← Book details Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 84

Sashe 52

Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mutu wallahi ƙauyawan banza da wofi." Nanno da kanta ta ja ragon, Innah Kulu tace Zakiya ta kinkime kwandon tumaturinnan. Nan rikicin ya samo asali. Nanno ta ja ƙafar rago, Innah Yahanasu ta ruƙe ƙahon ragon suka shiga jani in jaka. "Cika tsohuwa" "Bazan cika ba sai na tafi dashi" Zakiya da zata ɗauki kwandon tumaturinnan, Fannah sai ta dafe. Tana fincikan kwandon Fanna da Rayya na fincika. Nanno saida ta karya ragonnan ɓaras wallahi sabida yadda take ja, Innah Yahanasu na ja. Rago sai kuka kawai yake yi. An cika danƙam su Uwatale ba damane. Ai Innah saita saki ragonnan da Nanno da ragon suka tafi suka faɗi rigija. Innah tayi kanta ta kinkimeta, na faɗa muku ƙatuwace ta jefata cikin kwanukan wanke_wanke ji kuke kwakwaracam. Kuka Nanno take yi wiwi. Kanta saida ya daki gini ƙum, tana nunoni tana cewa. "Kina gani Hindu abinda duk akeyi akan ki ko?" Innah Kulu ma zata je ɗagata Yalewa ta tareta ta hanata wucewa ta ingizata taje ta daki buhun shinkafa da bayanta. Nan ta shiga haki. Ta damƙo Zakiya ta danna mata kai cikin tumaturinnan dake kwando. Da ƙyar su Anti suka ceceta, Yalewa ta daketa a ƙirji tab. Akaita rikici da dambarwa da su Yaya Jamila, da su Innah Yalewa da ƴan ɗakinmu, ragowar ƴan gida sai kallo, su Innah Abidah dai suna ta hanawane, amman Innah Mairamu wallahi gefe ta ja sabida wai ta riƙe Jamila ta fincike, wai kar ai mata illah tana fama da ƙafa. Matar Yaya Sojanmu itace gaba wajen ba da haƙuri. Sai maƙota dattijan da suke ta ƙoƙarin yayyafama ƙurar ruwa, suna nusar da Nanno hakan ba daidai bane. Koma menene da Mijinyawan akasa ya karɓo da kanshi duk ba ayi wannan rigimar ba, an riga da an zama ɗaya. Rikici fa yaita ƙamari, dokanni in doka ƙaƙas tsakanin dangina da danjin Mijinyawa. Kwandon tumaturi ɗaya ma an yi kaca_kaca dashi. Rayya ta jefa Uwatale kan attaruhu, sukaita murginawa, a ƙoƙarin uwatale na ceton ranta ne, duk tayi watsi da tumaturinnan, jama'a suka tattake. Akaita abu ɗaya, Jama'are ta ɗauka, al'umma a ƙofar gida tamkar ana yaƙi. Wannan rana tana daga cikin ranakun da bazan mancesu ba abadan, tana cikin ranakun baƙin ciki, da jin kunya mai ƙarfi a gareni. Ba abu bane mai sauƙi ba, lamarine wanda bazai kwatantu ba, amman ku hasaso ace rikici da doki in doka harda suruka, ga Innah Yahanasu itama ta ɓalle rikici duka kawai take kaiwa, ya faɗa kan mai rabo. Innah Yahanasu da Innah Yalewane suka turasu waje, koma ince suka watsasu waje suka danna sakata a ɓarayin nawa. Nanno sai kukan mutuwa take yi. Maƙota dasu Shafa suna ta rarrashinta kamar wacce jaki ya doka da ƙasa. Duk wannan fa abun ina tsaye ni da Luba Azgar yana rungume a ƙirjina. Bakina ya kullene, na kasa furta kalma, da idanu kawai nake bin mutane nayi_ nayi in buɗe bakina na kasa, sai kawai na haƙura nayi shiru. Amman ta ciki zuchiyata ci take kawai da wuta wallahi. Ƴan gidanmu sai ƙus ƙus suke ta faman yi, sun harhaɗe kansu anata sharafin gulma dama itace ta kawosu, Nanno ta basu akan sari. Shikenan sai an shekara fin nawa duk wani taro da za'ayi suna ko