← Book details Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 84

Sashe 13

Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 3 min read

sha ɗayan rana muka farka. Masar Bauchi na turara mana na dama mana kokko. Ni dai ni nake jan mijinyawa da hira, amman shi kam ya ɗauki damuwar duniya ya ɗaurama kanshi, abinda damuwar ba zata sauya ko wacce iriyar ƙaddara, ko jarabawa ba. Saima dai ta sake tura sabuwar matsala. To amman nasan lamarin yana da girman da ya kamata ace an yi tunani kam a kanshi. Koni daya fita saina zauna inata tubkewa ina warwarewa da kaina. Inna buga sai in kwashe na kasa haɗa komai. Tafe_tafe damuwa tai ta cin ƙasan ranmu, har rama muka yi, na shiga sabon ciwon makarai, kullum sai sun tashi, jikina ko ina a kumbure, ga tsami. Amman bamu kuma ta da zancan rashin haihuwa ba. Matan gida ni kam nawa sun ɗauka laulayine, dan babu laifi ina nuna yanayi na laulayi a aikace sosai. Har hannu nake sawa a bakina in ƙwaƙwalo aman dole inta sheƙashi. Gashi na zama kusan ɗanya har kaina saida ya kumbura. Gaga_gaga_gaga har ranar zuwana biki gida yazo. Na harhaɗa tsarabata, da duk kayana na kintsasu a jaka. Ɗan kunnayena biyun na saka a ƙaramar jakar hannuna. Mai sarƙar kuma na sa a wuyana. Nanno tayi faɗa kamar zata ari baki, akan ita ba za'a hau mata hanya da jika a ciki ba. Akace rashin sani yafi dare duhu. "Cikin da da ƴar da jiɓin goshi aka samu, shine zaki je ki jijjigeshi a hanyar Kano, koko mai kike nufi ne. Kai yanzu kana gani zata tafi sabida dai kai baka da kataɓus a cikin gidanka. Haka kaga Yayunka suna tafiyar da gidansu ne. Kuma sabida salo ace wai dakai zata tafi, yanzu dan zata je ganin gida sai kun tafi tare?" "Kiyi haƙuri Nanno Innarsu ce ta aiko tana son ganinta shi yasa, biki za'ayi a gidan. Ni kuma zan rakatane sabida yanayin hanya, kuma kinga ba ita kaɗai bace" "To ban yarda ba shanyayye, kaji ko nace ban yarda ba." Ai kuwa Nanno taƙi fur mu tafi tare da mijinyawa sai dai tasha ya kaini. "Kar ki manta da shirinmu, kinga yaci ace cikinnan ya fito, to a gida kuma ko kinsan tsumma za'a samu mai taɓawa ba kamar nan bane. Sai kiyi yadda muka ce ko? " Kai kawai na gyaɗa mishi ba tare da nace uffan ba. "Sati nawa zaki yi to?" Sati biyu yayi maka, ko sati ɗaya?" "To kiyi sati biyun banason daɗewar sabida kar su bugo jirginmu ne, da sai ince kiyi uku" Ba zasu bugo jirginmu ba. Ai akwai da yawan mata da ciki yake bin jikinsu, ko Mamansu, yadda nayi ma Mamana dole zasu gamsu nawa Mama yabi. Kai dai kafin in dawo ka tanadar mun gadalinnan, kar ka mance da batun itace, kuma ka zauna da shiri dana dawo sunturin Asibiti ya ganmu" Saida motarmu ta fita a tasharnan kana ya tafi shima. Gudu motarmu take yi, amman zuchiyata bata tare da gangar jikina, tunanukane fal zuchiyata. Takalmin ƙafata na kalla wanda na siya sabo, amman ba mai tsada yadda na sababa, ta fannin suturu bani da matsala sai dai fa nawa na gidane na sako masu tsada, gani da adani da tattali ni kayana basa tsufa gaskiya. Mota na saukemu a tashar unguwa uku sai na nemi abun hawa sai Na'ibawa. Ina sauka a ƙofar gida muka haɗu da Qazzafi shi da Akarami sun fito zasu masallacin magriba anata kiraye_kirayen sallah. Qazzafine ya suri buhun tsarabata ya wuce ciki yana ta kallona. Akarami kuma ya ɗauki akwatina, ni kuma ina riƙe da jakar hannuna muka ratsa gidan. Matan gidan duk suna ciki. Ni kam wannan karon na zaɓi saina huta zan bisu da ɗaya da ɗaya in gaishesu. Muna shiga falonmu aka kawo wutar lantarki wallahi sai naji tasirin wannan haske har a zuchiyata. Da Innarmu muka haɗa idanu taci kwalliya tana harɗe a kujerar dake falonmu da littafin turanci a hannunta tana nazarinshi. Mrs Bukharice
Chapter 13 · 0% Book details