Sashe 61
Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yi mun. Batun asibiti kuma, mun gama shan magunguna, allurai duk an kuma ma Mijinyawa. Muka koma akaita gwaje_gwaje shiru babu wani labari. Daga ƙarshe ma likitan cewa yayi ya sallamemu muje mu dangana. Ai kuwa shikenan muka burne wannnan sirrin. Ina ya Allah babu ya Allah. Har shekara ta zagayo cib Ranar asabar muka wayi gari da mutuwar Abdulƙadiri. Wanda shaidu suka tabbatar faɗane ya kaure a tsakanin Abdulƙadiri, da Halima. Kuma dama baƙin cikinta ne ya kaishi ƙasa ciwo yake yi kusan kwananshi bakwai a kwance ƙaƙas. Amman sai aka rurrufe lamarin mahaifiyarshi tace kada a ɓata mata gawar ɗanta, ai mai wanka a kaishi lokacine yayi. A ranar Uwatale kuma ta sauke cikin dake jikinta ɗanta namiji ta samu. Allah al hakim, wasu na kuka, wasu na murna. Wasu sun rasa, wasu sun samu, faɗuwar wani, tashin wani. Duniya makaranta a ranar da kai ka gama, a lokacin wani nata murna farawa zai yi. Wannan kaɗai ya ishi mai hankali tsoron Allah. Su Mijinyawa da Qasimu sun yi kuka, sun yi kuka har saida aka rufu a kansu anata rarrashinsu. Ita kuma Halima wannan ne yai sanadin rashin lafiyarta, har aka gama wannan makokin tana kwance. Tasan ta cutar dashi, kuma dai dasa hannunta wajen mutuwarshi. A haka aka watse aka barta da ɗiyarta. Su Mijinyawa ne suka ci gaba da ɗaukar ɗawainiyarsu. Ga Asama'u yarinya ce mai laulayi babu wuya ta kwanta ciwo, sai an dangana da asibiti. Inata saka idanu inji yaushe su Uwatale zasu koma gidansu, tunda dai an yi suna an watse. Sai nake ji a bakin Baraka, wai an ɗaga tashin tukunna dai da saura. Gaga_gaga_gaga_gaga. Ina zaune a ɗaki, nayi kwalliya shar, littafin hausa nake karantawa, hankalina ya tafi soyayya. Har wani narkewa nake yi a sakamakon yadda ake gudanar da wata iriyar soyayya mai sanyi. Allahn daya halicceni ina mugun son soyayya, da riritawa gaya. Shi yasa nake son kasa kasan indiya gaya. Azgar yana zaune sai wasanshi yake yi, yana surutai ya samu kayan wasan yara, mota da jirgi Baba sojanmu ne ya aiko mishi dashi. Da sallama Mijinyawa ya shigo rungume da yarinya a kafaɗarshi a tsumman goyo. Azgar ya tashi yaje ya ruƙunƙume ƙafafunshi. "Oyoyo Abbah" Hannu yasa ya ɗagoshi ya haɗasu hagu da dama a kafaɗarshi. Littafin na ajjiye ina kallonshi da yaran. Shima ni yake ta kallo. Saida ya sauke Azgar, ya miƙomun Asama'u. Hannu na miƙo mata. Ta kalleni, sai tayi dariya ta miƙo jikinta, na ɗauketa na ɗaurata a cinyata. "Ga yarinya na baki ita duniya da lahiri, na sanki da amana" Rungumeta nayi tsam a ƙirjina inajin son Asama'u na ratsani sosai. Na karɓeta Ubangiji Allah ya raya mana ita da imani. Mahaifiyarta fa?" "Kema kinsan ba zamu barma Halima yarinya ba wallahi. Tana gadon asibiti ma bata da lafiya, shine na nemi ɗaukar yarinyar gaskiya. Abinda zan iyama Abdulƙadiri kenan" Kunu na dama ma Asama'u, a baki na dinga bata. Bata da kuzari irinna yara, kuma gashi bata girma, jikinta babu ƙarfi alanƙosa haka take. Nanno yaje ya sanarma riƙon Asama'u ya dawo hannuna. Ai sai gorin haihuwa ya ɓalle, ta dinga tijarar haihuwa shiru daga Azgar shikenan. Ita wallahi, ita tallahi. A daren ranar da aka kawo mun Asama'u bamu rintsa