Sashe 37
Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Jama'are:.
Daga ƙofar gida Mijnyawa ya hango su Qasimu. Ganinshi yasa suka zabura suka nufoshi.
"Yanzu muke shirin shiga cikin Bauchi asibiti mu duboku, me ake ciki haihuwarce koko dai wani abunne? Ni wallahi nama kasa faɗama Nanno wai kace mun asibiti zaku je, kuma a tunanina ba kwana zaku yi ba. Jiya fa da ƙyar ƙura ta lafa, ga Innar Hindu tazo daga Maraya. Kai in kaga rikicin da sukaita yi ita da Nanno hmm. Yanzu ma basu daɗe da gamawaba Nanno harda kuka"
Kafin yace musu wani abun Mijinyawa Babba ya fito. Ganin É—an uwan nasa yasa ya nufosu.
"Yaushe kuka dawo, kuma kai haka akeyi koma ina zaku je ba zaka sanar ba. Ga can Innar Hindu sai ta da husuma suke yi ita da Nanno"
"Wallahi asibiti muka je can Bauchi. Kuma lokacin daidai Uwatale tana naƙudannanne Nanno na ciki. Hindunma ta sauka, an samu ɗa namiji shine nace bari inzo in sanar ma mata"
"Haihuwa a asibiti kuma a gidannan? Tabb yau na yadda baka gudun magana. Duk da dole aima uziri Hindu ƴar birnice ace dole dole saita haihu a gida tauyewane gaskiya. Yanzu dai kazo mu shiga mu samesu, Qasimu Abdulƙadiri sai kuzo ai a shiga daku"
"Kafinnan, ina zuwa zanje in samu Shehulle zan bashi saƙon wasiƙa ya kai gidansu Hindu"
"Ai ko kayi sauri, dan naga ya fito da motarshi tun lokacin sallar asuba. Babu mamaki sammako zai daka"
Ai da hanzari mijinyawa yaje wajen Shehulle, sai a wajenshi ya samu takadda da biro, ya rubuta wasiƙa ya bashi ya ba Innarmu.
Godiya yayi mishi, ya dawo wajensu Qasimu.
Suna shiga suka ci karo dasu Nanno a babban tsakar gida.
"Yauwa ga É—an halas É—innan ma. Ina Hindun take?"
Cewar Yaya Jamila, Nanno dasu Innah Dubu da Innah Yahanasu idanunsu na kan Mijinyawa.
"Tana asibiti ta haifi É—anta namiji jiya da daddare"
Innah Yahanasu ta É—aga hannu tace.
"Alhamdulillahi, yaro Allah yayi maka albarka daka É—auki matarka salin alin ka kaita inda ya cancanta. Allah ya raya"
Nanno tace.
"Ba shakka ka ɗauketa ka kaita asibiti, ni ina cikin gidannan, ina unguwar zoma wacce a kaf faɗin garinnan duk wacce zata haihu ni nan ake kira, surukan gidan kab ni nake karɓar haihuwarsu. Amman dake Hindu ita gwalce komai nata na musamman ne, shine ka ɗauketa ka kaita ta haihu a asibiti kalan su kashe maka ɗan da da ƴar ta zuchiya ta sameshi ko?"
Yaya Jamila tayi saurin caɓewa da cewa.
"Lallai a gaisheka Magawata. Hindu na juyaka yadda suke so su da danginta. Dama ga Babarta nan da aka turo ta É—auketa ta kai asibiti tazo tun jiya. Ashe an riga an kaita ma. To Allah ya raya É—an da aka samu"
Nanno dai fuu ta wuce ciki wiwi da kuka mai jiniya, su Jamila suka mara mata baya. Innah Dubu tace.
"Baka kyauta ba. Wannan abun da ka aikata babbane, kuma dole Nanno tayi fishi dakai. Da kai da Hindu bakwa son zaman lafiya. Jibi irin asarar gonarka da kayi a aurenta. Yanzu kuma ai shikenan tunda ta haihu dakai ai sai inda take so zaka zauna.
