← Book details Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 84

Sashe 32

Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ko? " Sosai kuwa Baraka. Allah dai ya saukemu lafiya shine kawai" Dariya tayi tace. "To ameen Hinduwa. Ga nan abincin bari in koma gida. Ya'u ai bayanan ya raka Babarmu ɓoto. Shi kam ma da damina ta wuce zai tafi almajirci, dama shayi ake jira ayi, kuma kinga anyi harta warke, yaro ya girma." Kai kawai na gyaɗa dan bani da ta cewa. Ko'ina da al'adarsu. Su sunfi gamsuwa su tura yaransu nemo ilimi a nesa, kamar yanda ake tura ƴan bodin na boko. "To bari in je uwar biyu sai da safenku" Bokitin tsarabar su Uwatale na juye mata komai a leda na damƙa mata, sai godiya take yi. Tsakanina da Baraka ai babu godiya alkhairansu baya misaltuwa sam. Tana fita bata jima ba sai ga Mijinyawa ya shigo. Abincin na zuba mana. Tuwon dawa da miyar karkashi bushasshe ya ko ji bushasshen kifi. Ci muke yana wucewa, amman hankali da tunanikanmu duk basa jikinmu ma. Ranar tafiyarsu Mijinyawa zuwa Bauchi yazo, ya tafi ya barni daga ni sai halina, daga kwanciya sai kwanciya. Nanno kullum saita zo dubani ko naƙuda ta tashi, harfa cikin dare turowa take yi azo a duba. Wannan damuwar saita ƙaru mun gaya, sati na zagayowa saiga mijinyawa yazo mun da mummunan labari kam cewar har wannan lokacin babu jaririnnan fa. Jikinmu duk a sanyaye gaya. Rubutu aka soma yo mun ina sha da shafawa Nanno tace. "Babu mamaki cikin ƴan biyune a jikinta, dan kuma shekara kuka yi tim a ciki, itama naga halamu shekara zata yi." To wannan hasashen shi ya ɗan riƙemu, har hankula suka sauka a kaina, masu jiran tsammani suka tura. Ta ɓangaren su Baba Sojanmu kuma nayi musu wasiƙa akan har yanzu haihuwa shiru, kuma munje asibiti sun bani wa'adi akan in wa'adin ya cika ban haihu ba to za'a ciro ɗan ko ƴar. A wasiƙar da Innarmu ta turone take tambayar ko a turo Inna Yahanasu tazo ta zauna dani. Ranar kwana muka yi muna canki cankar abinda zamu ce ma Innarmu a matsayin amsa. Da ƙyar muka cimma matsaya. Muka ce babu damuwa Nanno na kulawa dani, da Shafa Matar Yaya Salihu. Hankalinmu in yai dubu ya tashi fa jama'a. Tafe_ tafe _tafe har wata goma sha ɗaya ciki ji kuke shiru, Mijinyawa yaje gidan marayu yafi a ƙirga shiru babu labari harma dai mun sare gaskiya. Mun kuma yanke hukuncin zamu je kawai asibiti kamar yadda Hajiya Bara tace zata taimaka mana a bamu gawar jariri. Ina ya Allah babu ya Allah, abu har ciki ya shiga shekara. Wata ranar asabar wacce abadan ban isa mancewa da'itaba, koda hauka nayi bana jin wannan ranar zata gogemun a rayuwata. Ranace mafi zafi da tsanani a tare dani. Dama dai jiya banyi bacci ba, daga ni har goga naku. Makaraina sun tashi sunata buge_buge suna kururuwar da saida kaf ƴan gidan suka taru a ƙofar ɓarayina dan jin ba'asin abinda ke faruwa, da dalilin zuwansu. Nasan baya wuce baƙin ciki suka zo taya ni, na abinda ya samemu. Mijnyawa shi ya tsaya kai da fata a kaina, ba nuna gajiyawa, babu nuna ƙosawa da lamarin. A