Sashe 25
Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read
kika mutu kika barni fa" Sai ya fashe da kuka, kuka mai gunji, gabaki ɗaya ya tashi hankalinshi, ya tashi nawa hankalina. Haka naita tausarshi, ina bashi kalma. A ranar mijinyawa da zazzaɓi mai zafin gaske ya kwana cur. Dangane da shawarar likita, haka kuwa akayi, sau biyar akayi mai a kemis, na shidanne ni nayi mishi, da haka harna ƙware, har zuwa lokacin zazzaɓine kau a jikinshi, sai da muka je asibiti. Likita ya kuma kwantar mishi da hankalinshi. Abubuwa sukaita tafiya, da daɗi babu daɗi dai. Cikin ƙudurar Ubangiji yanayi na ciki duk ya bayyana a jikina, sakamakon kasa baccin dare da nake yi, kusan dare na shiga nake faɗawa wani yanayi. Ga damuwar maganar samun jariri ko akasin haka. Rannan da safe muka shirya tsab muka nufi ɗakin Nanno jikin da sauƙi, tana gane kowa, tana iya magana, amman babu kuzari a jikinta sam. Sannu Nanno ya ƙarfin jikin naki? " "Da sauƙi. Wai nace har yanzu ba zaki haƙura da zuwa koyarwa ba, ciki kusan wata bakwai. Ko sai kin shiga watan haihuwar zaki dena zuwa? " Babu fa ƙwari a jikinta, amman saida tayi mun wannan batun. Kaina a lokacin sabida tsananin ciwon da yake yi mun tamkar zai faɗo haka nake ji, ga fuskanta tayi wani irin kumburin da idanuna ma sunyi mun nauyi. Babu damuwa Nanno zan iyane, kuma inna zauna ma jikin babu daɗi" Yaya Jamila tace. "In naƙuda ta kamaki a titi kinga ai shikenan. Gashi duk kin kumbura kin sauya kamanni ma" Cikin gatse ta faɗa, sai nayi dariya nace. Ai shikenan Yaya Jamila. Fatanmu shine sauka lafiya. Nanno Allah ya ƙara lafiya. Na tafi ni" Na miƙe da ƙyar ina jin wani irin juwa na ɗibana. Wallahi in sauka a ɗan tudun ɗakin Nanno saina kasa ɗaga ƙafata. Bauchin da ba'aje ba kenan sai washegari da na ɗan samu baccin awa uku cikin dare, sai jirin ya sassauta mun. Asibiti wajen likitan Mijinyawa muka koma, allurai da magunguna sun ƙare. Wasu tesa_tesan aka kuma yi mishi, akan nan da sati guda mu dawo. Hajiya Bara tana ofis sai gamu mun shigo, ina turawa da ƙyar, ga ƙwarya lailaye a cikina, ga ciko a ƙirjina. "Hindu kune a tafe da safe haka, kunga zuwana kenan nima gidan. Bismillah ga waje" Zama muka yi, ina dafe da kaina. "Lafiya naga duk kin kumbura, kamanninki sun sauya, Mijinyawa meke damun madam ne haka? " "Wallahi gata nan dai. Damuwa ta ɗauka ta ɗaurama kanta, duk akan sha'anin ɗaukar jariri ne. To dake tana da makarai shine suka matso kusa. Kin ganmu ko baccin kirki bama samu. Jiyane ma ta samu baccin awa uku. Jiyan muka so zuwa, amman jikin yaƙi" Hannayena Hajiya Bara ta kama. "Kar kiji komai in sha Allah zaku samu. An sassamu jira_jirai a makonnan har uku. Muje ku gansu, sai dai ina fatan kafin wa'adin wata taranki a samu wasu jariran. Muje ku gansu." Nan muka bi bayanta, tana ta nuna mana yanayin gidan, da yaran cikin gidan, dama ma'aikatan cikin gidan. Har muka zo ɗakin da jarirannan suke ciki, ga mai kula dasu tana zaune. "Baba an basu madarar ko, naga wancan yayi bacci, iyayenshi ma suna hanyar zuwa ɗaukarshi" Cewar Hajiya Bara da take magana da ma'aikaciya, mai lura da jariran. "Yayi kuka sosai, jiya kwana muka yi ba mui