Sashe 6
Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 2 min read
shayi tana sha ga wara a gabanta. "Malama ashe kunzo kun tadda bananan? Wallahi wajen aiki naje, basason wasa sam dole ka fita sassafe shi yasa. Ki ma maigidanki iso mana yazo ko shayine in haɗa muku gidan ba komai" Kinga ma mun siyo doya a bakin asibiti, shayin dai zamu sha ki haɗa mana, bari in kirashi. Fitowa nayi na kirashi muka shiga, bayan an gaggaisa haka sai muka ci abinci nayi sallah, mijinyawa yayi sallah tun a asibiti. Kai tsaye gidan ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan marayu Harira ta kaimu. Hajiya Bara Mun tadda wasu mace da namiji a zaune suma tafiyarsu ɗaya da gani ma ma'auratane kuma ba yara bane sam. Waje Harira ta nuna mana muka zauna, ni dai nayi shiru ina taraddadi a zuchiyata bayan mun gaisa da wannan bayin Allah. Can sai ga wacce muka zo gani ta shigo da sallamarta. Muka amsa baki ɗaya tare da gaggaisawa. "Harira wannan itace Hindun? " Wannan mata ta tambaya. "Itace, wannan shine mijin nata ƴan biyune shi mijin nata." "Allah sarki to bari in gana da waɗannan baƙin nawa. Kunsan harkar tana son sirri." Harira tace. "Bakomai Hajiya" Nan ta shiga da baƙinta ciki, sunfi awa ɗaya a ciki kafin suka fito, sai tasa akai kiranmu ɗan ƙaramin falonta wanda anan take ganawa da baƙi. "Harira kinyi musu bayanin dokokin da matakan da akebi a hukumance, da dokance? Kunsan bafa mu zamu baku ɗa bane haka, sai da yarda, da sahalewar masu ruwa da tsaki. Zan muku bayani daki daki amman ba abu bane mai sauƙi ba. Waɗannan bayin Allahn da kuka gani sun fita, suma jinjiri suke buƙatar su ɗauka sabuwar haihuwa, nan da wata shida haka. To samun jirarirai yana da wuya gaya, loki ne samun gaskiya, bawai ba'a samu bane amman duka ba, loki ne dai" "Banyi musu bayani ba, nace dai waƙa a bakin mai ita ai yafi daɗi Hajiya" "To muna saurarenki Hajiya ayi mana bayanin yadda zamu bi tsari da matakan in abune mai yiwuwa, sai mu yi, in ba mai yiwuwa bane sai mu haƙura mu dangana. Cewar mijinyawa kenan. Mra BukhariMRS BUKHARI