Sashe 56
Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bakine, dan rikicin Æ™in Æ™arewa yayi. Sai da Innah Yahanasu ta rakasu har Æ™ofar fita É“arayin baki É—aya. To dake gidan a cike yake. Yaran Innah Dubu sunzo suna, na Innah Akulu ma haka. Sai rikici ya É“alle, zagi in zaga tsakaninsu dasu Yaya. Wannan karon Æ´an gida sun taÉ“uka dasu akaita musayar zagi, dake sunga dangin Nanno suna da yawan gaske. Kunji wannan babin? An yi akan kayan ciki. Da aka kuma turawa a karo na biyu, su Falmata sun tarar har su Zakiya sun soma ma hanji kitso. Innah Yahanasu da kanta taje har É“arayin ta kinkimo bawon kayan cikin, tazo ta dureshi. "Kuci gaba da aikin Saratu. Wacce take jin kanta wuta yake fitarwa tazo ta É—auka, kamar yadda naje na É—akko" Aka gama wannan, sai maganganu da sukaita zagaye. anyi akan naman ragon suna sabida mu a al'adarmu a girki duka ake zuba naman a cinyeshi. Innah yahanasu tasa aka raba ragonnan uku aka ba su Nanno kashi É—aya a É—anye, kayan cikin ma aka raba uku aka basu É—aya. Nan rikici ya É“alle aka dawo da naman, aka mayar musu. Aka kuma aikowa. Sai da Yaya ta rutsa Shafa. "Wai menene dalilin dawo da namannan da kuke yi ne? " "Sabida soyawa ya kamata ace kunyi, mu a soye ake raba nama ba a É—anye haka ba. Sabida haka mu ba zamu karÉ“a ba, kuma wannan É—an naman a rago biyu, wa za'a ba, wa za'a hana?" A cewar Shafa. Yalewa da kanta ta mayar musu da naman. Ta faÉ—a musu al'adarmu karace ma akayi aka basu a É—anyen, sabida dai ba za'a basu abinci ba. Nan dai akaita rikici sun dai karÉ“i naman sabida sunce É—ansune ai yayi. Ana suna, ana hirar rikicin su Yaya Jamila. Ƴan gida an samu labarin adanawa. Innah Abidah ba damane, ta kafa ta tsare ita a tsakar gida ma take zaune kawai. Sai nishaÉ—i da fara'a sosai take yi. Sai Æ™us_Æ™us da Innah Mairamu suke yi. A wannan rikicin, sai ga Harira tazo suna, harda atamparta da rigar yaro itama, haka Halima, da Baraka atampa da rigar yaro, harda omo ana Baraka, Halima kuma harda sabulu sanda uku kore. Akazo rabon abinci, suka ga ana fitarma dasu mijinyawa abincika na alfarma tire_ tire manya. Ko wanne tire akwai dafadukan shinkafa, akwai shinkafa da miya, akwai tuwon shinkafa da miyar yakuwa, akwai sunasun da miyar kuÉ“ewa É—anya. Haka al'adar take, kuma a cikin babban tire aka haÉ—a komai da komai. Kamar na mutum huÉ—u, ko uku, ko biyu, in madaidaitan tiran robane, sai ayi kowa da nashi. A cikin ko wacce miya namane faca_faca kawai. Nama duk a abinci aka kididdaba, har Dandaru anyi ds cinyoyin baya biyu. Haka aka fice musu da tire kusan goma manya manya. Ga koka kola kiret É—aya aka wuce dashi. Nan kallo ya dawo É“arayina. Kuma matan malaman makarantarmu sun ssmu zuwa, an babbasu wannan kofuna sobeniya da aka tawo dashi daga gida, duk suna gani. Ga kayan fitar suna in sa wannan in sa wancan hankalin kab Æ´an gidan yana gareni. Musamman dana saka wagambarinnan, ta haskani, na fito da kyau. Kuma a lokacin na fito tsakar gida, rakiyan malama. Kunsan Allah leÆ™e har ta katanga. Uwatale kuwa, data fito firit muka ci karo da'ita a hanyar shiga É“arayinmu, kasa motsawa tayi. Ni dai wallahi har sanda nazo dokin Æ™ofa, dana