haka har garin Allah ya waye damu ranar asabar ɗin kenan da fatan kun gane. Gashi jiyan dai muka karanta wasiƙa Innarmu, cewar Innah Yahanasu tana hanya daga Maiduguri zata zo ta kaini asibiti, inya kama ma a tawo dani kano ne duk dai yadda ta kama, inma gurin maganin gargajiya za'a kaini dai duk zata zo ayi duk wacce za'ayi a gabanta. A cewar Innarmu bai kamata ace babu wani nawa a yanzu a wajena ba, dole a nuna ma su Nanno gatana. A hakanma sun makara da turo mutum. Ana wata ga wata kenan, ranar tonon asiri, ranar da ramin ƙarya zai ƙure. Sukuku haka duk muka kusan wuni, ni babu inda baya yi mun ciwo ma a jikina, hatta akaifa dake hannayena da ƙafafuna ciwo kawai suke yi mun, jinsu nake yi kamar suna ɗurar ruwa. Wajajen la'asar ina gaban murhu na dasa tagumi, bana gane komai bana jin komai. Ashe Nanno ce a kaina tana ta magana, sama da ƙasa Allah bai bani ikon jinta ba sam. Har saida Mijinyawa ya zungureni dawowarshi masallaci kenan. "Nace wai lafiyar matarka kuwa, shekara guda ciki anƙi a haifeshi, ga can Uwatale fa naƙuda take yi awa uku kenan tana abu ɗaya. Cikin jikin matarka fa kusan wata uku yaba na Uwatale. Ni inaga makarantane suka danne cikinnan suka kifeshi gaskiya. Gobe ni da shafa zamu ɗauketa zuwa can Burra, wani ƙauyene a Toro, akwai wani bafullace mai ba da maganin mayu, da muyagun makarai. Dan haka ka shirya har da...... " Shafa ce ta shigo da saurinta. "Nanno kizo ki ga Uwatale, abun fa yana ta sake kankama. Wannan karon gaskiya abun sai a hankali." "Kin bata hannun maryam ɗinnan dana jiƙa kuma? ( Shajaratu Maryam) Shahararriyar bishiyace wacce ake jiƙama mace mai naƙuda tasha ruwanta, domin samun sauƙin haihuwa da rage raɗaɗi. Yawancin unguwannin zoma na al'ada ke amfani dashi, dole a kwai hannun Maryam a ƴar jakar unguwar zomansu. "An bata ta sha Nanno" "To damo tsakin kuka maza, da ta sha bakin mahaifar zai buɗe, maza Shafa" Da sauri suka fice dukkansu. Mijinyawa na kalla rauni linkib a idanunshi. "Taso mu tafi Tutar so, maza taso matata" Miƙewa nayi, ban tambayeshi ina zamu je ha, banyi tababa ba, shiga ciki nayi sabida ƙarfin hali nice harda sake sutura, na saka mayafina mai kyau, ƴar jakar da kuɗaɗena, da magungunan da Harira ta bani, suke ciki na ɗauka, na zura ɗan kunnena da sarƙa na gwal a cikin jakar na fito. Ɗan makulli yasa ya rufe ƙofar ɓam. Ya amshe jakar hannuna. "Kiji da kanki" Tare muka fito dashi, ƙofar ɗakin uwatale cike da takalma. Ga dutsen niƙa a ƙofar ɗakin an ajjiye. Wannan wani canfine na mutan da, ajjiye dutsen niƙa a ƙofar ɗakin mai haihuwa dan kareta daga mayu, ko makarai. Ficewa muka yi suɗuɗu. Babu ko kowa a babban tsakar gidan, har muka fice babu wanda ya ganmu. Sai dai kash muna fitowa sai ga Abdulƙadiri da Halima, dama yace zai kawota ayi zumunci, tunda dai tun bayan aure bama mu sake haɗuwa ba. Su Barakane ma suka je, har mijinyawa yake tsokatamun Halima tace dani ya kamata tayi ƙawance nice wayayya basu Baraka ba. "Kai Magawata har kun mance da zuwan