ba. Jikinta yayi kau _kau da zazzaɓi, sai kuka take yi a hankali. Na kasa zaune na kasa tsaye. Goyota nayi na dinga jijjigata. Na sauketa na sakata a kafaɗa. Na jiƙa tsumma na dinga goge mata jikinta zazzaɓin dai ya sassauta. Mijinyawa shi ke taya ni sata a kafaɗa. Runtsawa bamu yi ba, sassafe sai asibiti. Zuwan farko aka bamu gado jikinta zafi sosai. Ashe baƙon dauro ne ke damunta ana bata magunguna sai ko ƙurajennan duk suka feso. A lokacin Mijinyawa bashi da kuɗi a hannunshi, duk sun ƙare a maganin Halima. Ni na biya komai na asibiti. Kwananmu uku aka sallamomu. Mun dawo gida mun tadda Uwatale na bin maƙota anata sallama. Jibi zasu tashi. "Inaga bari in jaraba zuwa yima Nanno magana, Allah bashi ta barmu mu tafi tare. Ni ko hayace sai mu kama Tutar so" To shikenan Allah yasa a dace, nima nafi son hayar. Fita yayi, ni kuma na dawo da kallona kan Azgar dake ba Asama'u ƙuli_ƙuli a baki sai tura mata yake yi. Allah sarki. Watarana da girmanku zaka ciyar da'ita abinci a baki na soyayya. Matarka ce baka sani ba" Ajjiyar zuchiya na sauke. Na shafi kan Asama'u ta juyo baki duk yawu tana ta mamular ƙuli_ƙuli tai mun dariya. Fuskarta duk saɓar baƙon dauro. Haka Mijinyawa ya shigo ya taddani ina wasa da yarana. Yadda na ganshi a sanyaye na tabbatar da matsala. Sai ban bi ta kanshi ba, naci gaba da wasa da yaran. A hankali Azgar ya sakko ya koma jikin Babanshi. Itama sai ta bishi duk ya haɗasu a jikinshi. Dogon wando na ɗakko na sanya ma Asama'u naji garin da ɗan sanyi, na sanya musu hulunan sanyi. Shiru Mijinyawa yayi da yarannan rungume a jikinshi. Uwatale ce take ta doka sallama daga can ƙofar shigowa ɓarayina. Fita nayi na sameta. "Dama sallama Nanno tace inzo in miki. Shan ruwanmu a ƙauyannan ya ƙare. Zamu koma birni mun barku lafiya, sai in mun zo ziyartarku kuma mazauna ƙauye. Amman kayana duk sunanan in mun zo anan zamu dinga sauka" Sai gatsine take yi, wai ita shegiya. To Allah ya tsare yasa ku koma a sa'a ko?" Bam na rufe ƙofata na koma ciki. Su Uwatale suka tafi muna kallo. Nan Mijinyawa ya shiga godon Nanno, amman wallahi ta kafe mai. Sai haƙuri yake bani. "Kiyi haƙuri ina jiran wani lokaci ne, in dai har bata amince da komawarmu ba. Zan ɗaukeki mu tafi kawai. Allah yana gani nayi duk wata biyayya daya dace. Ki ƙara haƙuri na ɗan lokaci kaɗan." Akaita cukumurɗawa fa. Harma Nanno tace in ya ɗaukeni ya koma dani birni bata yafe mai ba. Kuma saita ɗaga mishi Umma. A ranar na haɗe kayana, dana Azgar da Asama'u da tayi mugun sabo dani gaya. Nima inason yarinyar sosai kamar yadda nake jin Azgar ɗina. Na lashi takobin bazan zauna ba wallahi. Tunda Nanno bata da dalilin hanamu tafiya. Mijinyawa ya shiga damuwa sosai da sosai, yaita roƙona akan kwana bakwai kawai yake buƙatar in bashi kacal. To shikenan na baka, daɗina da gobe saurin zuwa" Munyi haka dashi da kwana huɗu kwatsam da safe misalin sha ɗayan rana, ranar asabar sai kawai muka jiyo muryar Baba Sojanmu a tsakar gida ana gaggaisawa. Zumbur muka miƙe a kwance daman muke, muna tattaunawa duk akan tafiyarne. Kafin in fito har sun shigo ɓarayina da sallama. Babu wasa ko wargi a fuskar Baba sojanmu. A sojanshi ya fito tamkar yana filin yaƙi. Kayan sojojine ma