biki, sai an jaddada labarin wannan rikici tamkar lokacin abun ya faru. Balle Aurena da ƙiris ake jira aji yayi targaɗe, sai gashi sun tadda karaya. Wannan abune da bai taɓa faruwa da wata ƴar gidanmu ba, ace tana da babban saɓani da dangin miji irin wannan ba, ace har ta kai ana faɗa harma da suruka a ciki ba. Sai akai na Hindu ya faru. "Aikin banza da wofi. Ke buɗemun ƙofarnan duk wacce ta isa ta sake shigowa, in bansa itace na gabɗeta ba wallahi. Ku kuma munafukan banza duk kunyi cirko_cirko sai ƙus_ ƙus kuke yi, an samu nayi madadin ku shigo ko ayi daku ko ku raba, aa kuna tsaye kuna ɗaukan rahoto. Ke kuma Abidah burinki ayi miki bayani ta yadda zaki samu abun faɗe da hujjarki. Kai tur Allah ya sauwaƙe." Innah Yalewa itama da yare take tata maganar tana zaginsu Innah Abidah, dasu Nanno. Abun baima Innah Yahanasu ba. Sakata ta zare ta fice babu ko mayafi a kanta. Yaya da Yalewa suka bi bayanta Nima dolena na fita, ko takalmi babu a ƙafata ga ruwa anayi. Ashe waje ta nufa, a ƙofar gida ta tadda Nanno ta tusa Mijinyawa tana kuka tana bashi labarin abinda akayi mata. Kuma cefane yace bashi yayi ba ashe shi yayi. Yana kan rantsuwar bashi yayi ba Innah Yahanasu ta isa wajen. "Kai kayi mana yaro faɗa mata gaskiya, ita gaskiya ɗaya ce, ko babu hakkin wannan a wuyanka ne? Sannan wallahi ke ki kiyayeni ina faɗa miki kenan. Muddin ƙafarki ta sake takowa ɓarayin Hindu da sunan neman fitina, wallahi saina ɓallaki kamar yadda kika ɓalla ragonnan. Tunda na lura ke ba tsohuwar mutumci bace. Madadin kece mai hanawa, aa kece kan gaba wajen ƙulla wutar rikici kina wai uwa, anya ma yaronnan ke kika haifeshi kuwa? ." Tana yi ne fa tana dungurema Nanno kai har sai da Yalewa ta ƙarasone ta shiga tsakani. Nanno ta wani fashe da kuka, tana girgiza kanta. Ni dai mijinyawa na kalla, ya dubi ƙafata ba takalmi, gani ba mayafi, ga ruwa anayi. Kawai sai ya lumshe idanunshi yana tausata ta idanunshi. A fuskata bazai iya karantar komai ba, kadaran kadahan. Kunyatace an riga da an kunyatamu, an kwaye mana baya, sai nake ji abinda ya tafasa to yama daɗe bai ƙone ba. Da ace bakina ya buɗe da su Jamila zasu yi mamakin maganganuna, Ita nanno uwace na barta a hannunsu Innah Yahanasu. Nanno sai girgiza kai take yi. Mijinyawa ya ɗago yama kasa ɗagowa sam. Qasimu ne yake ta ba da haƙuri. "Dan Allah ayi haƙuri. Nanno, Innah ku yi haƙuri. Ke kam damo sarkin haƙuri Hindu bamu ma da kalma, Allah yai miki albarka. Innah ku shiga da'ita ruwa sai taɓata yake yi, ga babu takalmi bare mayafi a jikinta." Sai lokacin ma suka ankara dani, da ƙyar ya lallaɓasu Innah Yahanasu muka shigo ciki, nanma sai da ta bangaji Nanno ta kusan faɗuwa, Qasimu ne yai saurin tareta. Innah na riƙe dani tana ta faɗa. Ni dai basu ji ko tarina ba. Ɓarayin nawa shiru ko tari ba'ayi, kowa yayi jigum. Inaji ina za'ace ƙasa ta tsaye in faɗa da yafi mun. Illahirin kunya. Baraka ce ta shigo da ƴan matasa suka ɗauki niƙa kayan miyanma saida aka kuma wankewa. Tumatur kwsndo guda anyi asararshi shi kam. Innah Yahanasu tace wasu su bi Baraka gidan yayi kaɗan. Ɗuuu suka bita, su Innah Abidah dai suna falo su huɗu iyaye. Sai su Khadija a ɗakin ajjiye abinci. Su Yaya