← Book details Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 84

Sashe 34

Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Harira taimaka mun mu fito da'ita kinji sai in goyata mu shiga, na cire mata ƙwaryar cikinta. Jikinta yayi zafi sosai."
Cewar mijinyawa wanda duk ya ruÉ—e ya fita hayyacinshi ganin Hindu kwance babu yadda take.
Harirace ta zagayo ta buɗe ƙofar ta riƙe jaka da ƙwaryar cikin Hindu. Shi kuma daya fito saiya zarota ta kafaɗa ya fito da'ita. Harira ta taimaka mishi saiga Hindu a bisa kafaɗar mijinyawa yayi mata riƙon yara wanda kai da ƙafa suke reto a kafaɗa, ba dan bata da nauyi ba, aa sai dan yana ganin dole yayi hakan, sabida yayi sauri a ceto mishi rayuwar mata. Harira na biye dashi.
Suna shiga ma'aikatan babban asibitin Bauchi masu karanmci suka ba Hindu gado.
"Magawata bari inje wajen Dr AA NafaÉ—a in mata magana aminiyar Hajiya Bara ce zan zo yanzu."
Ina hankalin nashi ma baya tare dashi sam, har Harira ta dawo ita da Dakta AA nafaÉ—a farar dakta Æ´ar duma_duma baima san anayi ba. Adda'a kawai yake yi yana zurga zurga.
Jin an buɗe ƙofar ɗakinne yasa yayi zuruf yabi bayan Dakta AA nafaɗa. Harira na kiranshi ina.
Mata ya gani a kwakkwance a gado kawai, ga mata biyu a tsaye a gaban gadon Hindu suna dubata.
"Kaine Mijin Hindu kenan ko?"
"Eh nine likita. Dan Allah ki taimakeni Hindu ta tashi, kar wani abu ya sameta, gara ni komai ya sameni wallahi"
Murmusawa tayi, kafin tace.
"Babu abunda zai sameta. Asibiti ai gidan warakar ciwone da yardar Allah. Yanzu kaje daga waje ni da kaina zan duba Hindu."
Fita yayi jikinshi a sanyaye, amman ya zauna ya kasa zama.
"Mijinyawa zanje in tawo da Hajiya Bara yanzunnan akwai buƙatarta a wajennan. Sannan dama ai itace ta turani wajenku nai kiranku"
"An samu jaririnne Harira, dan Allah kice mun eh an samu?"
"A'a ban sani ba. Ni saƙwan kira kawai ta bani. Yanzu ka jira zanje yanzu zamu dawo tare. Nasanma ba za'a tambayeka komai ba tunda tana wajen Dakta AA nafaɗa"
A haka Harira ta tafi ta bar mijinyawa cikin zulumi sosai da sosai. Yana tsaye sai karatun Qur'ani yake yi, ba da ƙarfi ba, amman ba a zuchi ba a bayyane yake yi, harma wani bawan Allah da aka shiga da matarshi ya dinga tayashi suna yi tare.
Fitowar Dakta AA nafaÉ—ane ya zaburar dashi.
"Biyoni muje mijin Hindu"
Da sauri ya bita, yana tafe yana waigen É—akin da aka shigar da Hindu.
"Ka kwantar da hanalinka, duk taimakon gaggawan da take buƙata an riga an mata, an ɗaura mata ruwa, anyi mata abinda ya dace. Bacci da hutu sosai take buƙata, kusan cutar damuwace taso ta kamata, amman dai zamu shawo kan matsalar, sannan kayi ƙoƙari wajen rage mata nauyin zuchiyarta, ta ɗauki damuwar abu ta ƙwallafa a ranta. Ko duk akan batun ɗaukar jaririnne. Dan Hajiya Bara shekaranjiya ta mun magana akan zan bata gawar jariri daga mutuware, irin yaran da aka haifesu babu rai, sai iyayensu su gudu su bar mana su. Mu kuma saimu adanasu a mutuware, wasu suna dawowa daga baya rashin kuɗine ke sawa su gudu. Wasu kuma zasu haifi jariran ma da ransu zasu gudu su bar mana su, sabida ba zasu iya kulawa dasu ba, wasu dama bata hanyar Aure aka samar dasu bane, to ire irensune bayan duk mun gama musu gwajin lafiya sai mu turasu gidajen marayu, na gwamnati, ko masu zaman kansu."