waiga Uwatale na Æ™ame motsi wannan ta kasa, ta juyo ma ta kasa. Kai kawai na girgiza. Akan abinci ma da suka ga ba'a basu ba, an zuba an kakkaima maÆ™ota, ga su Khadija a babban tsakar gida suka zauna suna cin nasu, kuma dama neman fitinane, hatta su Innah mairamu babban tsakar gida suka fito, suka shimfiÉ—a babbar tabarma, anata cin abinci. Nama kawai baja_baja a abincin. Nanma sabon É“alli ya tashi. Æallin da hatta maza manya wallahi saida suka shigo raba wannan rikicin. Sunan dai bai yi armashi ba, rigima da hassadar dangin miji ta motsa Æ™aÆ™as, haka akaita dambarwa, innah Yahanasu kuwa babu damane. Ni kam dama tun bayan la'asar na soma jin wani irin sanyi kamar yana shiga É“argona, take na soma rawar sanyi. Sai Baraka aka turo da kayan barka na dangin miji. Sabida Innah yahanasu ta hana kowa shigowa, kujera tasa a bakin Æ™ofar tayi zamanta fa. Kunsan irin wannan rigunan na da can masu kala kala duk a jiki, mai gajeren wando, zaku ganta akwai ja a jiki, akwai yalo, akwai bulu , akwai shuÉ—i layi layi kun ganeta? To irinta har guda goma sha biyu, sai omo kwano É—aya, sai sabulu sanda biyar, da wata atampa ruwan kwara_ kwara. Shikenan kayan dangin mijin. Ni kuwa kayana saida aka cika bahun manya uku, maÆ™il_maÆ™il wallahi kamar za'a buÉ—e kanti. Haka aka wakilta su Anti suka kai É“arayin nanno, a lokacin kuwa ana kan ganin na uwatale bahun guda Æ™arami anata zuzuta goshin da yaron yayi. Dai _dai nan aka kai musu nawa, Nanno riris ba lafiya ma, ita kam bata samu ganin kayan ba ma. Idanunta a kulle sai hawaye kawai suke yi. ZazzaÉ“i fa riris ya rufeta matarnan abun almara. Haka suka É—akko suka dawo, muka dai Æ™arashe sunan babu armashi. Ruwane ma ya tsuge kamar da bakin Æ™warya, shikenan rigimar ta Æ™are kuma. Magriba na shiga aka kasa gane kaina sam. Washegari ma mager_mager na wuni duk aikace_aikacen da su Yaya suke yi da idanu kawai nake binsu. Dan jiya ruwa ya hana wanke_wanken suna. Abincin daya ragu da safe suka É—umama, shi suka ci, ragowar suka lodama Baraka Innah tace su raba da matan gidansu. Saida suka gyaramun komai suka kintsa komai washegari asubar fari suka kama hanyar Kano. Ƴan Maiduguri suka kama tasu hanyar. Gida daga ni, sai Innah Yahanasu, da Azgar Innah Yahanasu tana gaban murhu tana soya naman kai sabida busarwa take so tayi. Mijinyawa kuma yanata faman jidon ruwa. Ni kuma inata haÉ—a duk kayan da nake buÆ™ata a jaka, nawa daban na Azgar daban. Saida mijinyawa ya gama jidon ruwan kana ya shigo ya taddani, duk fuskata ta aune. Jikina babu laka sam, da Æ™yar nake iya É—aga hannuna, kaina da zuchiyata nauyi sosai. Anan muka zauna muna É—an tattauna abubuwan da suka faffaru marasa daÉ—i, wanda ni bana ma son tunosu sam. Tayani yayi muka Æ™arashe haÉ—a kayan yana yi yana ma Azgar wasa, shi baima san me ake yi ba, bawan Allah. Haka dai kafin gobe duk abinda ya dace Innah ta killace, ta killace mun. ÆŠakin kayan abinci ta gyaremun tas, kayan garata ta shigar dasu Kicin É—in falona tasa ki ta datse, da kayayyakin suna, manya manyan atampopin tace dasu zamu tafi za'a É—inkamun acan, É—ananun ma ta tsinci wasu. Harma ta cirema Baraka atampa da sabulun gib na