← Book details Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 84

Sashe 68

Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mijinyawa.:.
Washegari sassafe ya nufi tasha. Yamman sakaliya sai gashi ya sauka a Jama'are. Kai tsaye a ƙofar gidansu Qasimu acaɓa ya saukeshi, ya biyashi ya tsallake kwata ya shige.
A zaure yayi sallama. Sai ga Qasimu zuruf.
"Tun É—azu nake ta zuba idanu ko zanga dawowarka, kaga yanzu shigowata kenan.
Mijinyawa ya riƙe hannunshi zuwa waje. Shagon kwana ya tura suka shiga.
Nan ya labartama Qasimu abinda ya faru.
Tare da cire rigarshi ya juya ma Qasimu bayanshi, duk ya fashe.
Dariyar mugunta wallahi har fitsari saida Qasimu ya soma a wando.
Mijinyawa yayi kasaƙe yana kallon abinda yafi zare tsayi. Rigarshi a hannu.
A guje Qasimu ya fita, ko miƙewa baya iya yi.
Yaje ya sako kaya ya dawo da wasu a hannu.
Mijinyawa kuwa kwanciya yayi zazzaɓi sosai yake ji.
"Tashi ka sauya kaya kafin ka shiga, in Nanno ta ganka da jini a riga sabon rikici ne kawai.
Wai amman dan Allah kayi ihu sanda yake dukanka? Soja fa"
Ai sai dariya kamar zata halakashi.
Tsaki mijinyawa yayi, tare da miƙewa ya sauya riga, wandoma bai sauya ba.
Anan kwance yabar Qasimu dariya na shirin halakashi.
Har ya isa ƙofar gida yaji tub_tub Qasimu ya tawo da gudunshi, tare suka shiga bai ko kalleshi ba.
Bafa daina dariyar yayi ba, yana yi.
Tsakar gidan sunci sa'a ba mata sai yara.
Ɓarayinshi suka wuce. Ya buɗe ƙofar suka shiga.
Qasimu yace.
"Ai alwala zamu yi muje sallah in mun dawo sai kayi wanka, kasha magani, na karɓo maka ruwan zafi a wajen Baraka sirikin Soja."
Hararshi kawai yayi, bai tanka ba.
Kafin a idar da sallah fa jikin Mijinyawa ya rincaɓe a daddafe aka idar dashi.
Ana sallamewa ya fita kawai
Sai daga baya Qasimu ya bishi ya samu yana ta rawar É—ari.
Ruwan zafi ya karɓo mishi a wajen Shafa sabida yaji labarin Nanno jiya tayi tafiya. Taje biki, daga can wai sunyi da Nawata zai kai Uwatale bikin, in an gama sai su koma Kano da Nanno, taga waje.
Jin wannan labarin ya kuma hautsina Mijinyawa tunda yanzu dole sai sun jira dawowar Nanno.
Shagon gidansu Qasimu suka koma acan suka kwana jikin dai kau. Bayan ya gargasa jikin nashi, Qasimu yabi layi_layin shatin bel É—in daya kwakkwanta raÉ—au a allon bayanshi.
Ga ciwo ga rashin bacci, yana kwance tunanin tutar so kawai yake yi. Yama rasa inda zai saka ranshi. Tunaninshi ko ta farfaÉ—o, ko tana nan cikin halin daya barta? Inta farfaÉ—oma yasan tananan tana amsar zafin dukan da akayi musu, ga kuma ciwon jiki na tashin makarai.
Idanu ya lumshe, tare da miƙewa zaune akan katifar yayin da yake kai.
Idanu ya kuma lumshewa, tare da tuno Hindu a lokacin da suke halin yarda da juna.
Azgar da Asama'u ya tuno suma.
