Sashe 15
Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ga Hindu ga Hindu, ga mai ciki, ga mai ciki. Kai tubarkallah jibi yadda kika cika ta sama, wallahi cikinne gashi duk kin canja" Cewar Innah Abida da take ƙoƙarin riƙeni, nayi saurin kaucewa, sai hannuna ta samu zarafin taɓawa. Hakan yasa dole tayi turus. Kayan su Akarami suka dire, Qazzafi ya dunguremun kaina ya fice. Akarami kuma ya sakarmun murmushi. Amman inata ganin tausayina a idanunsu su su biyu, to ko me ya sa oho. Jikina na kuma kallo ni dai banga aibuna ba, takalminne ma ni yake sani jin kunya kamar in nitse. Wajen Innarmu na ƙarasa na zauna. Gaishe da Innah Abida nayi, na juyo na gaishe da Innarmu. Kafin muka miƙe tare da Innarmu. "Salamatu ma ta zo hutu tana ciki, in kika huta kya zo ku gaisa da mutan turai, sannu Hindu ya ƙauye da mutanen cikinta? " Innarmu tayi murmushi tace. "Abidah kenan ke dai ba'a rabaki da magana. Ai ke da ganin Hindu kinsan ƙauye da mutanen cikinta lafiya suke, ga tsarabanan buhu guda, kya taya ni buɗewa ai." Ni dai ciki na wuce, inata kalle_ kalle kamar fa na wanke makaranta. Ko ina ganinshi nake haɗaɗɗe. Innarmu ta sake fenti harda kujeru da labulaye duk ta sauya, da kafet ɗin tsakiyar ɗaki. "Abidah sai rigima in bata yada zance ba ita dai bata jin daɗi. Ke kuma wannan wanne irin takalmine a ƙafarki kika sako kamar wata marar galihu, ko irinshi yake iya siya mikine. Sannan zaki tawo ba zaki sa kayan da ba'a sanki dashi ba, sai ki kama ki sako kayanki tun na gida, sabida iskanci ba zaki ɗinga kayan zuwa gida ba. Haka kike ganin inayi in zani maiduguri ne? Hatta ku ɗinnan ɗinki nake yi muku, wannan ai sai ki tsinkani, wai kinga yadda Abidah ke kallonki kuwa. Ga gidan fal jama'ar biki, gashi goben dai sunan Matar Babanku Lukumanu matarshi ta haihu Amaryace yayo" Ni dai shiru nayi akan batun kaya da takalmi, na dai yi barka. To ya zanyi, bani da wani kayan da zan iya sakawa in burge, saina akwati ko wanda na tafi dasu, ba ɗinki nake yi ba. In banda ɗinkunan ankon bukukuwan gidannan bana ɗinkin komai. "Kije ki ɗauro Alwala kizo kiyi sallah" Miƙewa nayi da ƙyar ina ɗan turo ƙirjina dana sa rigar mama ƙatuwa mai cike da soso nayi him. "Tubarkallah ga cikinnan harya bayyana. Kema cikinki irin ya Yayarku ne baya girma sai dai yabi umma, amman bakya jin daɗin yanayinki ne, naga fuskarki ta kumbura. Ayya sannu ciki haka yake fa." Ni dai fita nayi bance uffan ba, ina wajen alwala da wanke wankenmu su Qazzafi suka shigo. A ɗakinmu na samesu Qazzafi na magana da Innarmu sai kallona yake yi. "Innarmu ni sai naga Duwaf ta yi girma sosai tayi ƙiba, amman wuyanta ya faɗa, fuskarta kuma ta kumbura." "Bata da lafiya ne, ta samu juna biyune abinda duk ake ta nema" Abun almara da al'ajabi sai kawai Qazzafi ya durƙusa yayi sujudul shukur, fuskarshi fal fara'a da dariya. Ina idarwa na kalleshi ina murmushi. "Allah sarki ɗan uwa abun wuya. Qazzafi na Duwaf. Ina jin daɗin yadda baka bari Mairamu ta raba maka zumunci da Duwaf ba. Ina jin daɗin yadda baka yi fishi ba lokacin da Hindu ta nuna ita ba kai take so ba. Tayi