wanka. ragowar kayan abincinmu anan É—akin da muke ajjiyewa ta barshi. Gandar nanma data soya a É—akin ta bari, tace mijinyawa ya dinga dubawa. Washegari da safe wajajen tara furob ya Æ™araso mijin Innah Yahanasu, ashe a Bauchi jiya ya kwana. Ai baima shigo ba, mijinyawane ya shigo yake sanar mana da zuwanshi. Shi da Qasimu suka fitar mana da kayanmu zuwa cikin mota. Ina saye da sabuwar lafayata da takalmina da jakata sababbi. Na kumbura, na aune sosai fa. Innah Yahanasu tana riÆ™e da Azgar ta runguneshi muka fito. Itama ta É—auki wankan haÉ—uwa da furob, jiya da daddare saida ta sake tusa lallenta ma. "Ga kin É“arayinta nan sai ka kula kaga da dukiyarta a ciki. Kar azo ana wallahi tallahi" "Aa kuje dashi, zan dinga kwana a gidansu Qasimu babu damuwa" Innah tace. "To shikenan hakan ma yafi. Da fatan dai zaka zo kafin ace ta dawo ko? " "In sha Allah zan zo Innah. Allah ya tsare mungode sosai." Wuf uwatale ta fito. "Komawa zaki yi ne Innah? " Wani harara Innah ta sakarma Uwatale ta ja tsaki kawai. Ta shiga mita Innah ce fa. Sai ni nace mata. Zanje wankan gidane ni saina dawo" "Wankan gida? To to shikenan sai kin dawo" Wucewa muka yi muka barta tana sosa kai. Da Æ™yar Mijinyawa ya shawo kan Innah akan muje inma Nanno Sallama. Ta dai ga mutumcinshi munje. Nanno dai cewa tayi.. "Sam ba da yawuna ba wallahi. Babu inda zata je ta zauna a É—akinta. Duk tatseshin da kuka yi bai isheku ba, sai kun tafi da'ita gida kun sake tatseshi ko tausayinshi bakwa ji, dubi duk yadda ya rame, hidimar da akayi a wannan suna, da irin suturun da yayi ma yarinyarnan na fitar suna, ni tunda ummana ta haifeni ban taÉ“a ganin irinsu ba. Ga wani irin suna babu kan gado. Ni tunda naji sunan yaron na kwanta jinya, kuna gani ba lafiya bace dani ba sam" Innah Yahanasu tace. "Shi mai aurenta da yawunshi ai. Ke Hindu wuce mu tafi kinji? Saida nace muku ai bazan zo ba. Ayi mace ke dole sai kin yi son zuchiya ko son kanki, kai tur subhanallahi" Ina, harma ta fice a É—akin. MiÆ™ewa nayi nabi bayanta muka fice. Naima su Shafa, da maÆ™ota da suka saba kafa majalisa a tsakar gidan sallama" "Au wai ashe zaki je wankan gida Hindu? Tabb Allah buwayi" Ku da bakwa wajen, In kun tanka, to nima na tanka. A zaure muka tadda Uwatale tana tsaye. Data ganmu ne wai take cewa aike tayi tana jiran yaron yazo ne. Ina isa bakin motar, ga mijinyawa ga Qasimu da AbdulÆ™adiri a tsaye. Sai ga Nanno ta fito, wallahi harda É—an gudunta. Ta riÆ™e hannuna carab wai bazan shiga motar ba. "Babu inda zaki je kinji na faÉ—a miki. Kai kuma yanzunnan ka bata umarnin komawa ciki" "Wallahi bai isa bada wani umarnin hana tafiyarnan ba. Ko ya yarda ko bai yarda ba sai na tafi da'ita. Bari kiga. Ni banÆ™i ma auren ya Æ™are ta bar wannan Æ™addararren gidan ba. Ke É—innan kinfi zaman Æ™auyennan zamewa Æ™addara a rayuwar Hindu" Zagayawa tayi ta miÆ™ama furob Azgar ta zagayo ta finciki hannuna, ta jani, Nanno ta jani itama. In Innah yahanasu ta ja, sai Nanno ta ja. Ga jikina babu laka sam, ni kaÉ—aima ji nake zan iya faÉ—uwa. Su Qasimu aka bari da ban baki. "Kiyi haÆ™uri ki barta su je, kamar yadda aka bar su Shafa, dasu Tsahare suka tafi. Kamar yadda su