Saida Qasimu ya farka fitsari ya ganshi a jingine yanata karatun Qur'ani.
Kai Qasimu ya girgiza, ya fito wajen inguwa a talatainin dare, ya tsula fitsarinshi a gaban kwata yayi tsarki ya koma ciki da butar a hannunshi.
A haka washegari suka wuce wajen Kawu da hantsi suka isa. Kawu na zaune yana rubutun Qur'ani a allo a ƙofar gida yana zaune akan buzu sai gasu.
"Qasimu kune kuka sake dawowa kenan? Na dawo iyali sun sanar mun da zuwanku. Nasan dama dole da wata matsalar ko?"
"Eh Kawu da matsala ita ke tafe damu. Ina wuni kawu? "
Nan suka gaggaisa suka kwashe bayanai kaf suka labarta mai, harda tafiyar Hindu gida. Amman banda batun karatunta, amincewar komawa birnin kawai suke da buƙata.
"To akanme zata hanaka alhalin ta barshi shi ya tafi. ÆŠan gwalne shi ko duk ba Æ´aÆ´anta bane?
Zan sameta muyi magana. Amman yanzu kam suna wajen bikin ɗiyar Amadudu, iyali ma suma sun tafi jiya. To in suka dawo zanje da kaina mu yi magana in ji dalilinta in sha Allah. Ba zai gagara ba, zan mata magana. Bata kyautawa abubuwan da take yi. Wasu na dawowa kunnena ta bakin Gude, wasu kuma bana sani. Ita Jamila itace take ƙulla wasu abubuwan. Inda ace ita a matsayinta ta mace kuma ya. In uwarku ta kauce sabida tsufa, ko wani abun. Ita ya dace ta dawo da'ita hanya. Amman Jamila halinta sai ita. Wani daga cikin gadonku ma na wasu manyan gonakai da Ɗan Safiyo ya mallaka, da da aka danne anata rikici akansu. Allah yayi sun fito an ma siyar kuɗaɗen suna hannuna, Salihu dashi akayi komai"
Sun dai jima, Qasimu sai bashi wasu labaran matsaltsalu yake ta yi. Kawu yayi tsam yanata nazartar kalma bisa kalma. Kafin daga bisani dai suka mai sallama tare da komawa gida jiran dawowar Nanno, wanda baisan yaushe bane.
Shi dai yananan an barshi da dakon tunani da jumurin jiran dawowar Nanno, da baisan yaushe bane.
Aka tura har kwana huɗu, jikinshi da sauƙi, zuchiyarshi ce babu sauƙi sam, damuwa da tunani ne ya aureshi gaya.
A kwana na biyar da daddare kawai mijinyawa yace gobe sassafe Kano zai wuce, Qasimu ya rakashi zai je batun siyan fom ko Allah zaisa yaga Hindu da yara.
"Ni kam bafa zani ba, tsoro nake ji inje ya rufe É—aki damu haka siddan. Sannan akwai kuÉ—i a hannunka ne ma na fom da kudin motarmu?
" Akwai na fom É—in. Na mota yana wuyanka. Kuma wallahi sai munje. Inma kashemu za'ayi a kashemu"
Qasimu ya kafe. Mijinyawa ya rantse sai yayi rakiyarnan.
Cikin sarayar da rai suka kamo hanyar kano, sun ko sha ankon yadi mai ruwan bula, sai gasu da magriba a ƙofar gidansu Hindu. Amman me? tsoro ya hanasu shiga, sun kasa aika yaro.
Suna wannan raɓe ɗayan biyunne, suka hango Baba Soja da wasu matasa da kayan sojoji suna tawowa.
"Ga mahaifin Hindunnan ma zuwa. Qasimu gabana faÉ—uwa yake yi. Kaga yadda yake yi mana muzurai kuwa?