bacci ba. Ya hana bacci samuwa, ya sha madararma yaƙi sha" Kai na girgiza, sai ganina nayi a gaban kyawawan yaran, inata ƙare musu kallo, inaji tamkar in ce a bani su dukka. Mijinyawa ya dafani, duk mukai shiru muna kallon yaran. Ashe hawaye mijinyawa kawai yake ta faman sharewa abun tausayi wallahi. Da yawa ba lallai su gane, ko su fahimci irin nauyin da zukata suke shiga ciki ba, a yayin da suka kasa samun haihuwa, harma aka tabbatar musu a asibiti ba lallai su haihu ba. A hakanma magungunan hausa ko kafin dawowata mijinyawa ya dafa wasu da yawa, ko shekaranjiya yaje wani ƙauye ya karɓo maganin haihuwa, ana dai ta sha, mun zubama sarautar Allah idanu. Sai dai bamu fidda rai ba. Dafani da Hajiya Bara tayi ne ya sa muka juyo tare. "Kinga da ace cikin ki ya shallake wata takwas, ko da kwana biyar ne, da sai kin zaɓa. Wannan namiji ne, waɗannan mata ne biyu. Gasu kyawawa kuma lafiyayyu, basa ɗauke da ko wacce cuta mai cutarwa." Murmushin dole na ƙwaƙwalo, idanuna a bushe tamkar babu ɗigon ruwa. Babu dama ciki wata bakwai, ace na haifi taranni ai akwai ƙura kuwa. Amman ni tsorona Allah tsorona kada lokaci ya cika, a rasa jariran tunda yanzu an samu anya ba zamu yi amfani da damarmu ba kuwa? " Mijinyawa ya riƙe mun hannayena, dan ya fahimci hankalina a mugun tashe yake, ga ba ishasshiyar lafiya bace gare ba" "Hakane zancan Hajiya. Kina ganin babu ta yadda za'a iya bamu ɗannan mu tafi dashi kawai ace ta haihu? " Murmushi tayi tace. "Allahu Akbar. Nasan a cikin ruɗu da tsoro kuke, har kuke ganin ga wata dama ta samu kuna tsoron kar ta kubce a samu matsala ko? Kuyi tunani, ɗaukan yarannan da sunan haifarshi akayi da cikin wata bakwai, magana ta domin Allah asiri zai iya tonuwa. Hindu ke macece kinsan yadda ake haifar bakwaini fa." Ajjiyar zuchiya na sauke a hankali. Na ambaci Allah sai nutsuwa tazo mun. Wannan gaskiya ne Hajiya. Idan muddin muna da rabo zamu samu in sha Allah. Babu damuwa muna faɗama Allah" A gabanmu wannan mata da mijin da muka haɗu dasu a gidan Hajiya Bara zuwanmu na farko suka zo ɗaukar jaririnsu, ita cikinsu ya wuce wata takwas. Kyakkyawan namijin suka ɗauka yaro ɗan Fulani gashinshi lub_lub ina kallon yaron a idanun zuchiyata har yanzu. Matarnan ta rungume yaronnan ƙam a jikinta, ta durƙasa guiwowinta a ƙasa tana godema Allah maɗaukakin sarki. Murmushi kawai na sha'awarta da ɗan ya kamani sosai. Mijinyawa na kalla, idanunshi jawur jijiyoyin kanshi sai tashi suke yi. A haka muka koma gida, zukata cike da sabon zulumi, in kuka ganni ko da yaushe ambaton Allah, istigifari, karatun Qur'ani, sallar dare. A zaune nake yin sallah sabida azabar ciwon kai, duk halittuna sun sauya, kamannina sun koma wani iri daban, wallahi sharrin makarai har kaina saida ya sake girma. Ta wani fanni hakan yayi mini, sabida ya ɗauke zargi a kaina. Ta fannin ciwon jiki kuma, ina abun ba'a cewa komai sai godiyar Ubangiji. Kunsan masu makarai da zaran sun shiga damuwa, ƙunci, ko tashin hankali. Makarannan sai su matso kusa sosai domun su baka kariya. Wannan dalilin ne yasa suke yawan tashi, kuma dalilin da yasa nake ta kumbura kenan. Masu makarai irin nawane kaɗai zasu gane.