"Wallahi likita akan batun da ta tashi hankalinta kenan. Nama dakkotane sabida mu zo wajen ita Hajiya Bara akan batun gawar jaririn, sabida yadda mahaifa suka matsa, shekara guda tana kife da ƙwarya a cikinta"
Kai ta girgiza tace.
"Nasan komai dangane daku, Hajiya Bara aminiyatace, mace mai tausayi, da mutumci kenan. Ai lamarinku ya tsaya mata a wuya fiye da yadda kuke tunani. Itama Hindu tayi namijin ƙoƙari. Abun mamaki yadda naga ta kumbura tamkar mai cikin gaske, yafi komai ɗauremun kai gaya"
Ƙofar ofishin aka ƙwanƙwasa, ba'a jira neman izini sai ga Hajiya Bara duk a firgice.
"Ya ake ciki ƙawata ta farfaɗo? "
"Kibi a hankali kinfa san sarai lalurarki. Mun shawo kan lamarin in sha Allah. Ya jaririn an samu kuwa? "
Mijinyawa ya ƙura mata idanu yana son yaji to me zata ce.
"An samu har biyu, mace da namiji, shine dalilin da yasa na tura Harira tai mun kiransu"
Zubewa mijinyawa yayi, tare da yin sujjadar godiya ga Allah da wannan babban asiri da ya rufa musu. Da kuma murnan samun jaririn, dan kusan yafi Hindu ƙwallafa rai akan samun wannan jaririn.
"Allah sarki bawan Allah. Kuna ta faÉ—i tashi, sai yanzu Allah ya nufa. Ina fatan asiri bai tonu ba dai ko? "
Kai kawai mijinyawa ya girgiza halamun asiri bai tonu ba.
Dakta AA nafaÉ—a ce tace ya basu waje, ya koma can É—akin da Hindu take zaima iya shiga.
Ai kafin ta ƙarashe ya fice da saurinshi, har yana zamewa. Ɗakin ya shiga ya tadda baiwar Allah a kwance, ga ruwa yana shiga jikinta a hankali a hankali. Fuskarta ya ƙurama idanu, yayi shiru kawai yana jin dama ita ta tashi shi ace shine a kwancen. Amman yasan haka Allah maɗaukakin sarki ya hukunta musu.
Ya jima a tsaye kawai a bakin gadon yana aikin kallonta ƙirjinshi na hawa da sauka. Ina ma Hindu irin son da bashi da abun misali. Duk da har kullum ya yarda kuma ya gamsu, son da Hindu take mai ya ninka wanda yake yi mata. Duk wanda ya kalli ƙwayar idanun Hindu, yasan tana sonshi gayatan.
Da ƙyar ya nemi farar kujerar dake gefen gadon ya zauna, tare da yin tagumi. Fatanshi da burinshi shine farfaɗowar Hindu, da kuma irin farincikin da zata yi a yayin data buɗe idanu taga jaririnta a gefenta.
Dakta AA nafaɗace ta ba da umarni aka maida Hindu wani ɗaki na musamman wanda gado biyune kacal a cikin ɗakin, daga na Hindun sai na wata baiwar Allah data haifi ƴan biyu, ga jarirannan a wani gado daban sunata bacci, itama uwar bacci take yi, ga ƙarin ruwa anayi mata, sai mai jinyarta guda ɗaya mace.
