← Book details Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 84

Sashe 71

Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko da luba ta kawo mai wasiƙa da leda yayi farin ciki sosai. Musamman daya karanta wasiƙar. Layi uku ce rak, amman wannan layi ukun tana da girman da yafi ace shafi uku aka cika. Murmushi yayi, tare da buɗe ledar. Kuɗin da suka ganine yasa su buɗe baki, musamman Qasimu. "Wannan maɗuɗun kuɗaɗenfa na menene? ' " Hmm baiwar Allah. Babu mamaki ta bani ne sabida jigilar dawowa, da kwaso kaya. Kasan Hindu akwai tsinkaye, da hangen nesa." Shiru Qasimu yayi tare da dafa kafaɗar Mijinyawa. "Bari in maka nasiha ba dan na fika sani ba. Ba dan na fika haƙuri ba, asali ni bama mai haƙuri bane, yau faɗa da Baraka, gobe shiri. Haƙuri kawai aketa yi. Nasan ka kai mai sanyine, mai haƙurine ko akan su Yaya Jamila za'aima wannan shaidar. Dan wallahi in nine basu isa su mun abinda suke ma ba. Kana da riƙon amana tun muna ƴan yara kai ake kawo ma ajjiyar kuɗi, kuma bai taɓa ɓata ba, baka taɓa cinyewa ba. Kaga Hindu matarka? To ka riƙeta hannu ɗari_ɗari. Ko da sauyin zamani da lokaci zai sauya maka ita. Kai kayi ƙoƙari kaita kyautata mata. A gaskiya tana sonka. Kuma naga ƙokarin iyayenta sosai da suka ɗauketa suka baka ita. Hindu mutum ce har da rabin mutum" Qasimu yai ta mai nasiha da kwatance kala_kala. Mijinyawa na zaune a mota, amman minti_minti sai ya warware takaddarnan ya karanta, yayi murmushi ya damƙe a hannunshi. Anjima ma ya maya. Satarshi Qasimu yayi, ya warware kenan ya fisgeta, tare da sawa a ajjihu. Murmushi yayi mishi. "Sabida kunyi faɗa da Baraka shine zaka huce a kaina"? Dariya suka saka baki ɗayansu. Gaga_gaga_gaga_gaga. Nanno dai a ranar da ta cika sati biyu da tafiya. Sai gata Nawata ya dawo da'ita. Tace sam ba zata hawo mota ita kaɗai tun daga binni har Jama'are ba. Sun dawo yau washegari sai ga Kawu da misalin irin sha ɗayan safe yazo. Yaronshi ne ya kawoshi, dake yana da mota da yake yin lodin ƙauyuka haka. Shi da Malam Liman Kawu yasa aka tattaro kan ƴan gidan, da waɗanda suke gidan mazajensu. Waɗanda suke da nisa ƴan uwansu su wakilcesu. Bayan an cika an batse ga Malam Kalla Liman kenan a gefe, sai kawu yace. "Dangane da waɗannan katafarun ganakai biyu da shi Ɗan safiyo marigayi ya bari ne dama. Shi Salihu kusan dashi akayi komai. Dama saidasu akazo yi abinda ya faru ya faru. To Alhamdulillahi gonakai sun fito an siyar ga kuɗin magada za'a ƙarashe raba musu. Malam Kalla gareka" Nan Malam Kalla ya kasabta kuɗi bisa doron sharia, aka cirema kowa kasonshi ga kuɗinan muna_muna aka danƙama kowa nashi. Dake yawa garesu dai maza sun tashi da nera dubu ɗari da sittin sai matan kuma suka tashi da dubu tamanin. To a gaskiya wannan kuɗi a wannan lokacin kuɗine mai yawa, ba kamar yanzu ba. Bayan Kawu ya sallami kowa, ya sallami Kalla, su Jamila ma yace kowacce taje gidanta, zai yi magana da Nanno, Salihu, Mijinyawa, sai Mijinyawa Babba. Bayan sun shiga ɗaki yace. "Yaro yaje wajena da ƙoƙon bararshi, dangane da batun son komawa binni kamar yadda ɗan uwanshi gashi ya koma. Wanda kika je kika dubo inda suke" Sai kawai ta fashe da kuka