a jikinshi. Gabana ya yanke ya faɗi ras. "Innarmu, Baba Soja sannunku da zuwa. Ku shigo mana daga ciki" "No nid. Hindu nazo ɗauka mu tafi, tunda alƙawarin daka ɗauka ka saɓa. Ɗan uwanka da kace a baka taim in ya gama gininshi, zaku dawo birni yarinya ta shiga makaranta. Yanzu watansu nawa da dawowa birni? Naje zan kaima Shehulle wasika ya kawo muku, yake bani labari. I was shok, an safrais. I am dibli dis'afointent. I neba esfet dat furom yu, bot is ol Nagoɗis folt. Hi yu bilej gel go insait an girab yo tins" Ya dinga turanci yana zazzare idanu. Da ƴar Mijinyawa ya iya motsa bakinshi da zummar magana Baba sojanmu cikin tsawa yace. "Wil yo shotob an bi bilemful?" Saida hantar cikina ta kaɗa. Ɗaki na shiga a guje. Dama kayan dana haɗa ban suncesu ba nawa. Na yaran na kuma haɗawa. Innarmu ta biyoni har ciki. "Hindu yi maza kinji? Nayi juyin duniya da janaral akan abi a hankali yaƙi. Yanzu sai kawai aga mun dawo gida dake, me za'ayi tunani dan Allah? Duk da Mijinyawa ya saɓa alƙawari gaskiya. Ƴan uwanki sai samun ci gaban rayuwa suke yi kinga, amman ke ace har yanzu iyakarki fa sakandare. Ina wannnan abun zai yi mana kyau" Kafin ince wani abu Innarmu idanunta yakai ga Asama'u dake zaune a gado. "Wannan wacece Hindu?" Yarinyar marigayi Abdulƙadiri ce abokin Mijinyawa. Riƙonta ne ya dawo hannuna. "Allah sarki hakan yayi kyau. Lallai ta samu uwar riƙo tagari ba dan kin kasance tawa ba." Innarmu yanzu wannan gidan zan koma, to me za'ace musu innah koma dan Allah fa?" "To Hindu shima Mijinki bai duba mun ba. Dan ni za'a saka a matsala, Abida ma ta isheni ga Salamatu da yaranta sun kawo ziraya, shi kanshi Daktan yana ƙasar baki ga yadda yake musu facakar kuɗi ba. Jiya muka shiga Bauchi. Tun jiya yaso mu ƙaraso mu ɗaukeki, in yaso ma kwana a Bauchin tare. Motace ta ba Qazzafi matsala, shi ya tuƙomu yana waje" Baba sojanmu me ya buɗe labule ya ƙura mana idanunshi. "Wandaful" Ai ba shiri na rufe akwatin. Innarmu ta ɗakko Asama'u. Ni kuma na jawo Azgar da jakar kayansu. A ƙofa na dure jakar, na koma na ɗakko tawa. Na fito ni bamma samesu a tsakar gidan ba. Ƙofar na jawo na fito. A tsakar gida na tadda Innarmu da Nanno a tsaye. "Au tafiya da'ita zaku yi sabida wanne dalilin, yarinya na aure za'ace an ɗauketa haka siddan?" "Mijinta zai miki bayanin daya dace. Mu kam yarinya dai tamu ce ai ko? To mun ɗauki abinmu" Cewar Innarmu. "Aurenne ya ƙare kenan ko yaya, sannan da ƴar mutane zata tafi? " "Kusan hakane. Aure kam girgiɗi yake yi. Yarinya kuma ai bata akayi" Nanno ta girgiza kai tana almara. Kallona tayi tace. "Giringiɗishi wato kuma yau mahaifinki da mahaifiyarki, da abunda kuka ɓullo ma wannan yaro kenan, anata wahalashi tamkar kece mace tilo a duniya ko? To wallahi aure zai yi kina tafiya. Ke daga haihuwa ɗaya ma baki kuma ba. Dama shima wannnan ɗin da yaya ya samu. A cikin gidannan bayan haihuwar Azgar, saida ko wacce ta haihu. Ga Uwatale mutan birni tare kuka haihu, amman gata da goyonta na wata nawa ma" Dawowa Innarmu tayi ta riƙe hannuna muka tafi. Mijinyawa yana tsaye a gaban motarmu. Ta gabanshi na wuce na shiga mota, Innarmu ta zuba kayana a bayan but, ta miƙamun Asama'u na rungumeta, ita kuma ta shiga ta