"To dama a inda ke kike so zai zauna? Wai ku kuma haka kuke da zuzuta ƙaramar magana ku ƙerata ta zama babbane? Kai mijinyawa ɗakko mun kayayyakina a ɗakin wannan mata, maza in kulle a ɗakin Hindu sai mu koma ka kaini asibitin inga uwata, da sabon miji"
Mijinyawa da Abdulƙadiri ne suka tafi ɗebo kayan. Qasimu kuma ya karɓi ɗan mabuɗi yaje ya buɗe ɓarayin, suka kawo kayan.
"Bara in É—an watsa ruwa sai mu tafi"
"To shikenan Innah, nima zan karɓo mata abincin da zamu tafi mata dashi, a ɗan ɗaukar mata zannuwa"
Cewar mijinyawa daya fita.
A ƙofar ɓarayin nasu ya tadda su Mijinyawa Babba dasu Qasimu. Wai ga Nanno can sai kuka take yi ƙaƙas wai an haifar mata jika a asibiti abun kunya.
Ko da Mijinyawa yaje, korarshi tayi tace bata son ganinshi ya fice mata kawai.
Jiki ba laka ya fito.
"Sai haƙuri dama munsan za'a rina. To dole a dubama Hindu fa.
Bari inma Baraka Magana ta haÉ—o abinci sai mu je asibitin tare ai."
Mijinyawa Babba bayan Qasimu ya tafi tawo da abinci yace da É—an uwan.
"Kasan uwatale ma jiyan ta haifi namiji, bana an samu namiji, sunan haÉ—awa ma za'ayi. Zanso suma asa musu Nawata da Magawata ko me kace?"
"Aa akwai sunan dana zaɓa mishi harma nayi mishi huɗuba dashi gaskiya. Sabida ai banma tuno komai ba, kuma bansan Uwatale ta haifi namiji ba"
"To ai shikenan babu damuwa Allah ya raya mana. Batun mahaifar yaron fa, ka tawo da'ita nanne za'a burne kusa da namu, kasan na yaran gidannan ma duk a waje É—aya suke.?"
"Ai ni na burne a can, sabida da daddare ta haihu, in nace zan bari saina tawo da'ita, warima zai ishi kowa a mota"
Kai yake ta girgizawa, yana jinjina girman rikicin muddin Nanno ta kuma jin wannan magana.
"Nima bari in shiga in sauyo kaya sai muje"
Tare da Abdulƙari aka barsu.
Basu jima ba, saiga Qasimu da Baraka, da kulolin abinci an ƙulle a ɗankwali, sai filas ɗin shayi.
Innah Yahanasu ce itama ta fito, da ledar kayan Hindu a hannunta, ta sha lafaya fara sol. Mijinyawa babba bai fito ba.
Qasimu ko da yaje kiranshi, sai cewa yayi Uwatale jikinta ya É—an tashi, suje zai biyo bayansu.
Haka suka hau acaɓa zuwa tasha, daga tasha suka hau motar Bauchi.
Mrs Bukhari.
Sai mun haÉ—u zuwa gobe, son so💪ðŸ¼MRS BUKHARI
..........
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JVdGBW8N6iFFBHyPGYXdrF?s=sw&p=a&ilr=0
*Kin Dade kina neman Adashin gatan da zaki shiga ki rika Tara kudi kadan kadan ki kwashi idan nace Miki kaya hajiya ta ina nufin komai ga Anty zee nazo muku da Tsarin adashi ki rika Tara kudin ki kadan kadan ki kwashi duk abunda kike so, akwai bangaren kayan sawa na Yara Dana manya, akwai kayan kitchen, akwai sarkoki ,takalma , jakuku Nan Yan gayu, mayafai dadai sauran su me kuke jira maza ku shigo ku fara tari tun yanzu* 💃💃
Hindu:.