hakanne sabida ƙiyayyar Mairamu a gareta. Kuma ko ni dalilin da yasa naƙi aminta kenan. Ni ba kanwar lasa ba, Mairamu ba kanwar lasa ba, abun bazai yi muku kyau ba." Shigowar Baba Sojanmu da sallama ne ya katse Innarmu. "Hindu kece a tafe, ina Magawatan yake to, ko ke kaɗai ke kullum kike zuwa, da bazai rakoki ku tawo bibiyu ba, ga biki za'ayi?" Sai nayi murmushi nace. Yaso zuwa ma Mahaifiyarshi ce ba lafiya shi yasa. Nice ma nace ya zauna, amman yace in dai jikin yayi sauƙi zai zo in sha Allah, sai mu tafi tare." "Ashsha to Allah ya bata lafiya. Zai zo ai ya sameni ba zaki koma ba har sai yazo, naji me ya ɗaukeni. In nayi fishi abun bazai muku daɗi ba, Nagoɗi ne yake ta tauyeni shi yasa har kuka kai tsawon shekaru har shida. Da yanzu kin gama karatunki komai da komai, ko a Bauchi gya samu aiki. To yanzu gaki da juna, shikenan in kika sauka sai a bani hujjar sai kin yaye ko kuma me? Qazzafi ku zama shaida inna juya Hindu da mijinta ba zasu ji daɗi ba. Akan wannan yarjejeniyar in nace a bani ɗiyata kar aga laifina. Ko gaban malamai naje ba zasu ce nayi laifin komai ba, sabida akan doron wannan sharaɗinne harna yadda ɗiyata tayi aure acan. Jibeta fa yadda ta zama ƴar ƙauye ji wani kwalli damamme a idanunta. Ku in akabar Hindu haka wallahi watarana ba ganeta zaku yi ba. A hakanma tayi daban da sauran ƴan uwanta. Hatta yaran Dogara sun fita kyan fasali. Infosiful in saka ido ina kallonta haka. Shi is not ibin ashaim ob ha sef, jus luk at ha, bilej gel" Ya dinga faɗa yana ruwan turanci, rabi da kwatan maganganunshi da turanci yake yi. Ni dai nayi zuru _zuru gashi ance bazan koma ba sai Mijinyawa yazo. Tabb karfa asirina ya tonu lallai ina cikin tsaka mai wuyar fita. A yadda Baba Sojanmu ranshi ya ɓaci, wallahi nasan ko shekara zanyi, to fa tabbas sai Mijinyawa yazo kafin ya barni mu koma. "To ya jikin naki bakya fuskantar wani matsala ko, kuma hof dai kina zuwa awo ko?" Naje, jikinne dai sai dai a hankali kawai kullum ba lafiya" Sai kuma ya sassauto ya shiga hira dani harma yana zolayata ko na kawo musu nono da fura. Kafin inci abinci Innarmu ta juyemun ruwan wanka na wauwatsa naji daɗi sosai. Koda na fito duk a babban falo na samesu, ina shiga naga Innarmu ta ajjiyemun doguwar riga ƴar kanti ta yayi sabuwa fil. Murmushi nayi, uwa kenan mai daɗi, wallahi wanda ya rasa kulawar uwa abun a tausaya mishi ne. Innarmu Akwai tsumi da tanadi, da dabara sosai irin nasu iyayen da. Man mai gurguwa wanda Innarmu take mai haɗin gargajiya na gyaran jiki mai sirri na shafe jikina dashi. Na saka wannan riga na yane kaina da mayafin kana na fito. Innarmu bari inje in gaishe da matan gidan, babu wanda yasan shigowata." Fita nayi na dinga bin lunguna ina kwasar gaisuwa, ƴan uwa da abokan arziki ƴan biki sunanan cike da ko wanne lungu, su kuma sai ƙaremun kallo suke yi Innah Mairamu ce tace. "Duwaf kema cikin naki irinna Saratu ne baya fitowa, sai dai yabi Umma. Gaskiya zamu je asha bikin suna damu jama'are. Ranar jama'are zata ɗauka gaskiya dan har waɗanda basu je ba lokacin biki yanzune zasu je, barinma