← Book details Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 84

Sashe 64

Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Mijinyawa:.
"Ai sai ka shigo kazo mu je kayi mun bayani.
Jibi yadda mahaifinta yake maka tsawa. Iyayen arziki ne zasu zo su É—auki É—iyarsu babu gaira babu dalili."
Wucewarta ciki tayi.
Qasimu dake gefe ya dubi mijiyawa.
"Kar ka faɗa mata sabida karatune, ƙurar buleka zata yi. Ka kafe akan batun komawa birnine. In taƙi amincema ka tattare muku suturarku kabi matarka, kaje ku rayu. Ka dinga zuwa kana neman yafiya. Ballema kaje ka fito muje mu samu Kawu mu zauna. Dole a dubama wannan baiwar Allah.
Ji yadda mahaifiyarta ta damƙa mata Asama'u ta rungumeta a jikinta. Magawata kar kayi wasa da lamarin Hindu, da lamarin karatunta. "
"Kazo muje tare Qasimu. Nanno a fusace take sosai"
Qasimu ya dubi mijinyawa yace.
"Muje to ya zanyi. Inma dukanne a kashemu tare"
Shiga suka yi, suka tarar anata tattauna zancen. Anata gutsiri tsoma.
A zaune a kan gadon bono suka tadda Nanno tayi shiru.
Zama suka yi a ƙasa.
"Nanno kiyi haƙuri dan Allah ki barmu muma muje birni mu zauna. Kamar yadda abokin tagwaitakata yaje. Ada nayi zaton dukanmu ne bakya so mu bar gabanki kamar yadda kika ce. Amman tunda Nawata ya soma gini baki hanashi ba, ya kwashi su Uwatale zuwa birni baki hanashi ba. Me yasa muma ba zaki barmu mu tafi ba Nanno? Ki duba nima aimun adalci, wannan alfarmar kawai nake nema a wajenki. Sannan in akwai wani laifi da Hindu tayi miki, ko ni nayi miki, ki faɗa mana a shirye muke mu baki haƙuri mu nemi gafararki'
Sai ya ja fasali. Qasimu yayi gyaran murya yace.
"Dalilin zuwan iyayen Hindu su tafi da'ita Nanno shi kuma. Akan batun komawa birnine. Tunda dama Mijinyawa yace musu zasu soma zama ananne kafin daga baya su koma birni. Tunda a birnin suka haÉ—u, shima kuma yana samu sosai akan sana'ar lemunshi da yake yi acan.
Da wannan iyayenta suka yarje musu suka zo Nanno. Magawata ya riga Nawata shiga birni. Kuma a birni yaso ya zauna kece kika ƙi shine ya ba iyayen Hindu haƙuri, akan su bari zai rarrasheki in yaso Allah bashi daga baya sai su koma birnin.
Kinji wannan dalilinne yasa, da suka ji labarin ai Yayanshi ya koma birni, to shine suke ganin danme shi da yayi alƙawari zai karya alƙawarin. Waima misali in bakya so su zauna a wani waje daban. Ba sai Nawata ya basu waje duk su haɗu su yi zumuncinsu ba. Ga Uwatale ga Hindu"
Magawata ya É—ago ya dubi Qasimu.
Qasimu ya É—an mai nuni akan ya kwantar da hankalinshi, a dai je a hakan.
"To kinji Nanno. Kuma in suna taren hankalinki zai kwanta sosai _sosai, ki duba wannan lamarin dai ayi adalci. Ke Uwace, ki duba a duba wannan al'amari"
Shiru tayi tana kallonsu, sun jima a haka kamar ma ba zata ce uffan ba. Maganar shiganta yayine, ko yaya dai oho.
Shigowar Yaya jamila kusan za'ace shi ya tarwatsa komai.
Kafinma ta zauna ta yaɓa mayafinta a ƙarfen gado maulidi, sai zufa take yi.
"Sannu Qasimu wato kaine bakin Magawata ko? To da kake cewa a barshi zuwa birni da matarshi. Ita Nanno duk yaranta majiya ƙarfin sai su kama hanya su tare a birni kenan. Wa zai lura da'ita to."
"Kema kya faÉ—a ai wannan yarinyar.".
Cewar Nanno wanda ada fa ku gane bata ce komai ba.
" Haba Yaya Jamila, naga ga manyan yayu a cikin gidannan. Yanzu kamar Yaya Salihu, da Yaya Garbati, da su Muttaƙa, da du suke gidannan basu isa kula da Nanno ba har sai Magawata. To ke kanki aikin me kuke yi ke da Yaya Zakiya, da ba zaku kula da Nanno ba ga baki ga hanci. Ga su Shafa, Tsahare, gasu innah Dubu.
Koni nan bazan kula da'ita bane. Ko ko dai sai shi Magawatanne ƙwararren wanda zai iya kulawa da'ita, ko aikinshine shi kaɗai ne? Mu dinga cizawa ana hurawa"
Mijinyawa yace.
"Kuma naga da can a birnin dai nake. Nawata ne ma yake shiga ƙauyuka ko yanzu ai a tsakanin Bauchi da Gombe nake. A cikin gidannan ma nine kaɗai na soma shiga birni"
Qasimu yayi carab yace.