Hindu:.

Abu kamar da wasa ya zamana ni da su Innarmu sai idanu kawai. Bakina baya magana, ina buɗewa inci abinci, in sha ruwa, in sha magunguna da Innarmu take ta karɓomun.
Dukkan abubuwan da ake tattaunawa inaji. Da rikice_rikicen gulme gulmen da aketa yi. Inaji in su Innarmu na hirar.
Suna cikin tashin hankali mai girma. Ni kaina na shiga damuwa, Allah kaɗai nake ambato a zuchiyata. Ruhina yana azabtuwa irin azabtuwar da ban taɓa ji ba.
Ina dai ta faman tunanin abinda ya hana mijinyawa zuwa. Ko dai jinya shima yake yine? Nayi imanin in lafiya yake zai zo ko da kasheshi za'ayi, zai zo sai dai a kasheshi.
Idanuna na lumshe. Tsoron Allah ya sake shigata wato mu godema Allah da yayi mu masu yin magana, ma'ana furuci, kuma yayimu masu ji da kunnuwanmu, ma'ana amo. Lallai baiwace mai girma.
Allah Ubangijin masu ji, kuma Ubangijin kurame, Allah alhakim nagode maka da dukkan ni'imominka gareni. Allah buwayi ka buÉ—emun bakina, harshena yai furuci ko zuchiyata zata rage nauyi.
Haka akaita murɗawa, nice wankan magani, nice hayaƙi, sha da kunu, ci a abinci. Ga maƙota sai zuwa dubani suke yi, tare da zuwa ganin ƙwaƙwab. Cikin kwana biyar na rame na zama wata iriya sai kun ganni, dole sai kunji tausayina. Bana fatan maƙiyina ya gamu da cutar makarai wallahi, amman Alhamdulillahi nasan a kwana a tashi Ubangiji zai yaye mun nima.
Kwatsam da magriba muka jiyo muryar Baba Sojanmu, daga falo.
Mrs BUKHARINRS BUKHARI

..................

*Wai kina da labarin Gidauniya ta mata, farin cikinsu, da walwalarsu, mai suna *MURYAR MATA (FARIN CIKIN AL'UMMA)*🧕🏻👩🏻‍🎓
*Wanda ni Mrs BUKHARI muka yi haÉ—in guiwa wajen buÉ—ewa, tare da sauran shuwagabannin Taskar Badiat Ibrahim?*
*ku matso kusa ki kasance a cikin wannan tafiyar ta Alkhairi, tafiyar da zata gyara rayuwar Aurenki, tafiyar da zata gyara miki tunaninki, tafiyar da mace zata gane ni'imominta, tasan kima da darajar kanta, gidauniyar da zata koya miki sana'ar da zaki dogara da kanki, gidauniyar da zata koya miki tattalin uwar kuɗin kasuwancinki, da yadda zaki tattali ribarki ta yadda zaki ƙarfafa kasuwancinki, sha'awar son komawa makarantar addini, ko na boko kike so? To biyomu muje wannan gidauniyar taku ce mata, gidauniyar ta ƙunshi abubuwan da zatonku ma bai zata ba.*
*Ga lambar wayata ga matan da basa cikin Taskar Badiat group 1 group 2 group 3 sai kui mun magana in sha Allah zaki kasance a cikin wannan tafiyar ta manyan mata*
(08179523215)
*Ƴan taska kuma zaku iya tuntuɓar Admins ɗinmu ta pc domin kuji yadda tsari da dokokin kasancewa memba a cikin wannan shahsrarriyar, garnaƙaƙar gidauniya wacce ta haɗa manyan masana zamantakewar aure, malamai, manazarta, mahukunta, ƴan gwagwarmaya, masana ta ɓangaren gyaran aure, ƙwararrun ƴan kasuwa, da gogaggun ƴan boko, wanda ya haɗa matan arewanmu da kudunma baki ɗaya, zamu kasance a duk faɗin Najeriya da izinin Allah*

Leƙowa Baba sojanmu yayi.
"Ya tayi magana kuwa ko har yanzu?"
"Bata yi ba tukunna dai. Muna fatan tayi in sha Allah"
Kallona yayi tare da girgiza kanshi, ya É—agomun hannu irinna kurame. Nima na É—aga mishi.
"Kizo ku gaisa da mijin nata, gasunan shi da abokinshi. Ki tawo mai da yaran banma gansu ba"
Wani irin sanyine naji ya ratsa dukkan rassan jikina Alhamdulillahi.
"To barka Alhamdulillahi. Yara suna wajen Saratu ta tafi dasu. Damun Hindu suke yi da surutu. Ga Asama'u na lura laulayine da'ita, jiya ma saida na kaita asibiti. Shine Saratu tace zata tafi dasu"
Miƙewa Innarmu tayi ta fita. Nabi bayansu da idanuna kawai. Ina jin wani irin farin ciki.
Chapter 68 · 0% Book details