wiwi. Kawu yayi kasaƙe yana kallon abun almara. Baice uffan ba. Mijinyawa sai kallon Kawu yake yi shi kuma. Yayin da Yaya Salihu ke harararshi. "Ƙarata yakai zaka ce Yaya. Ni banaso yaje ko'ina. Ni dai kawai ya zauna" "To shikenan. Kai Nawata zan bata umarni ita ta baka, cewar ka dawo da Uwatale nan ƙauye nan da sati ɗaya. Ka tabbatar ka siyar da gidan kafin ku dawo. Ki bashi wannan umarnin na baki umarni. In kuma ban isaba ga yaranki a gabansu ki nuna musu iyakata. Ni kuma daga yau ni dake mu raba hanya, ta yadda ko kin ganni a hanya ke baki isa yinƙurin nuna ni a matsayin ɗan uwa ba" Nawata yayi saurin ɗagowa. Yaya Salihu shima ya ɗago. "Kawu duk ba haka bane. Akwai daliline da yasa bata so ace ya koma birnin. Sabida matarshi ta riga ta mallakeshi sai yadda tace dashi a gabanmu. To ina ga sun koma binni? kuma garin da danginta suke. Watarana wahalar gani ma zai mana musamman in yayi kuɗi. Kuma fa yarinyarnan bata da kunya, bata da kirki..... " "Bata da kirki ko, maras kunya ce irin Shafa wacce ta kama Uwarka da dambe farko_farkon kawota, a sakamakon uwarka na son juyata kamar yadda ta juya gidanta a lokacin da mahaifinku yake raye ko? Ko juyashi take yi kamar yadda Jamila ke juya Ubale ko? Shin kun taɓa tsawatarma Jamila kan cuta ma Ubale da take yi, da su kansu yaran Ubalen data kaɗa uwarsu? Ko da yake ita da gatanta kam. Hindu ce bai dace tace ma mijinta ayi kaza ba. Bai dace Mijinyawa ya bata dama, irin damar da Ɗan safiyo ya ba gyatumarku ba kam. Uwarku ce ya dace ta tsara musu yadda zasu rayu tabbas, ya dace sai abinda tace. Ke kefa nake jira" Nanno tayi shiru ba amsa, sai haɗiyar zuchiya take yi. Ita bafa zata iya barin mijinyawa da Hindu bane a binni. Kuma bata isa musu da Yaya ba. "Yaje tunda kace yaje. Sai dai bana son ƙara ganinshi da iyalinshi Abadan" Murmushi yayi mata. "To kai kaji. Tashi kaje ka soma shirin binni. Duk ranar da yazo sai ki koreshi. Ranar da Nawata yazo da iyalinshi ki ɗauki Uwatale ki maidata ciki kinjo ko? Kai kuma inta koroku sai ku wuto gidana kai tsaye, ta bari ƙafafuna su taka gidannan akan kunzo ta koreku. Allah ya tsare muku hanya" Kai yasa ya fita. Mijinyawa na zare idanu ya miƙe. "Koma ka zauna dan babban, tsinin, abu ta kazan..." Cewar Nanno da bata taɓa shiga irin wannan halin na ɓacin rai ba. "Dama zan rakashine" Harararshi tayi, tana kuka. "Kaje ka rakashi ka dawo munafuki" Cewar Yaya Salihu. "Kada ka sake bakin ka ya sake furta mun kalmar munafuki. Zan iya jure komai banda wannan kalma mai muni" Mijinyawa an ɗan taɓuka yau. "To in ya kuma me zaka yi mishi? Yanzu in farfasa maka baki" Inji Nawata "Fasa baki, to ko zaka zo ne? Ai kasan karonmu dakai, kaga in bar kwantar dakai a nan ba" Har zai fita Nanno ta kirawoshi ta miƙa mai hannu halamun ya bata kuɗin wajenshi. Ledar ya miƙa mata babu musu, yaje ya raka Kawu ya dawo gaban Nanno. "Na gode da tursasani da kasa Yaya yayi. Watarana ma zaka sa ya tursasani akan in barma Hindu kai ita kaɗai tabbas. To naji ku tafi tunda an mun dole, amman bana so, kuma bazan taɓa so ba abadan. Na kuma gode da yadda ka nuna mun ban isaba" Mijinyawa zai yi magana Nanno ta ɗaga mishi hannu. Kallon