"Ga wani gidan gonan da Maigidanmu ya buɗe a can Kano ɗin. Kanonnan ko ba Hindu fa aikinmu ƙarfinshi ya koma Kano, da Gombe ne. A duba wannan lamarin yarannan a sakar musu mararsu su yi fitsari ai inaga zaifi. Ko kuma shima Nawata ya dawo a kula da Nanno tare kawai. Tunda ai kowa ladannnan yana so. Kuma naga Nanno fa gadagau take da lafiyarta, kullum tana yawon karɓan haihuwa ko ba gaskiya ba"
Nan Yaya Jamila ta hayayyaƙo musu. Qasimu shima ya hayayyaƙo ta inda ya tsikara ba tanan yake ja ba, mafaɗacine sosai.
"Kefa ke kike jan duk wannan masifar. Kin kori kishiyarki, kina azabtar da yaran miji, mijinki kab garinnan kwatancenshi akeyi. Yadda yake ɗaukan miki talle kasuwar ƙauye_ƙauye. Asirce_ashircenki fa duk an sani a ƙauyannan. Kallonki kawai akeyi. Shi yasa ma ake tunanin wai ko asiri akayi yima Magawata. Abinda mutum yaima na wasu ne kawai baya so ayo mishi. Ni wallshi gaskiya ɗaya ce"
Yaya Jamila ta shiga cashe Qasimu, bil haƙƙi yake ramawa ƙaƙas.
Har saida Innah Dubu ta leƙo.
"Kai gidanku da wannan sa'insar, yayar taku kake ma wannan ɗiban albarkar. Itace uwa yau in ƙasa ta rufe ma Yaya idanu fa. Shin bakwa bin komai a hankali ne. Yau ga shegantaka noma da babbar riga. Wai batun tallarnan da Ubale ake cewa yanayi da gaske ne kenan Yaya?"
"Ahh da gaske ne. Har tsokanarshi fa akeyi. Ubale akwai bashi ne? Sai yace Jamila ta hana bada bashi, kuma ta ƙirga"
Cewar Qasimu daya kwanto kura.
Nanno ta fatattakesu, tare da rantsuwar babu zuwa birni itace harda dukan ƙasa. Ta kuma cashema Innah Dubu dama ta saba.
Kai tsaye Qasimu ya ja Mijinyawa zuwa wajen Kawu. Suka tadda Kawu bayanan an gaiyaceshi wani biki na babban mai kuÉ—i da za'a gudanar a garin Kaduna, amman gobe zai dawo.
An yi an yi dasu su tsaya su sha fura, ko suci abinci ma, amman ina.
Mijinyawa bashi da sukunin cin wani abinci.
"Qasimu gobe asubar fari zan kama hanyar Kano in sha Allah. Ko da ban samu mafita ba, ai ya kamata ace naje naga halin da Hinduna take ciki. Nayi imanin hankalinta da tunaninta yana nan tare dani itama"
"Hakane to amman me zaka riƙa musu ta magana wanda har mahaifinta zai gamsu dakai. Ba zaka jinkirta Kawu ya dawo ba, sai kaga ma kayi tafiya mai cike da ƙwarin guiwa"
"Kayya Qasimu bari dai in soma zuwa tukunna. Wannan lamarin ai sai an yi yaƙi tukunna"
Qasimu yace.
"Hakane. Kuma kaga wannan Jamilan hmmmm kusan itace Nanno wallahi, sai Uwatale mitsiyaciya kenan. Kaje É—in in ka dawo sai mu sake komawa wajen Kawu. Ka rufe mata É—akinta da kyau kasan dai sauran Shafa nanan. Kuma dogon hannu gareta"
"DaÉ—ina dakai baka sakaya abu Qasimu. Jibi abinda kayi ma Yaya Jamila"
"Hahaha kyaleta zan kai da? Wallahi da nice da yayu irinsu haukace zan manna musu, inta tambotsan da takalata ma ba'aso ayi. Sabida kar inta tumɓele. Amman kai dake haƙuri gareka shi yasa, suke zuba kashi a kwanyarka suci. Jamilan me, dan a yayata tazo, sai mulki. Tayi a gidanta, tayi a gidana ina. In zaka gyagije wallahi ka gyagije"
Haka sukaita tattauna wannan matsala.
Sassafe mijinyawa ya fice a gidan.
Wajajen bayan azahar irin ukun yamma sai ga Mijinyawa ya shiga gidansu Hindu da sallamarshi.
Saye da yadinshi mai ruwan makuba, da hularshi tashi da ƙwaƙwa an ko ci sa'a bai sayo kwalli ba. Sai ragowar wanda ya saka jiya dake idanun nashi shima fa fes dashi kamar ba kwananne ba.
"Magawata kaine a tafe? Za'a rina, sintiri ya aureka kuwa, in ba kayi ma janaral abinda yake so ba"
Innah Mairamu ke wannan maganar a yayin da Mijinyawa ke neman gurbin tsugunnawa su gaisa.
"Innah mun sameku lafiya, ya gajiyarku ta suna? "
"Laaa ashe rabonmu tun sunan wannan yazo Azgar. Kai wannan suna munga masifa mai ƙafa huɗu. Ina Nanno sarakan ba da umarni? "
Qazzafi ne yace.
"Haba Innah"
Fitowarshi kenan. Hannu yasa ya É—aga Mijinyawa, ita kuma ta hau sosa hannu.
"Muje daga ciki, Hindun suna ciki ai"
Mijinyawa ya bishi suka ratse gidan. Ana tafe ana gaisuwa har zuwa falonsu Hindu.
Chapter 64 · 0% Book details