancin in zuba ido ba. Ke da makaranki Allah ya baku haƙuri. Robona da tashin makarai nima na mance, tunanina ma sun rabu danine. Jeki gyara kanki akwai ruwan zafi a ciki. Kai kuma kaje kafin gyatumarka ta tsinema, sannunka da ƙoƙari" "Innah kiyi haƙuri da duk abinda suka faru. Da wanda ma zasu faru a gaba. Dan Allah ki dena tankawa, nasan rigimarnan ba'ayi komai ba. To kuyi haƙuri dan Allah" "Au haba ba'ai komai ba. To me jaki ma yace ayi tsere bare mai doki? Ni kaɗai na ishesu. Yi tafiyarka kawai yaro kar in sauke kwandon jalala a kanka" Zai kuma magana ta ɗaga mishi hannu. Dole ya miƙe a hankali ya fita. Ya sake rama sosai wallahi, gashi bama samun keɓewa yadda ya kamata. Haka lamura sukaci gaba da cukumurɗawa dai har ya rage saura kwana biyu suna wanda ayau muke sa ran zuwan Yaya Saratu, da Yaya Zubaina sune zasu soma yowa gaba. Har zuwa wannan lokacin sabida rigingimu, su Nanno da su Yaya Jamila sun sha'afa da tambayar wanne suna akaima Azgar huɗuba dashine. Hmm tsugunne nasan bata ƙare ba, tunda ranar raɗin suna za'ayi shelar sunan a ƙofar gida, tare da makaɗan kalangu. Tun bayan munyi wanka Innah da Baraka da Halima suke ta girke_girke. Tasa mijinyawa ya siyo kaji zata yi miya dasu. Banda ƙafar saniya da tace ya ƙaro. Sai Baraka na ƙullema kuɗin ta fita ta kai mishi ya siyo ya kawo. Innah babu ruwanta, aikinta shine ya siyo wannan, ya ƙaro wancan. "Hindu kunyi magana da Mijinyawa akan abincin suna kuwa, ya kamata kuyi magana sabida naga ƴan ɓarayin facalarki harsun soma tsintar shinkafa. Ko zamu jira zuwansu Yayane? Ya kamata da wuri asan me ake ciki. Tunda kinga nasan zamu yi namu girke_girken daban. Sannan shima ai zai kawo nashi cefanen ko?" Hakane Luba, ni kaina inata so in ganshi muyi magana, sabida asan me ake ciki. Bari anjima in ya shigo zan mai maganar muji me ake ciki. Wannan ciki Luba haihuwa ko yau ko gobe" "Fatana ma kar inzo in haihu a ƙauyennan Nanno tace dole ita zata karɓi haihuwata" Dariya muka sa tare da tafawa tabb. Baki da kirki Luba. Zaki haɗu da Nanno babu ruwana" Muna wannan hirar sai ga sallamar mijinyawa, ya leƙo yace. "Kuna nan abinku. Luba sannu fa. Tutar so zo muyi magana ga Qasimu zai yi magana dake, kuzo da Luba" Miƙewa nayi na kamo hannun Luba muka fito. Duk sai suka tusamu a gaba. "Qasimu baku ce komai ba. Ko dai in baku wajene? " Cewar Luba dake yinƙurin miƙewa. "Aa wallahi. Ai in zan iya shiga gaba akan sabgar Magawata. To kema zaki shiga gaba a sabgar Hindu. Ƙawance ba ƙarya bane. Hindu nasan abinda zamu faɗa ba daɗine dashi ba. To amman yaya zamu yi lokaci yanata ƙurewa dolene mu sanar dake halin da ake ciki dangane da batun abincin suna." Sai ya ja tunga, yana ta ƙunƙunda. Ni tuni na riga na bugo jirginsu. Na kuma zo iyakar wuya. "Kaci gaba da bayaninka Qasimu" "To Luba. Wallahi birni muka shiga ni da Magawata, da Abdulƙadiri mukayo cefanen kab abincin suna sabida dai a