yanda kika yi jinkirinnan. Ai su Khadija ma duk zasu je. Allah dai ya raba lafiya" Ni dai na fita inata saƙawa a zuchiyata, toh ni yanzu yama zanyi da jama'ar gidanmu ta yaya zan fita kunyarsu ni Hindu. Kuma naga alamar kowa cewa zaiyi zai zo gaskiya, ai wallahi ko dan gulma, da son jama mutum jarfa nasan zasu iya yin bus uku ma cike Wannan tunanin har na kammala cin tuwo ban bari ba. Qazzafi fa sai da Innah Mairamu ta kirashi kana ya bar ɓarayinmu, a hakanna saida ya turo aka aikomun da gashasshiyar kaza ƙatuwa taji yaji jan gashi ma malam. Take yawuna ya hau gudana, innarmu na tsittsinkawa yawu na ambaliya a bakina. "Ungo ci Hindu ko zaki ji daɗin bakinki, gobe zan karɓi girki nasan kina kewa ko, me kike son ci wanda kike kewa sosai" Margi, da masar safe ta kari." "Ohh gulma, masar da kusan dole kuke cinta, yau itace in kuka bar gidan kuma babu abinda kuke kewa sama da'ita. Ai shikenan Abidah zata soya kici ki ƙoshi Hinduwa ta" To Allah ya nuna mana. Innarmu ba'a turomun yadin ankonsu Aminan ba, ko basu fitar da anko bane?" "Haba Hindu, a gidannan za'a iya biki ba anko ashe? Sun fitar da kala biyu, atampa da shadda. To Yayarku ta fitar muku da wata atampar, sai kammala ƴar senegal a madadin shaddar. Har an ɗinko dake ma, nace in kika zo kya biya kuɗin. Ko kuma ki barshi kawai na bar miki kuɗin. Amman ki sani sutura na da mahimmanci, kina ɗaukan albashinki duk wata, ki ɗan dinga siyan suturu mana, dasu takalma ki adana abunki sai in zaki zo gida ki saka. Abidah fa bata dena kallonki ba har saida taga kin saka wannan doguwar rigar, a tunaninta fa da'ita kika zo. Sannan in zaki tafi zan siya miki zannuwan jego falle_falle ki tafi dashi, kuma ki daure ki tanadi kayan zaman bakwai masu kyau. Kayan fitar suna kuma zanga yadda zanyi, ko Yayunki maza sa yi miki a ɗinka miki su daga nan, sai dai kawai ki saka." Ni dai nayi shiru kawai, ina jinjinama jarumta irinna Innarmu. Duk yadda nake da jarumta, Innarmu ta dokeni. A ranar Innarmu ta barnine na huta, nayi bacci a ɗakinmu mai cike da tarihi, ga fanka sai hurani take yi ni'ima takota ina ga wutar nefa duk inda na juya zanga haske, ga ba sauro sam, ba haushin karnuka. washegari da sassafe sai ga Yaya Saratu, da Yaya Zubaina sun zo mu gana kafin su wuce wajen aikinsu. Doya da ƙwai da miyar hanta Yaya Saratu ta kawomun, da ruwan shayi mai kyau. Kulolin data zubo abincin da basket ɗin da ta sako kulolin duk ababen kallone. Yaya Zubaina kuma farfesun ƙafar sa ta kawo mun, da biredi mai laushin gaske, ƴan uwa abun wuya, masa suka zuba a kwano ko wacce a gurguje ta wuce wajen aikinta. Ina zaune a falo ina shan farfesun ga kular a gabana, Baba Sojanmu ya fito ya zauna a falo tare da kunna tv dan soma sauraren labaran tara. "Hindu zo ga masar na kwashe ki zo ki zuba" Cewar Innah Abida. Da sauri na miƙe, zuba farfesun nayi a kwanon da nake ci na miƙa ma Baba Sojanmu, ya karɓa tare da jinjina mun. Ina fita Salamatu na fitowa daga ɗaki taci adon sufa, wuya da kunnenta duk gwal jiki duk hutu, ƙasan wuya duk madara. Ficewata nayi naje na ciko roba da masa guda