namu ne zaku fita tattaki. Gamu mun zo ai dole sai a koma ko? " Cewar Abdulƙadiri da yake magana da karsashi. Halima ma tayi carab tace. "Gaskiya kam ai gara mu koma ciki tunda dai mun haɗu ba ku yi nisa ba. Ni da ƙawata hira kam yau sai abinda na manta" Mijinyawa ya dubeni, nai mishi nuni da idanuna akan kar mu koma, tuni ya ɗauki haske, renon Innarmu ne fa mu ɗin. Wallahi sabida soyayya da fahimta, da karantar juna ko da hanci kayi magana miji yasan inda ka dosa, shi yasa ko ɓacin rai innarmu take yi da Baba Sojanmu bata dena mai komai data saba, a idanunta kaɗai yake gane tayi fishi, kuma ya shiga taitayinshi. Ai mace mai aji tayi. Ga wani hadisi kyauta na baku. Manzo rahma Arrasul S A W yace da ummuna Aisha. "Lallai ni na san lokacin da kike farin ciki da ni (ba kya fushi), da kuma lokacin da kike fushi da ni." Sai Aisha ta ce: "Ta yaya kake gane hakan, ya Ma'aikikin Allah?" Sai Annabi (S.A.W) ya ce: "Idan kina cikin farin ciki (ba kya fushi), idan za ki yi rantsuwa kina cewa: 'A'a, na rantsu da Ubangijin Muhammadu' (Wa Rabbu Muhammad). Amma idan kina fushi da ni, sai ki ce: 'A'a, na rantsu da Ubangijin Ibrahim' (Wa Rabbu Ibrahim) (A lura: Lafazin rantsuwar shi ne "Ubangijin Ibrahim" ba "Ubangijin Ka'aba" ba, kamar yadda bayani ya zo a cikin sahihan littattafai) Jin haka, sai Sayyidatuna Aisha ta yi murmushi ta ce: "Haka ne, ya Ma'aikakin Allah! Amma wallahi, ba abin da nake bari illa sunanka kawai (amma soyayyar taka tana nan a zuciyata)." Allahu Akbar wato ummuna Aisha macece mai hikima, macece wacce ta iya jan zaren soyayyarta da ma'aiki Arrasul S A W Itace macen da aka tambayi Annabi wa yafi so duk duniya yace Aisha. Akace a maza fa yace mahaifinta. Tsarki ya tabbata ga Ubangiji Annabi Ibrahim da Haruna. Ke ki zauna dai kina cewa ai mijinyawa ko Baba sojanmu tsoron matansu suke ji, juyasu akeyi, kar ki iya jan zarenki kinji ko? Maza dai zauna samadora, bodara. "Kai Abdulƙadiri ai fitowar bata motsa ƙafa bace ma, fitowace ta zuwa asibiti, jikin yayi nauyi sosai, ciki shekara guda. Gara muje asibiti muji abinda likitoci zasu ce. Kafin ace na gargajiya za'ayi." "To kace wani abu. Amman me zai hana ka bari su Nanno su yi da kansu? Kasan fa ba'a son batun asibiti musamman ta a wajen haihuwa. Kar ku tafi ku bar baya da ƙura" "A'a Abdulƙadiri. Dole nine a haƙƙu da in kula da'ita. Nanno tana karɓar haihuwar matar Nawata, sai su iya kwana ma ana abu ɗaya, kai fa ka sani. Zamu je kawai Amarya tazo barka da suna kawai." Da haka dai muka zulle musu, kai tsaye wajen motar Bauchi muka isa. Saura mutum uku mota ta cika, zuwanmu sai ya rage saura mutum guda. Ni dai kaina na jingine a damatsen mijinyawa naku mai ƙirji him hahaha😆. Har motarnan ta cika muka hau titi. Shiru motarnan tamkar ruwa ya cinye kowa. Wani irin sabon al'amari nake ji a jikina, wani iri zuchiyata take yi mun. Abun almara ana daf shiga cikin tasha, munfa riga da mun iso cikin Bauchi. Sai numfashi yai halinshi na suma.
Chapter 32 · 0% Book details