kuma sune zasu kasance a uwarɗaki tare dani. Amman suna tsakar gida. Ni kwantawa nayi na rufe idanuna kawai. Luba na gefena tayi tagumi kuka take yi kamar ranta zai fita. Yaya ma tayi kuka sosai Anti, ce tai ta basu haƙuri dai. Sai tashi nayi naga gari ya waye harya soma haske, kwana akayi ashe a tsaye a kaina. Da magriba rikici da dawo sabo, sakamakon dangin Nanno da suka zo, ai labarin abinda ya faru shi ya tunzurasu, nan akaita ɗauki babu daɗi, ni kuma magashiyyar a sandare ma aka shigo dani, ina ihu da fiffusga, wannan kenan. Ga ƙamshin girke_girke ina jiyowa da hayaniyar mata a tsakar gida. Makarai sun yi nasu aikin. Wainar duk da aka ƙarasa toyawa bani da masaniya. Yaya ce ta shigo da kaskon Turaren wuta. Innah Abidah ta biyota da babban buhu shaƙe da kayan barka. Khadija na biye da'ita da wasu kayan a leda. "Jiya husuma yasa ban samu damar damƙa muku kayan barka da dangi da ƴan uwa suka bayar ba. Kai munja galala jiya, ni dai wallahi ban yi bacci ba. Ke Saratu kirawo Yalewa dan Allah banda Yaha ni fitinarta ta isheni , jiya raba dare tayi tana mita. Bamu san yau mai zata haifar mana ba. Dan dangin mijinnan naki a shirye suke. Yaya bata ce uffan ba ta fita. Bata dawo ba sai da shayi mai zafi, ta zaunar dani.. "Sha Hindu kafin ki soma komai kinji" Banyi musu ba sabida inajin yinwa gaya. Innah Yalewa ce ta shigo. "Ga kayayyaki nan na barka wanda dangi, da ƴan uwa na cikin gida, harma da maƙota abokan arziki suka yi. Wannan kuma kuɗine gashi Hindu" Ta miƙomun su masu kauri. "Iyayenki mazane suka harhaɗa suka ce in kawo miki nasu gudunmawar kenan. Wannan kaya da suke daban gasu a hannun Khadija, Qazzafi ne yace a kawo miki nashi gudunmawar kenan, tunda har yanzu bai gaji da rigar zawayi ba. Ga buhun shinkafa uku, manja, farin mai, maggi, garin tuwo, man shanu, komai na gara dai gashinan daga dai Yayyu mazan gidan kafataninsu, kamar dai yadda aka saba wannan a kansu yake. Allah ya raya yaro da imani" Innah Yalewa tace. "Madallah Abidah angode sosai, saƙo ya iso munji daɗi sosai. To zan koma ina kan suyan Sunasun ne aka tasoni. Hindu ya kamata ki yi wanka ki shirya kafin a soma shigowa ai. Sannan kiyi haƙuri, babu komai" A banɗakin ciki nayi wanka, dole na fito a gabansu na gabatar da sallolin da ake bina. Ina idarwa Yaya tace. "Jini harya tsaya miki Hindu, ikon Allah. Haka fa Zubaina tayi kwana huɗu jini ya tsaya mata. Sanyi naji a raina. Shiryawa nayi cikin shaddar da mijinyawa yayi mun, Yaya ta miƙomun ɗan kunne da sarƙarta na gwal a lokacin babu kowa a ɗakin. " Saka wannan kimun loncin sabone na canja babu wanda ya sanni dashi" Dariya nayi na saka, nabi jikina da humra, Yaya taimun ɗauri na fito shar. Azgar shima yana kwance shar_ shar dashi yaci sabon farin seti na kanti mai kyau. Ɗaukarshi Yaya tayi muka fito falon anan na tadda su Innah Mairamu. Take kallo ya dawo kaina. Ƴan gida sai kallon wuyana da kunnena suke yi. Gaggaisawa dasu nayi, sai wani koɗani suke yi. "Su Abidah na can ɗakin sai ki shiga ku gaisa. Nima hutawa nazo yi, tun huɗun asuba muke tsugunne ana aikin abinci kala kala." Miƙewa nayi na fita tsakar gidan nawa. Ga tukwane nan a
Chapter 52 · 0% Book details