"To Magawata anan Hindu zata ci gaba da kwanciya har zuwa lokacin da zata samu lafiya, amman ya kamata kaje ka sanar a gida cewar ta haihu ko? In yaso Harira sai ta zauna da'ita. Kai namijine ba zai yiwu ka zauna kai mata jinya ba, dama É—akin dai ku kaÉ—aine. Hajiya Bara zata kawo jaririn yanzu"
"To Dakta mungode sosai Ubangiji Allah ya bar zumunci. Sai dai zan so a barni sai zuwa gobe da safe in naga farfaɗowarta, to sai in je in sanar musu. Kuma inaso in kwana ko da a ƙofar ɗakine sabida in dinga dubata jefi_jefi. Aimun wannan alfarmar"
Murmushi tayi tace.
"To shikenan Magawata, Ubangiji Allah ya bata lafiya ko? "
Sai ta saka kai ta fice.
Harira tace dashi.
"Inason zuwa gida in É—akko riyon kayan jaririn, sai ruwan zafi a filas. Da abinci zaka iya zama kafin inje in dawo"
Nan Harira ta fita ta bar Mijinyawa a zaune yana ambaton Allah. Ko magriba bai yi ba, ga isha ma ta wuce.
Ganin wannan mata ta shiga banÉ—akin cikin asibitin tayo alwala shine ya tuno ashe fa bai yi sallah ba. Yanzu dole ya jira Harira ta dawo tukunna.
Can sai aka turo ƙofa, Hajiya Bara riƙe da jariri a cikin farin abun ɗaukan yara, tana isowa ta miƙama Mijinyawa yaron.
Jikinshi na rawa ya karɓi yaron, baima iyaba saida aka gyara mishi kan yaron.
Durƙusawa yayi guiwa a ƙasa, sai hawaye yana kukannan hawayen na ɗiga a fuskar yaronnan.
"Alhamdulillahi Allah nagode ma da wannan kyautar da kayi mun. Ya Allah mun karɓa mun gode ya Allah. Allah ka raya mana wannan ɗa da imani. Kasa duniyar musulunci tayi alfahari dashi"
"Ameen Magawata, ka daure ka tashi, kawoshi a shinfiÉ—eshi kusa da Mamanshi"
Hajiya Bara ta karɓi yaron daidai shigowar Harira da kaya rigi_rigi tamkar gaske.
"Allah sarki Ubangiji Allah ya raya. Hala sun É—an jima basu samu haihuwar bane ko?"
Cewar wannan mata da take jinyar uwar biyu"
Harira tace.
"Suna cikin shekaru na bakwai kenan Allah ya basu"
"Allah sarki dole su yi murna. Ubangiji Allah yasa hanya ta buÉ—e kenan"
Duk suka amsa da Ameen."
Hajiya Bara ta fito, Magawata ya bita.
"To shikenan in Allah yasa ta warke zata zo ofishinmu ta sanya hannu, kaima ka sanya bisa doron ƙa'ida. A kuma ji tsoron Allah a riƙe yaro da kyau dan Allah. Ni zan tafi, na biya komai na asibitinnan ba'a buƙatar komai daga gareku"
Godiya Mijinyawa ya dinga yi mata, shine rakiya har gaban mota. Saida ya tabbatar da fitar motarsu, kana yabi wasu fulani suka yi sallah a wata ƙatuwar tabarma. Ya daɗe a sujjadar ƙarshe, da tahiyar ƙarshe yana godiya ga Allah da wannan rufin asirin da yayi musu, yana roƙon Allah ya tashi kafaɗun Hindu."
Bayan ya sallame ma ya dinga zubo adda'a, daya tuno fuskar wannan farin jaririn sai yayi murmushi. Wato Allah cikin ikonshi da hikimarshi ji yake yi a zuchi, da gangar jiki, tamkar shi ya haifi yaronnan. Kuma yaji yana jin sonshi da tausayinshi suna shigarshi tamkar yadda ake ƙarama mara lafiya jini, da ruwa.
Lallai Ubangiji mai girma da É—aukakane. Hukunci sai mai tsaga idanu.

JAMA'ARE:.
Chapter 34 · 0% Book details