Nawata tayi tace. "Kana da wajen da zaka basu su zauna ne, ko babu tunda naga ba du ka kammala gidan ba?" Ta dubi Nawata. "To akwai babu kuma. Sabida akwai ciki da falonnan na can gefen da kika gani, to shi wannan kinga yarane a ciki kuma ƙananune, sai inda muke ciki. Sai wannan ɗaki ɗaya dake zaure. Sai dai in shi za'a basu kuma to" Yaya Salihu yace. "Ai sai ka basu wannan ɗayan" "To ai akwai kayan shirgin Uwatale a ciki. Amman ai" "Ba sai ya bamu ba. Zan kama haya ma nagode ƙwarai" Mijinyawa ya katse Nawata. Nanno ta ƙirgi wannan kuɗi rabi cib ta ajjiye gefe, rabin kuma ta miƙa mishi dubu tamanin kenan. Yasa hannu ya karɓa yana kallonta. "Kaje ka kama haya, ka kuma tabbatar gidan da zaka kama bashi da nisa da na ɗan uwanka, kafin asan yadda za'ayi dan dole a gida ɗaya zaku zauna, ba zai taɓa yiyuwa kane gefe dangin matarka su samu zarafin yin yanda suke so ba. In har ba'a samu haya a layin ba, sai ku jira har zuwa lokacin da za'a samu. Wallahi akan wannan ko Yaya bashi da yadda zai yi dani. Ko bayan raina tare nake son ku zauna a waje ɗaya, sabida ƙarfafa zumuncinku da yaranku. Sannan dokata ta biyu kayan kicin da sututa kaɗai na yadda ku ɗauka. Duk wani jere daka sani anan za'a barshi sabida duk lokacin sallah ƙarama, da babbar sallah dole kuzo da iyalinku ku yi sallah tare damu anan, wannan dolen dole ne kaji na faɗa maka" Hankalin mijinyawa ba ƙaramin tashi yayi ba, amman ya ya'iya da abinda yafi ƙarfin wuta inji kishiyar ƙonanniya. Baici ta zama ba, ɗaki ya koma ya shiga sunturi yana kallon kyawawan kayan gadon Hindu da sabuntarsu. Murmushin baƙin ciki yayi, wani yanayi na taso mishi. Ya kuma kallon kuɗin gadon nasu, murmushi ya kuma yi mai cike tab da damuwa. Nawata ne yayi sallama, tare da shiga falon Hindu. "Nace gobe zan koma. Ka biyoni akwai sababbin gidajen haya har biyu a cikin layinmu, ɗayanma wani ƙaramin gidane a tsakaninmu, in yayi maka ai sai ka kama. Akwai kuma wanda ba sabon ba ma" Murmushi yayi mai. "To shikenan Allah ya kaimu goben, sai mu tafi tare. Bari in ma Qasimu magana tafiyar tamu ce tare" Qasimu ya nemo ya sanar dashi duk halin da ake ciki. Qasimu yaso su koma wajen Kawu, mijinyawa ya nuna mishi haɗarin hakan. Dole ƙanwar naƙi yayi haƙuri. Yaita dakon tunani, da nazari har zuwa wayewar gari. Sukai sallama da Jama'are sai gasu a gidan Nawata da yamma. Dake Unguwar Kurna Uwatale na tsakar gida da itacenta tana tuƙin tuwo ta ga shigowarsu. Gasu Zainab da ƙannenta suna ta wasannin guje_guje duk sun cika gidan fal da hayaniya. "Ahh Qasimu kune tafe, tare kuke? " "Tare muke Uwatale. Mun same ku lafiya? " Fuskar Qasimu kadaran kadahan. "Waje yayi Allah ya sanya alkhairi. Kai masha Allah" Cewar Mijinyawa. Alwala ma dai suka ɗaɗaura sabida anata kiraye_kirayen sallar magriba ne. Masallaci suka wuce, tare da ƙarema unguwar kallo babu dai laifi za'ace ga mutumin daya shigo daga ƙauye ga wutar lantarki tanwar. Bayan sun idar da sallah a wani ƙaramin masallaci. Sai Nawata ya gabatar da Mijinyawa a wajen limamin masallacin. Tare da sanar dashi gida suke nema na haya. "Ai kuwa ga kamanninan sosai faɗi kawai zai
Chapter 71 · 0% Book details