samu a fita kunyar baƙin birni. Har nama muka siyo mai tarin yawan gaske dan ya kai cikin robar fenti babba wallahi. Duk wani cefane munyi duk mun kashe kuɗaɗenmu. To amman me? Wallahi acaɓa na saukemu saiga Nanno da Innah Kulu a ƙwar gida. Nanno haka tace dole mu shige mata da duk cefanen ɓarayinta, ita abincin suna su Yaya Jamila ne zasu yi tare dana Uwatale sai dai a kai kwalla, a zubo muku abincin. Hatta kayan soɓo da ledar ƙullawa mun siya, akan mu sallameku da wuri bamu san shirinku ba. To kunji dai abinda ke faruwa. Kuma babu kuɗi a hannayenmu balle mu sake baku wani. Sai dai mu bari zuwa gobe, muga mai zata haifar. Kunya duk ta kamamu" A lokacin da za'a tsaga jikina ba za'a tadda jini ba. Da mai kukace ni da tuni hawaye sun gama jiƙamun fuskata. Amman sai naji kawai idanuna sun bushe kamar zasu dare halamune na ƙarshen maƙurar ɓacin raina. Jikina har rawa yake yi. Amman murmushi nake yi, mijinyawa dai sai na zame mishi suruka. Ina tuno irin surutan da ƴan gidanmu zasu yi akan wannan lamari. Innah ba bafa zata yadda ba, abunne bai yi ba sam. "Amman a gaskiya ba'a kyauta mana ba. Kuma ai ba'a haka. Yanzu Innah na jin wannan labarin ba ƙaramin gagarumin rikici zata tayarba. Kuma ko ta tayar dafa gaskiyarta, magana ta domin Allah. Ace shikenan mu duk yawanmu sai dai a dafo abincin suna a bamu, muna zaune jigum_jigum kenan. Me zai hana a bamu namu, muna fa da yawa sosai. Ko yau mutum nawa ne zasu zo" Cewar Luba. Ni ko tunda nayi gefe da kaina, ban juyo ba. "Tutar so kiyi haƙuri, ki tausayamun. Wallahi da kinsan firejar da take kaina nasan zaki yi haƙuri. Kinfi kowa sona, kinfi kowa yi mun uziri. Kinfi kowa fahimtata" Babu komai Mijinyawa, su yi babu damuwa. Qasimu ba komai. Watarana mai bada labarin wannan abun ma ba za'a samu ba. Ni zan shiga daga ciki" Leda Mijinyawa ya miƙomun babba da kaya sosai a ciki" "Kayan fitar sunane nayi miki. Babu dai yawa, amman nasan zaki yi alfahari dasu sabida ya fito daga hannun masoyinki" Ƙwarai kuwa. Nagode Ubangiji Allah ya ƙara buɗi, ya raya mana Azgar. Qasimu nagode. Kuma in sha Allah babu wani hayaniya da zakuji dangane da batun abincin suna" "To mungode matar rufin asiri. Luba mungode. Kaga taso mu tafi kafin azo a riskemu mu shiga uku" Figar hannunshi yayi suka fice, sai waigena yake yi. Har saida nayi mai halamu da idanu na abinda shi kaɗai yasan sirrin. Kafin naga ya sauke ajjiyar zuchiya. "Yanzu ya zamu yi da Innah Hindu. Amman dai wannan tsarin bai yi ba. Taya ma za'ace wai su Yaya jamila ne zasu yi mana girki ma, mu sai dai mu yi jingum_ jingum kenan? " Inafa Luba. Babu komai akwai wasu kuɗaɗena zan ƙirgesu in danƙama Innah yanzu. Abinci kam ko sun kawo ki tabbatar ba'a karɓeshi ba, a mayar musu da kayansu wallahil azeem bana so." Dafani tayi tace. "Hindu na sanki, kuma bazan bari a karɓa ba in sha Allah. Muje ki harhaɗo kuɗin a danƙama Innah su nuna a hannunta" Shigewa