← Book details Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 84

Sashe 72

Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read

nuna ma. To zamu iya zuwa ku ga wajen, wannan bawan Allah ma haya zai kama ai sai mu ɗunguma tare ko Bilya? " Limamin ya dubi wannan bawan Allah da a wajen dama suka samesu, suna tattaunawa. Gidaje uku aka nuna musu, biyu daga ciki sababbine, wanda ya shiga shi zai soma shiga. Ɗayan kuma tsohone, amman ɗakunanshi sunfi girma, irin gininanne na masu dashi, wanda akayima ƙawa da ginin jan bulo ta wani ɓangaren. Sai dai sai anyi fenti, anyi gyaran ƙofa da dai sauransu, tagogin na gilashine masu murfi biyunnan. Ga tsakar gidan da yalwa sosai. Gidane na mutum huɗu kawai, mutum biyu bayan gidansu daban, mutum biyu ma haka, sai madafi babba a tsakar gidan. Sababbin kuma gidajene kamar na mutum takwas ɗayan kuma na mutum shidda. Mijinyawa yayi shiru yana ta nazari. Nawata yafi son sabon musamman na kusa dasu, Mijinyawa kuma yana ganin tsohon shi yafi dacewa, ɗakunan lallai da girma, gashi ko wanne ɗaki yana da ƴar baranda a ƙofar ɗaki. Kuma yalwa na da kyau. "Inaga zan ɗauki wancan na farkon tsohon, sabida kaga ɗakunan manyane sosai in yaso nayo fentin, kuma naga akwai rijiya a gidan. Duk da sauran akwai famfo, shi kuma nan babu" Qasimu yace. "Nima shi ɗin na zaɓa naga gaskiya suna da girma. Kawai a ɗaukeshi" Ai kuwa anan aka tsayar da magana. Kuɗin haya suka biya. Liman ya danƙa mishi ɗan mabuɗin gidan, da kuma ɗan mabuɗin ɗakin. "To shikenan Allah yasa ku shiga a sa'a Malam gaskiya zaɓinka yayi kyau sosai. Gidane mai kyau ginin masu kuɗi, tsufane dai kawai yayi. Bilya ko kaima shi zaka ɗauka ne? " "Gaskiya ina tunanin. Hakan, duk da ni wani auren zan kuma. Amman amarya ma tana son yalwa a bani kawai" Nan su Mijinyawa sukai ma liman sallama suka tafi. Sunje sun samu uwatale da yaran duk suna yashe a tsakar gida, suna ta yarɓar tuwonsu miyar kuka tako ji kalwa. Ga nasu Nawata a gefe kan tabarma an jera musu a kan farantin silba sabo 555. Sai langoginta tuwo da miya, da babban farantin da zasu juye. Ai kuwa Qasimu ya juye musu tuwonnan, tare da kwalala musu miya akan tuwon. Ruwan wanke hannu Nawata yace ta kawo, ta ɗebo musu a bokitin ƙarfe haɗe da buta. Bayan sun soma cin abincinne Uwatale take tambayar su Hindu da ragowar ƴan ƙauye. "Ai tana hanyar dawowa binni, harma mun kama mata waje, abinda ya kawo mu kenan. Baki ga gidan ba babba dashi, ga rijiya a gidan" Cewar Qasimu dake karantar Uwatale. Ai sai ta tsaya cak ta dena lashe miyar dake bin yatsunta. "Hindun, mijinyawa binni zaku dawo kuma Nanno ta amince muku, babbar abu ta k...." Mai ta tuno sai ta wayance da cewa. "Babbar magana kai abu yayi kyau sosai. Na ta ya ku murna. Kuma a wacce unguwarne, duk da ba sanin sunayen unguwannin nayi ba? " Nawata dake ta cin abincinshi yace. "Ta farko_ farkon layinanne, da ɗan nisa amman a layinnanne. Ina wani gida dake kusa da wannan shagon da kike zuwa siyan kayan miya? To gidan na kallon shagon." "Naji naji ai ko gidan babbane a haka a ido. me jinin jan bulo ko?" Nan dai Uwatale ta tsame hannunta ta shige ciki, abincinma ya fice a kanta. Sai tari take yi, sakamakon ƙwarewa da tayi da yawu. Qasimu ya girgiza kanshi kawai, tare da takalar Nawata da hirar me yake yi ne a binni, amman yaƙi faɗa fur, sai kau da zancan yake yi. Bai san Auwali ya sanar musu ba. Ɗakin su Zainab aka basu, su kuma akai musu shinfiɗa a falo. Mijinyawa bai kwanta ba, saida ya zaro takadda da biro da yayi dakon abunshi, ya rubutama Hindu duk abinda ke faruwa, tare da neman shawarinta. Sassafe suka nufi gidansu Luba. Tare da Luba suka zo layin, amman su iyakarsu wajen Auwali mai lemo. Luba bata jima ba ta fito mishi da amsarshi. *Dukkan abinda kake ganin ya dace ka siya.* *Ba sai ka bani kuɗim na siya ba, tunda ba'asan muna iya jin juna ba.* *Tunda ta amince, komai ai mai sauƙine jarumin jarumai* Ta faɗi a cire mata labule, a tawo mata da kefet, da kayan kallonta. Gaga_gaga_gaga_gaga. A cikin sati guda, duk gyare_gyaren da gidan yake buƙata saida Mijinyawa da Qasimu suka tabbatar ya kammala. Ranar da akayi fenti ne yaga Bilya ana buga ma matarshi amarya madafi na katako. Sai shima ya tambayi Liman shima yana so ya buga madafin. Liman ya amince mishi, tare dana Bilya aka gama fes. Haka su Mijinyawa suka kuma kwasa zuwa jama'are. Nan suka shiga tattare_tattaren duk abinda ya dace su tattare, na sawa a buhu suka sa, wasu a cikin randuna duk aka saka. Ya cire kafet ɗin uwarɗaki, na falon yace a barshi. Labulayen ma na Uwarɗakin kaɗai ya samu zarafin cirewa. Kwanansu biyu dai suna aikin, ana ukunne suka nemi motar kaya daga Azare, tazo ta kwashe kayan duka. Sallama Mijinyawa yayi da Nanno, dama mutan gidan. Su Yaya jamila duk sai da ya bisu har gidajensu yai musu sallama. Kadaran kadahan dai aka rabu. Cikin motar kaya, a bayan motar suka zauna, direba da mataimakinshi suna gaba. Ba su suka isa Kano ba sai wajen taran dare, motarnan tsohuwa zata ba zata ba dai shi ya kawosu izuwa daɗewarnan. Masu motar ne suka taimaka musu wajen shigar da kayan ciki. Kayan kicin ɗin duk aka loda a cikin kicin ɗin langa langarnan. Ragowar kayan kuma suka shiga dasu cikin falon. A saman kefet ɗinnan suka yi kwanciyarau. Mu kwana tare dasu a nan sai in Allah ya kaimu kuma gabatar be. Mrs BUKHARIMRS BUKHARI
Chapter 72 · 0% Book details